👑 👑 👑 👑 👑 👑 👑 👑
💖 💖 💖 💖 💖 💖 💖
💍 💍 💍 💍 💍 💍
...ME RABO KA DAUKA 02
Shatuuu095@wattpad
✍️Ammin su'ad
This page is dedicated to all those who showed me love during my muqqadari ne days.
A tare su ukun suma suka Sauke idonsu, hakan yasa shi sakin murmushi yace "barkanku da hutawa yan mata" nafisa ce ta dago tace "lapiya kayi mana tsaye akai? " kusada raudha ya matsa Yana fadin "wannan ce dalilin zuwana gurinan" dago idonta raudha tai ta xube idonta kanshi amma se ta samu kanta da kasa fadin komai, hakan yasa ta dauke kanta, Nadiya ce ta Mike Tana fadin "let's find another seat" Miqewa sukayi suka nufi wani vacant seat dake nesa da gurin, zama yayi Yana kallonta Don har lokancin Bata daena danna wayarta ba, shiru yayi Yana sake Kare mata kallo. A takure raudha take saboda kallon yayi yawa, dagowa tayi tace "me ya faru ne?" murmushi yayi kafin ya fara fadin "Ahmad Hashim, ni abokin mijin sulaim ne" kai ta kada tana duba text din Amin daya shigo yanxu, fada mata take ta saki jiki dashi, saboda ya hadu. Murmushi ne ya kubce mata wanda yasa Ahmad sake ganin kyanta " na ganki Tunda kuka shigo, ina sonki shi ne naga is better nazo na fara sharewa kaina hanya"
"nagode " shine Abinda kawai raudha ta fada, murmushi ya Kara saki wanda yasa raudha fara tunanin Meye matsalarshi ne dayake faman smiling kamar wani fool, duk da zuciyarta ta amince murmushin kyau yake masa kattse ta yayi Yana fadin "come on, ba godiya zaki minba just tell me your name"
"Raudha "kawai taji bakinta ya furta batareda tasan da hakan ba, cikin dabara ya dinga mata hira har ta sake, bai tashi a gurin ba saida ya karbi phone number dinta. Yana barin gurin su nafisa suka dawo suna tayi mata shakiyanci tareda fadin " Allah sa baki kwafsa ba" itade batace musu komai ba har aka gama event, kowa ya tashi a gajiye. .
Washegari aka daura aure, Aziza mijinta Dan wani minister ne zata zauna Abuja, itakuma Sulaim Dan sarkin Ringim zasu zauna a kano, Abdul Aziz kuma yar gidan waziri ya aura ya tafi DA ita cikin katsina inda yake aiki. Ana Gama daura auren aka shirya tafiya dasu gidan mazajensu, sulaim ko kuka Batayi ba amma Aziza kuwa kuka tai tayi itada raudha, Mami ma daurewa tayi tace a tafi da ita saboda suna neman karya mata zuciya, raudha ta miqe zata bisu Mami tace ta xauna haka tana gani aka tafi DA Aziza. Wunin ranar haka tayi shi sukuku babu wani walwala a tattare da ita abinci ma kinci tayi daga karshe ta koma gurin mama lami tana sake sabon kuka, rarrashinta ta dinga Yi har bacci ya dauketa. Mama lami tun asali kunyangar Mami ce Tun lokacin farkon aurenta da me martaba, lokacinda Mami tana da ciki suka tafi saudiyya umra, DA mama lami ta tafi saboda hidima Tunda tayi nauyi, a cikin Raudha ta Fara labour hakan yasa Bayan an haifeta sarkin Kano ya saka mata suna Raudha wanda shima Yaje umra da uwargidanshi. Wannan shine dalilin zaman mama lami me renon raudha, ta saba da ita, duk wata matsalarta ita take fara kaiwa kafin Mami taji.
Washegari gidan ya sarara ,mutane duk sun tafi, ya rage iya su Salma ne da dawowarsu kenan daga Kai amare, suma karfe uku kowacce tayi sallama ta nufi gidanta da yayanta. Gida ya rage daga kulthum wadda Ke level 3 a UMYUK, Amin, raudha wanda su basu shiga school Bama se Abdujjabar wanda yake aiki da NNPC a cikin katsina. Se sauran wayanda ake riqo amma dukda haka kowa Yana kewar su Aziza.
