FAIROOZ
NAGARTA WRITER’S ASSOCIATION.
Babi Na Uku.
K’awaye HUD’U kenan, wad’an da suka rik’e k’awancensu da gaskiya ba su bari ta watse ba, tun bayan kammala karatunsu.
MARYAM ita ce wacce suke wa nickname da (RAI DA SO) sai
HALIMA wacce suke kira da hali dubu babu na banza, amma in wata cikinsu najin 'yar tsoka na sai suce mata babu na zab’a. Sai Aisha wato (Esha cool).
Sannan sai Amina ( Mrs Hydar) wacce tun ba ta yi Aure ba suke kiranta da hakan saboda tsabagen son da take ma sunan Hydar, a ka yi dace kuma Allah ya had'ata Aure dame sunan.Cikin ziyarar da suke kaiwa junansu, sun fi ziyartar Maryam sosai a bisa dalilin, d’auke ta da Mahaifinta Malam Hafeez ya yi, tun bayan kammala karatunsu, suka koma rayuwar daji shi da ita, wanda babu wanda ya san dalilinsa akan hakan ba.
Dukansu basu so rabuwa da ita ba, amma shi Malam hafeez yace zaman shi cikin jejin yafi mai kwanciyar hankali a halin yanzu, saboda cikin gari na tuna mai da wani abu da ya faru a can baya!.
Wannan ne dalilin da yasa suka d’aukar wa Maryam alk’awarin ziyartarta fiye da sauran gidajen juna da suke ziyarta, domin su rink'a deb’e mata kewa tare da k’ara gina dank’on zumuncinsu.
Yau wannan ziyara nasu bai wa Maryam dad’i ba, domin dai ta kasance cikin zuciyarta tana Allah-Allah su tafi ko za ta sake duban fuskar kyakkyawan saurayin nan, wanda haka kawai ta tsinci zuciyarta da bengen sake kallon fuskarsa, gashi hankalinta ya matuk’ar tashi na ganin fuskar mai yalwataccen murmushi a cikin jini.
Amma duk da jinin dake fuskar tasa, idan ka kalleshi za ka d’auka murmushin ya ke yi. 'Allah sarki FAIROOOZ nawa!' Ta raya cikin zuciyarta.
Sunyi ‘yan hirarrakinsu tamkar yadda suka saba yi a ko da yaushe, duk da dai yau sun fahimci k’awar tasu Maryam ba ta cikin yanayi mai dad'i, domin yau ko binsu bata yi ba, inda sukan je su tsinko kayan marmarin da suke sha yayin da suke hira.
Su kad’ai suka je, bayan sun dawo sun wanke wad’an da zasu sha, wanda zasu tafi da shi gida kuma sun ajje gefe guda, suna sha ana hira, Maryam ko tun da ta d’auki wani nunan-nen d'an k’aramin Apple ja guda d’aya a hannunta, tana rik’e da shi bata sha ba sai jujjuyashi kawai take a hannunta, ta k’ura mai idanu sai kace madubi take kallo.
Gaba d’aya hankalinta ba ya tare da ita, ta mance shaf da Mutane ma a gabanta.
“K'awa anya babu abin da ke damunki kuwa? ko dai akwai wani abu da kike b’oye mana ne?” Cewar Esha cool.
Firgigit tayi had'e da dawowa daga kogin tunanin da ta shiga, ta amsa da cewa ''Haba babu wani abu cool baby kawai dai yau na tashi banjin dad’in jikina ne shi yasa……''
Caraf Hali dubu ta cafke tun ba ta kai k'arshe ba.
“Kinsan shi kansa yawan zama wuri d’aya yana kawo haka ko? Ba yadda ba muyi dake ba ki fidda Miji a maki Aure kink'i...."
''Dakata Don Allah!.'' Maryam ta dakatar da k’awarta daga k’orafin da ta fara mata, tana me d'aga mata hannunta.
''Kin san ba na son irin wannan zancen ko! To ya isa haka?''
“Is OK girls, kar a fara tone-tone, ya kamata mu koma fa domin time d'in ma duk ya tafi " Cewar Mrs Hydar.
''Gaskiya ne kam rai da so! To zamu zo mu koma'' Esha ta fad'a.
Nan take kuma sai taji kewar k’awayen nata ya kamata, tare da tunanin anya yau ta kyauta masu kuwa? Domin gaskiya ba haka suka sa bayi da ita ba.'
Godiya ta yi masu, inda ta k’ara da cewa “kuyi hak'uri don Allah, yau ba na jin dad’in jiki nane.”
“Ah! Kar ki damu fa, Allah yasa rabon soyayya ne a ka samo mana! Allah yasa wani gwarzonne ya siye mana zuciyarki." Esha da Hali dubu suka tafa suna dariya don sun lura kamar ciwon soyayya ke damunta.
Nan dai suka yi sallama tare da basu sak’on su gaisar mata su Nafisa, Nabila yarinyar Maman Andad, Bintu Junaid." Nan dai Maryam ta fara lissafe-lissafen sunan k'awayensu.
Hali dubu tace ''Ke ya isa haka duk za su ji."
