42

2.7K 215 5
                                    

👑 👑 👑 👑 👑

💖 💖 💖 💖 💖

💍 💍 💍 💍 💍

...ME RABO KA DAUKA 42

✍️AMMIN SU'AD

Shatuuu095@wattpad

KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

*ummy ontop, Sadiya maitama, Munix, Sasha, my Najeeyba, Ammasheikh, khadija DRB and unman beauty the page is yours*

Washegari, ana assalatu Ismail ya fito Daga dakinshi zuwa na raudha, Tana zaune kan sallaya da alama tadan jima da tashi Quran ne gabanta, jin an bude kofa yasa ta dago idonta ta zube kan fuskarshi wadda hasken wutar toilet ya haske Yana cikin jallabiya Fara tas, karasowa ciki yayi Yana fadin

"kin tashi kenan? "

Sunkuyar da kanta tayi tace

"Eh, barka da warhaka"

"barka dai, muje palour muyi nafila"

Mikewa tayi da carpet din ta bishi Yana gaba, raka'oi biyu sukayi sannan ya Dora hannunshi yayi mata addu'a, Yana gamawa yaji ana kokarin shiga sallah, mikewa sukai yaja ta sallar, suna idarwa Bayan sunyi adduoin su kowa daban daban, tace

"ina Kwana?"

Kallonta yayi yaga tana Dan lumshe ido, wani Irin kyau yaga tayi mishi,

"lapiya lau, how was your night? "

Bude idonta tayi kadan tace

"Alhamdulillah"

Kanshi ya kada yace

"jeki ki kwanta"

Kamar kuwa yasan bacci take ji, ta Mike ta nufi dakinta ta kwanta bacci babu jira yayi gaba da ita. Shikuwa Ismail Quran data Bari ya dauka ya shiga tilawa wajen karfe shida ya kammalla, dakinshi ya shiga ya canza kaya Zuwa jersey red da white da canvas red, har ya fara Kama stairs se ya dawo ya tura kofar tana kwance har lokancin, fanka ya kashe mata don yaga sanyin ACn ya cika dakin, fita yayi zuciyarsa na tuhumar shi akan wannan over protective akan raudha, shi kanshi ya rasa dalili Amma yasan amanarsa ce kuma dole ya kula da ita. Ta baya ya fice ya tafi strolling wanda aladarsa ce Tun yana UK.

Bakwai da rabi raudha ta Farka saboda sanyin da take ji, agogon dakin ta kalla hakan yasa ta duro da sauri ta shiga bayi, wanka tayi sannan ta fito ta shirya cikin cote divoire maroon, zani ne da riga very matured, simple dauri tayi ta Fesa turare ta gyara dakinta, parlon ta gyara ta maida komai yadda take so, agogo ta kalla, takwas saura, sauka tayi kasa nanma Daidaita gurin tayi sannan ta shiga kitchen, wow kawai take fada, kallon kitchen din ta tsaya Yi tana tunanin abinyi, fitowa tayi ta jona electric incense burner, sannan ta hau sama haka tayi kafin cikin sanda ta bude dakin da take zaton na Ismail ne, babu kowa ciki hakan yasa cikin sauri ta gyara komi sannan tasa incense sticks. Kasa ta sake komawa da waya Tana kiran Mami, da murna ta gaishe da mami

"auta yakike? Ya megidan?"

Wani Iri taji wai Itace mai miji tab

"duk lapiya kalau"

Yan nasihu ta kuma Yi mata sannan ta katse kiran, hawayen daya jika mata fuska ta goge sannan ta nufi kofa inda ake knocking, bata tambayi waye ba ta bude Don duk zatonta Ismail ne, Tana budewa taga khausar da kuyangi biyu dauke da manyan basket, da murna ta tare ta tace

"Ku shiga mana"

Shigowa sukai tana ta tsokananta, dariya kawai raudha keyi duk se taji hankalinta ya dan kwanta, ko zama basui ba khausar tace

...ME RABO KA DAUKAWhere stories live. Discover now