Kwance raudha take Kan gadon Mami, wayarta dake jikin socket ce ta Fara vib, zaune ta tashi ta janyo wayar PRINCE ne taga true caller tayi identifying, waye prince kuma ta Fara tunani ko yaya AJ ne, location ta duba taga Zaria to waye haka? Katsewa kiran yayi kafin tayi tunanin yin wani abu call din ya sake shigowa, a kunne ta Kara tana fadin
" Assalamu alaikum "
"Waalaikamusaalam " tayaya zata manta muryar nan, tayi tunanin bazai taba kira ba, katse mata tunaninta yayi ta hanyar fadin
"Kiyi hkri, bamkira kiba ko? School zan koma to Inata shiri am very sorry " ajiyar zuciya raudha ta sauqe jin reason dinsa, cikin nitsuwa tace
"babu komai, ya kuka je gida?"
"lapiya lau, baxaki tambayeni ban Gama karatu ba?" murmushi tayi tace
"To na tambaeka" 'yar dariya yayi a hankali Wadda yasan zata kasheta kafin yace
"three years back na gama degree akan computer science a Russia, so yanzu next week zan tafi Columbia masters dina" Kai ta kada tace
"Allah temaka ya kiyaye"
"Amin " ya fada kan ya cigaba da fadin "ke Meye naki plan din? " ido tadan jujjuya kamar yana gabanta tace
"ABU Zaria na samu admission zanyi food science and technology"
"mashaaa Allah, Allah ya temaka. Yaushe zanzo na ganki? " shiru tayi tana nazarin tambayar, ita zuciyar tata amince Ahmad yazo ya gwada saarsa to Amma Bata sani ba, but zata fadawa mama lami idan yaso sai ta tafi gidan yaya khairi Se ta tare shi
"ko Baki son nazo? " ya katse ta, Kai ta girgixa tace zan kiraka Anjima idan Nayi shawara, Daga haka sukayi sallama , daidai shigowar Mami kenan, kallonta tayi sannan ta dauke kanta batareda tace komai ba, zama tayi kan wani cushion dake gefen gado sannan Tace
" Amin na nemanki, ki tashi kije ki sameta" Miqewa tayi ta fita Bayan ta amsawa Mami, kicibis sukai itada Amin wanda ya sasu tsayawa kowa na maida numfashi , hannunta Amin taja suka nufi dakin mama lami Bayan ta bada umarnin akawo musu fruit, babu kowa cikin dakin Don mama lami bata nan ta tafi wani gari gaisuwa, zama sukayi saman sallaya daidai shigowar shafa kunyangar Amin da tray Cikeda fruits a yayyanke gwanin shaawa, ajewa tayi ta tsaya raudha ta dago ta mata alamar taje Dan dukawa tayi alamun girmamawa sannan ta fita.
" ina jinki twiny Don nasan bakinki akwai magana" inji raudha, murmushi tayi tace
"yaya abdulhakim ne ya kawomin admission letter Dita ta base" inji ummul-Amin, take fuskar raudha ta canja,
" yanxu da gaske twiny base din zaki bazaki Zaria ba, zaki iya rayuwa babu ni? "
"ya zanyi Tunda basu bani admission ba, kuma Abbu yaki yayi magana da sarkin zazzau, Kinsan shine chancellor. Kiyi hkri haka destiny mu take, we have to cross different paths" kai ta girgixa Tana tunanin yadda zasuyi Don Tunda aka haifesu basu taba rabuwa ba, dukda dayar zata fada kafin nata personal kawayen, idan basu suka fada ba bazaka taba tunanin ba uwa daya bace ta haifesu saboda yadda suke tare cikin shakuwa da son juna....
"Ahmad bai kiraki ba? " Amin ta katse shirun da ya gauraya dakin, take murmushi ya subuce mata wanda yasa Amin sakin dariya tana fadin "twiny ta ta kamu, Irin Wannan chuckling haka" apple raudha ta dauka ta Fara ci Don dauke hankainta daga iskancin DA Amin Ke mata, Seda ta gama sannan ta Fara bata labari da neman shawara, sun amince kan a sirrance su tafi gidan yaya khairi Se su tarbe shi acan. Daga haka kuma aka koma hirar saurayin Amin.Do vote and comment and also share to your loved ones. For whatsappians my digit is 09063467258, no calls whatsapp message only. I love you dearies
©️ shatuuu ♥️
ESTÁS LEYENDO
...ME RABO KA DAUKA
Ficción GeneralKowacce mace a duniya allura ce a cikin ruwa ME RABO KA DAUKA. Kaddara kansa mu hadu da mutane da yawa, wasu mu cutar dasu, wasu su cutar damu, wasu su bar Sautin muryoyinsu cikin kunnuwanmu, wasu Takun tafiyarsu cikin zuciyoyinmu, wasu su koya mana...