01

9.9K 555 6
                                    

👑 👑 👑 👑 👑 👑 👑 👑

💖 💖 💖 💖 💖 💖 💖

💍 💍 💍 💍 💍 💍

...ME RABO KA DAUKA 01

shatuuu095@wattpad show me some
love by voting and sharing

✍️AMMIN SU'AD

Alhamdulillah shatuuu is back with another tantalizing write up that I know must of you or I should say all will like. Follow me on this journey as I explore u about RAUDHA.

Eid Mubarak to every Muslim around the globe, Allah maimata mana yasa ibadunmu na Ramadan are accepted.

"Mami.... Mami.... Mami" haka ta cigaba da kwalla wannan sunan har ta samu ta tsallake mutanen dake dankare a parlour ta kutsa cikin bedroom dinta. Tana zaune gefen gado ta hakimce, Sanye cikin dankareren lace, fuskarnan Se annuri kawai Ke fita, daga gefenta kunyangarta ce tsugunne tana zuba mata abinci, se tsirarin mutane Wanda DA dukkan alamu yan uwa ne na jiki, jin kiran yayi yawa yasa Mami duban kunyangarta dake tsaye Tace "baraka waye ke kwallan kira? " tsugunnawa tayi tace "ranki ya dade FULANI ce" kai ta kada batare da ta furta komai ba, shigowar matashiyar budurwa wadda shekarunta bazasu wuce goma Sha bakwai ba, ta karaso ciki hannunta riqe da wani ubansun lace, fuskarta kadai ta isa ta sanar maka ranta a bace yake, gefen Mami ta xauna wadda take binta da ido Tunda ta shigo amma batace komai ba "Mami ki kalla kayan Nawa Duk sunyi kadan, musamman skirt din" spoon din hannunta ta aje kafin tace "shine dalilin kwalla min kira da kike? Ina manners dinki suke? " se lokacin ta fahimci bata kyauta ba, Don Mami mutum ce me tsauri wajen tarbiyya, slightly ka kauce to lallai Ranka zai baci, shiriu tayi tana wasa da yatsunta DA suka sha ja da bakin lallai, "kunnenki ya daina ji ne? " Mami ta tambaya Tana kallonta " Kiyi hkri " ta fada idonta ya cicciko kamar mai shirin kuka, abincinta ta cigaba da ci kafin ta dubeta tace "ki fadawa lami, akaiwa tela ya buda yanxu" Kai ta kada sannan ta miqe ta Fita ba tareda ta lura da mutanen dake cikin dakin ba.

Masauratar Daura ta samo asali lokacin bayajidda, inda anan ya yada zango har ake tunanin nan ne asalin Hausa. Masauratar daura tana da dumbin tarihi a arewa Dama Nigeria baki daya sannan tana daya daga cikin Hausa bakwai.
Sarki Suleiman Hassan shi ne sarki a Wannan zamani wanda ya gaji sarautarshi Daga gurin mahaifinshi sarki Hassan, shi ne babba kuma su uku ne maza se yan uwa mata da Allah ya basu, tun duniya na kwance yayi karatunsa a Ahmadu bello university dake Zaria a matsayin engineer , Bayan ya Gama ya auri A'isha wato Mami wadda yar kanin babansa ce kuma zabinsa, Mami Mutuniyar kirki ce, zai Yi wahala kaji wani yana kuka da halinta ba, tana da saukin Hali amma bata daukar hauka kuma tana da tsanani akan tarbiyya yaranta. Bayan shekaru biyu ta haifi danta Abdullahi wanda a yanzu Yana matsayin yarima kuma yana nan cikin daura da iyalansa, Abdulhakim matsayin turaki DA iyalansa a Abuja , Abdurrauf matsayin Dan maje Yana turkey da family dinsa, Abdulhamid Yana Kano da nashi iyalan. Lokacin sarki Hassan yayi murabus ya daura sarki Suleiman inda wambai ya bashi yarsa Saadatu (Ma) ya aura, yarta ta farko ummu-habiba tana auren wani ambassador suna japan, ummul-khairi anan daura take, Mami ta haifi Abdulaziz , Ma kuma ta haifi ummu-salma dake aure a bauchi, ummu-sulaim , Mami ta haifi Aziza sannan Abduljabbar. Ma ta haifi ummu-khulthum , daga nan haihuwa ta tsaya a gidan kusan na shekaru biyar kafin MA ta haifi ummul-Amin sannan Mami ta haifi auta Raudha wadda sarki yake kiranta DA FULANI. Amma akwai yaya dayake riqo sosae wasu ya aurar wasu suna nan.