Har sun juya za su tafi Maryam tayi sauri ta ruk’o Mrs Hydar, nan da nan taji idanuwanta sun kawo k'walla, gani take tamkar ba ta kyauta masu ba. 'Wanda ya taso yazo wurinka tun daga cikin gari har cikin JEJI, ai ya gama maka komai, to amma ya na iya, tunanin SAURAYIN DAKE CIKIN LITTAFINN NAN NE ya dagula min lissafina.' Duk cikin ranta take wannan zancen.
Su ko sun tsaya suna kallon ikon Rabbi! Maryam ta rik’o hannun ‘yar uwarsu sannan tana tsaye kuma tana ta faman sake-saken zuciya ba tare da tace komai ba.
Mrs Haydar ta rik’e baki tare da fad’in. ''Ke lafiyar ki Kuwa? kin rik’e ni ke baki sake ni ba kuma ke baki ce komai ba?”
K'wallar dake mak’ale a idanuwanta ne suka sub’uce mata. Tace ''Friends ina fatan ban b’ata maku rai ba? Don Allah kuyi hak’uri.”
Gaba d’aya suka had'a baki lokaci d’aya “Baki mana komai ba ‘yar uwa.''
Esha ta k’ara da fad’in “Ai daman yau da gobe sai Allah! Allah dai ya baki lafiya.”
''Ameen Ameen.'' Sauran suka amsa.
''Ba kice a gaida maki da Maman Ahmad ba kin san tana can 'yar uwa laulayi ya b’oye ta.''
“Allah sarki wayyo ku gaida min ita please, af! Na ma tuna kuce ina gaida namecy Maryam lbrahim litee, dasu Aisha ibraheem el ladan.'' Haka Maryam tayi ta lissafo sunayen k’awayen nasu kamar ba za ta k’are ba.
Hali dubu ce tace "kai ku zo mu tafi kunji! Wannan in har muka biye mata ba za ta gama wannan lissafe- lissafen nata ba, idan ta rai da so ne to tabbas an rink'a yi kenan har mu kwana anan". Dariya suka yi ga baki d'ayansu.
Sannan suka k’ara yin ban kwana, cike da nishad’i da farin cikin ganin junansu.
Rakiya Maryam ta masu har zuwa k’ofar gida.
Suna barin gidan Maryam ta ruga da gudu cikin lambu inda ta b’oye littafinta, don daman tana Allah-Allah su tafi.
LITTAFIN dake d'auke da sunan FAIROOZ ta sake d’aukowa, sannan ta bud’e.
Shafin nan da ta ga fuskar kyakkyawan Fairoooz d’inta cikin jini, kamar yadda ta rad'a amai suna, shi ta sake bud’ewa.
K’urawa shafin ido tayi sosai, tare da mayar da dukkan hankalinta ga kallon duhuwan bishiyoyin nan wad’an da ta gani d’azu, a tunaninta wai ko zata iya fahimtar wani abu a ciki, sai dai harta gaji da kallon hoton ba ta iya gano komai ba.
Shafin gaba ta sake bud’ewa, a nan kuma sai ta ga hoton shafin ya sha babban dana sauran shafukan. Wani irin zane ta gani mai kama da rafi-rafi kamar kuma rijiya mai d’an zurfi.
Zanen nan da take wasi-wasin rafi ne ko rijiya ta kasa banban cewa, shi ta gani d’auke da wata alama a tsakiyarsa, kamar an juya ruwan ciki juyi sosai! To a dai dai tsakiyar inda ruwan yayi alamar zurfi, saboda juyasan da a ka yi, nan taga shaidar wani haske mai k'yalli sosai a tsakiyar ruwan ya soma tasowa.
Kallon hasken ta rink'a yi tana mamaki, saboda taga yana motsi tamkar ba cikin littafi yake ba.
Sannan wani abin da ya k’ara rud’a tunaninta shine, ganin da ta yi tun da ta bud’e shafin, rijiyar da take kallo, ko rafi ne ma ita dai ta kasa banbancewa, hasken dake fitowa daga tsakiyar hoton, gani ta yiyana kad'awa kamar cikin iska!.
Haka wannan hasken ya ci gaba da kad'awa yana motsi kad’an kad’an, Maryam dai tana nan zaune tana kallon ikon Allah! hasken na ta k’aruwa a gabanta.
Maryam da karambani sai kawai ta yanke shawarar sa hannunta domin tab’a hasken dake tasowa daga cikin littafin, tana tab’awa kuwa sai taji ta zuuuuuuuuuuu…..........Gaba ɗayanta hasken ya zuk'e ta zuwa cikin littafin, ma'ana ta shige cikin littafin da take kallon hotuna cikinsa!.
![](https://img.wattpad.com/cover/120700986-288-k665469.jpg)
ESTÁS LEYENDO
FAIROOZ LITTAFI NA FARKO
Misterio / SuspensoTana tab'awa kuwa sai taji ta zuuuuuuuuuuu....Gaba ɗayanta hasken yazu k'ota zuwa cikin littafin, ma 'ana ta shige cikin littafin datake kallon hotuna cikinsa. Ga mamakin maryam sai ta ganta ta ɓullo cikin wata sabuwar duniya daban, da irin wacce mu...