FAIROOZ
NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION.
Babi Na Biyar.
Wani yalwattaccen sabon fili ne kuma ta tsinci kanta cikinsa.
Wuri ne mai matuk'ar kyawun gaske! Wanda duk wata halittar da ta tsinci kanta a gun, sai ya burgeta. Haka kawai Maryam taji kamar ta yi ta zama a wurin.
Daga gefe guda kuma na cikin filin, wani kyakkyawan lambu ta hango mai cike da kayan marmari da nau'in itatuwa daban-daban.
Daga k'asa kuma wasu launukan filawowi ne, suma kala daban-daban, masu kyawun kallo da ban sha awa.
Daga gefe guda can kuma ta hango wata k'orama, wacce ruwanta ke da matuk'ar haske sai gudana ya keyi abinsa.
Duka wad'an nan abubuwan Maryam tayi nazarinsu ne cikin dak'ik'un da basu wuce biyar ba. Daga nan inda take tsaye tana iya hango hasken ruwan k'oramar nan da yadda ruwan cikinsa ke tafiya a hankali a hankali. Dama kuma k'ishi ya ishi Maryam, musamman saboda gudun da ta sha wajen bin zomon da ta gani bayan shigowarta cikin wannan sabuwar duniya.
Bakin k'oramar ta k'arasa, sa'annan tasa hannuwanta ta d'ibo ruwan da bismillah ta fara sha.
Hajiya Maryam barka da zuwa BIRNIN SOYAYYA!''
Daga bayanta taji wani irin tattausan murya mai narkar da zuciyar wanda duk ya kasance ma abocin saurarenta.
Amma duk da dad'in muryar nan da Maryam taji, hakan bai hanata razana ba, dalili kuwa tun da ta tsinci kanta cikin sabuwar duniyar bata ga kowa ba, bare motsin wani, sai ko wannan d'an zomon da ta gani d'azu, wanda a sanadiyyar shi ne ta ganta ta b'ullo gun lambun data ke shan ruwa a k'oramar dake cikinsa yanzu!.
Cikin firgici had'e da razana ta waigo lokaci d'aya tare da mik'ewa tsaye daga tsugunnan da ta yi a bakin k'oramar da take shan ruwa.
Ba kowa idanuwanta suka gane mata ba face fuskar wannan kyakkyawan saurayin da take kallon hotunansa cikin littafin daya zuk'eta zuwa cikin wannan duniyar, wato saurayin da ta yiwa lak'anin suna da FAIROOOZ!.
Murmushi ya sakar mata tare da k'ara maimata abin da ya fad'a da farko,
Hajiya Maryam barka da zuwa BIRNIN SOYAYYA!''.
"Bawan Allah wane ne kai! Ya a ka yi kasan sunana, kuma ina nake a nan yanzu?'' Lokaci guda ta jero masa wad'an nan tambayoyin.
Murmushi ya sake yi, ba tare da yace mata komai ba, juya muryarsa yayi tare da yin wani abu kamar fito, fiuuuuuuuuu...sauti mai dad'i ya fita kai kace usur ya hura, nan take sai ta ga sun b'ace daga wancan lambun da suke ciki, sun b'ullo kuma a wani sabon lambu, wanda ya k'ere wancan na farkon kyau da tsaruwa!.
Domin a wannan lambun har da wani babban rumfa ta gani mai ado da k'awa na kayan k'yalk'yalin haske, ko ina cikinsa hasken k'wayaye ne ya cikasa tamkar wutan lantarki, ga wata darduma ta alfarma an shinfid'e a k'asa gaba d'aya! Daga gefe guda kuma wani tebur ne, cike yake da kayan Abinci da kuma kayan marmari na nau'in itatuwa daban-daban.
"Bismillah!." Ya nuna mata hannunsa alamar ta shiga cikin rumfar.
Ta bud'e baki da niyar yin magana sai ya dakatar da ita da hannunsa. Yace, ''Dakata! Kar kimin gardama, don ba a yin musu a nan.''
Cikin sanyin jiki Maryam ta taka zuwa cikin rumfar, kamar yadda ya umurce ta.
Tana sanya k'afafuwanta akan shinfid'addiyar darduman dake cikin rumfar, wani irin tattausan laushi taji sun ratsa k'afafuwanta.
Laushin da Maryam taji a k'afafunwanta tun da take bata tab'a jin abu mai tushi irin wannan ba, wannan ya faru ne duka a sanadiyyar taka kafet d'in da ta yi, a lokaci guda kuma taji wani abu mai sanyi daga jikin kafet d'in yana fesowa a k'afarta tamkar yayyafin ruwa. Nan da nan kima k'amshi ya gauraye wurin.
Duk inda ta sanya k'afarta sai taji wannan ruwan mai sanyi yayi feshi a tafin k'afarta, sanyin yana ratsata har cikin jikinta. Kayan dake jikinta ma nan take suka canza zuwa wata shiga irin ta alfarma tamkar sarauniya sai shek'i takeyi.
Abin ya baiwa Maryam mamaki ganin kayan dake jikinta suma sun sauya, ba tare da sanin wanda ya sauya mata su ba. 'To ko dai duniyar Aljanu na kawo kaina ne? Idan ba haka ba taya za'a canzawa Mutum kayan dake jikinsa kuma ba tare da shi ya canza su ba!'.
Tana cikin takawa kuma, daga saman kanta wasu k'ananan furanni ne taji sun fara zubo mata a jiki, suma kansu furannin k'amshi suke yi, da haka suka k'arasa zuwa dai dai inda babban teburin yake.
Wurin da Kujeru biyu masu fuskantar juna suke, nan saurayin ya nuna mata, tsayawa ta yi cak! Yayin da suke kallon juna ido cikin ido.
Har zuwa wannan lokacin, tsoro ba wai yayi k'aura daga cikin zuciyarta bane, dakewa kawai take yi, domin ta san ba ta da wani zab'in ko mafita da ya wuce tabi umurninsa, sai ko Addu'a da take ta kwararawa cikin zuciyarta. Domin Allah ya yi Maryam da rik'on Addu'a, dalilin marik'inta wanda ya tarbiyantar da ita a kan rik'o da Addu'a tun tana 'yar k'aramarta.
Saurayin ya yi murmushi, kamar ya san abin da take yi cikin zuciyarta.
'Tabbas ya san Maryam nan gaba kad'an za ta dad'a tabbatar da anfani da mahimmancin rik'o da ADDU'A!.
A tunaninta, ko da ma tace za ta gudu, to taya za ta gudamma Mutumin da b'acewa yake yi? Sannan kuma idan ma har ta gudun to ina za ta je?
Ba ta fa ma san a ina take yanzu ba, littafin kansa daya kawota wannan duniyar ma shi kanshi ya b'ace mata!.
Ashnur pyar❤
naam hei mera💃🏻Pls Vote✌🏻&
Comment🙌🏻
KAMU SEDANG MEMBACA
FAIROOZ LITTAFI NA FARKO
Misteri / ThrillerTana tab'awa kuwa sai taji ta zuuuuuuuuuuu....Gaba ɗayanta hasken yazu k'ota zuwa cikin littafin, ma 'ana ta shige cikin littafin datake kallon hotuna cikinsa. Ga mamakin maryam sai ta ganta ta ɓullo cikin wata sabuwar duniya daban, da irin wacce mu...