MA bata taba haifar namiji ba, hakan bai dame taba saboda wannan ba a gaban ta yake ba, duk da mafi yawanci Abinda muka sani game da gidan sarauta shi ne kishi DA hassada, to hakan yayi karanci cikin masarautar ta daura Don yadda yayi Saar mata daga Mami har Ma kuwa, zaman lafiya suke sosae, GA kan yaransu a hade bakace ba ciki daya suka fito ba. Sarki Suleiman Yana da wata a 'kida wadda dole yayansa har mata sae sunyi karatu kafin aure, mutane sunyi criticizing Amma ko a jikinsa Duk yayansa se sun gama secondary sun Fara tertiary school yake musu aure, a cikin tsarinshi babu Auren dole, ki fito da wanda kike so ya aura miki shi saboda shi mutum ne me son yayansa, no matter aikin da yake yana samun Lokaci sau uku a sati da zai saurari matsalolinsu sannan suyi hira, hakan yasa suka Saba dashi sosae kuma they are free with him suna sakewa su fada mishi damuwarsu.

Aziza ta gama karatunta itada sulaim a Riyadh, sun karanci common and Islamic Law, hakan yasa me martaba yi musu aure hade da yayansu Abdul Aziz . Gidan a cike yake da jamaa, kowa hadahada yake GA farin ciki dake kunshe kan fuskokinsu.

"Mama lami, kinga kayana sunyi kadan gashi duk an Fara tafiya wajen kamun" Fulani ta fada Cikeda da damuwa, Matar da bazata wuce shekaru arbain ba a duniya ta Kalle ta Tace "Fulani tashi Kiyi wanka kafin ki fito an buda kayan" wani murmushi ta saki tana fadin "Shiyasa nake sonki mama lami, nagode " kai ta girgixa Tana binta da kallo harta fita.

Cikin sauri take zura kayan da kuyangarta hanne ta kawo mata, maroon lace ne da milk a jiki, yayi mata kyau sosae kamar a sace ta, dama tuni tayi kwaliyyarta hakan yasa ta Bata Lokaci wajen daurin dankwali da yake gwanar kwaliyya ce baa Kada ita a Wannan fagen wani Hutu taje Abuja yaya abdulhakim ya kaita makeup school hakan yasa ta mugun kwarewa, wannan bikin babban biki ne a gurin ta Don haka take bata Duk wani Lokaci da take dashi don ganin tayi kyau. Ummul-Amin ce ta shigo itama Irin shigar raudha ce a jikinta, tayi masifar kyau, kallon raudha tayi tun daga sama har kasa kafin tace "twiny, Kinyi kyau am jealous "hararar ta raudha tayi daidai lokacin da take zura golden high wedged takalminta "Baki da dama twiny, DA Kinsan yadda kike daukar ido Bana tunanin zaki bata bakinki" dariya sukayi sannan suka fito inda masu hidima dasu Ke jiransu, sallamarsu sukai sannan suka kashe pictures kafin suka nufi bangaren MA, itama mutane ne dankam a ciki , duk inda suka wuce se ance sunyi kyau, harsuka isa ciki inda take Zaune, shekarun MA xasuyi arbain, Fara ce me matsakaicin jiki da tsayi, shadda ce jikinta se yaya khairi a gefenta, hotuna suka dauka sannan suka nufi gurin Mami, ta sauya kaya Zuwa wata Holland orange color, Tana ganinsu ta sake sakin murmushi tana fadin "Amin Kunyi kyau, wannan ai sai ayi tunanin kune amaren. " dariya sukayi ta jin dadi tare da mutanen gurin wanda ke fadin "rai dai wai ancirewa fara kai " hotuna sukayi sannan ko Wacce ta nufi gurin marikiyarta . Raudha tana shiga ta tarar da mama lami Zaune Kan dadduma dauke da casbaha tana ja, juyi tayi tana fadin "mama ta Nayi kyau? " "har sekin tambaya, inaga ko Aziza bazata fada miki kyau ba yau" sosae taji dadi kafin ta fice tana fadin "ina sonki mamata"

Gurin yayi kyau, babu Abinda Ke tashi se kidan kwarya da Kada shantu, Aziza da Sulaim sunyi kyau, kowacce hakimce gefen mijinta. Raudha taje sun gaisa sannan sukayi hotuna kafin ta koma gefen Nadiya wadda cousin dinsu ce ta zauna gefenta suna dan hira, ana haka Amin da nafisa suka karaso, nan kowacce ta Fara daddana wayarta.

Sanye yake cikin sky blue din kufta, ta amshi fatar jikinsa, cikin wani abu me Kama DA isa yake taku har yazo seat din dasu Amin Ke xaune, "Assalamu alaikum " ya fada cikin muryar shi me nuni DA cewa namiji ne, Lokaci daya duka su hudun suka dago suka sauke idonsu kan Fuskarshi, raudha ce ta Fara janyewa ta maida idonta kan wayarta.

How is it? Sweet? Nice? Boring? Don't mind me dadi na nan Zuwa. Keep on following me, ina sonku

©️ Shatuuu♥️

...ME RABO KA DAUKAWhere stories live. Discover now