👑 👑 👑 👑 👑 👑
💖 💖 💖 💖 💖 💖
💍 💍 💍 💍 💍 💍...ME RABO KA DAUKA 08
Shatuuu095@wattpad
✍️AMMIN SU'AD
🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
Fitowarta kenan a wanka, abinci ta gani Jere kan tray komai tsaf , mamaki ne kwance saman fuskarta yau satinta biyu a gidannan baa taba bata abinci ba se Yau lallai me martaba ya dawo , bata sake kallon abincin ba ta Fara shirinta tana gamawa ta janyo wayarta ta turawa Ahmad daddan text sannan ta dauki jaka ta fito, kicibis sukai da mashida hakan yasa ta tsugunna ta gaesheta amsawa tayi sannan tace "wayace a kawo min abinci? " kasa ta kalla sannna tace "hajja ce " murmushin takaici raudha tayi sannnan Tace "ki mayar da abincin kice axumi nake kuma nagode" Bata jira me mashida zatace ba ta wuce inda baba Alkasim Ke tsaye Don ta dade da daina yiwa hajja sallama Tunda tai mata wata tsawa tana cewa karta dameta.
Cike hall din yake da students suna jiran lecturer ya karaso , inda ta hango ruwaida can ta nufa as usual suna ta surutu itada ridwan, sallama ta musu sannan ta xauna nan suka Fara hirarrakinsu.
Ruwaida da ridwan 'yan asalin garin jos ne dake jihar plateau ne, iyayen su maza yaya da qani ne. Mahaifiyar ruwaida ta rasu Don haka mahaifiyar ridwan ta dakko ta hada da ridwan ta riqesu dayake wata biyar ne tsakaninsu. Tundaga primary suke makaranta daya har suka gama, inda raayinsu ya banbanta shi ridwan engineering yakeso ita kuma food science and technology, haka ridwan ya hakura suka cikata food science din. Xancen Kace shakuwa ce kadai tsakanin mutanen nan kayi kuskure wata Irin kwantaciyar soyayya ce wadda Kai kanka idan ba zama Kai dasu ba bazaka gane ba. Suna Tsananin son junansu ba tareda sun ankare ba. Wannan kenan
"fulani Kwana na Nawa ina kiranki bakya daga wayata? " yaya sunusi ke fadin haka lokacin da ya kira fulani a waya, gyara kwanciyarta tayi tana fadin "yaya sunusi kai hakuri, I was carried away ne " yaya sunusi babban Dan wazirin sarki Suleiman ne, tun fulani na Yarinya yake sonta, haka yayi ta yawo DA wannan son har ta girma ta mallaki hankalinta ya sanar da ita Amma ta nuna masa bata da Interest akanshi, duk da haka Bai hakura ba a cewar shi ai wanda ya nace shi zai dace amma ni nasan ba kowa Ke dacewar ba musamman akan raudha wadda yanxu zuciya, ruhi da gangar jikinta gaba dai suna karkashin ikon Ahmad, se yadda yayi da ita , ita da kanta Tana mamakin son da takewa wannan bawan Allah shi Baifi yaya sunusi kyau ba ko kuan Hali amma gaba daya ta xauce da soyayyarsa. Ji tayi kiit alamun an kashe wayar, zaro ido tayi ta duba wayar Ashe magana yake ta mata bataji ba, kanta ta dafe tana murmushi Sega text dinsa ya shigo
Fulani bansan dalilin wannnan kin da kike min ba, amma babu damuwa kila ko kina ganin ni ba dan sarki bane ko? Matsayinmu ya banbanta ko? Babu damuwa ki kula wanda kikeso ni zan jira har ki dawo gareni.
Wani Irin tausayunshi ne ya rufe ta Lokaci daya, kwatakwata ta rasa dalilin da yasa ta kasa amincewa da yaya sunusi. Nan ta Fara tuno nasihun Aziza akan Kada Ta wulakanta saurayi ta lallaba su rabu lapiya, hakan yasa ta jan doguwar numfashi sannan ta Fara neman layin Aziza, sun jima suna waya kafin suka rabu.
Shekaru shudewa suke, watanni na wucewa, ranaku kamar jansu ake yayinda kowacce awa ke tafiya hakan na sake kusanta mu da kabarinmu... Allah yasa mu cika da imani.....haka abin yake ga matashiyar fulanin sarkin daura. Yau ta cika wata daya da wani abun cif cikin masarautar ta zazzau. Wanda take ganin kamar ta shekara Dari, Tun dare take faman shiri kamar wadda zata bar kasar, Tana son Zuwa mid semester break DA suka samu. Bayan isha'i taje tayi sallama da sarki Hashim, tambayarta Ya dinga Yi ko takura mata ake Shiyasa take son tafiya, nuna masa tayi kawai missing gida da iyayenta take Tana so ta gansu. Da Wannan ya sallameta Bayan ta koma daki ya turo amintaccen bawansa ya kawo mata sako cikin envelope, tana budewa taga kudi ne ciki, Aiken godiya tayi sannan ta cigaba da shirinta.
Tsaf ta gama shirinta cikin plain gown ta voile peach an mishi sirfani da zare maroon da stone work me kyau. Saboda doguwar tafiyar da zatayi yasa Batayi kwalliya ba, powder ce zalla Se lip balm, mayafi maroon ta yafa sannan ta zura flat maroon takalminta, haka take ba sosae take saka high heel ba saboda babu laifi tana da tsayi hakan yasa Bata amfani da irinsu. Straight part din hajiya lubna ta nufa inda ta sameta tana karyawa, murmushi saman fuskarta ta Fara mata maraba, itama fulanin da murmushi ta karasa durkusawa tana fadin "mama barka da safiya"
"barkanki, Kwana biu kin dauke kafa ko karatun ne ya fara zafi" dariya raudha tayi tana fadin "Kina raina mama, abubuwa sunyi min yawa ne yanxu ma sallama nazo muku zanje daura " Dan hade rai mama tayi sannnan Tace "amma se yau zaki fada min? " girgixa Kai tayi tana murmushi tare da fadin "ayya Mamata Kiyi hkri " da haka ta karasa dakin Afreen inda take ta bacci. Wani Irin duka takai mata a cinya wanda ya sata tashi a firgice, ganin raudha yasa ta zama tana yamutsa fuska tare da fadin "har Kinyi me Matar yayan? " harara ta maka mata Don Bata son tana kiranta Matar yayan, dariya Afreen tayi sannan tace "sati daya xakiyi ko? "
"Eh, Bari na wuce kar baba Alkasim yayi ta jirana " da haka sukai sallama ta fice Zuwa gurin hajja, bata jima ba ta fito ranta a bace sannnan mashida ta raka ta har bakin mota da trolley enta karami.
A cikin motar baba Alkasim Ke tayi mata hira, saboda ita ta Fara masa tambayoyi akan garin zazzau anan yayi mata alkawarin zasu ware rana guda su zaga Zaria idan ta dawo, sosae taji dadi.
Tunda tazo Zaria ta samu experience sosai akan rayuwa, tana danne zuciyarta sosai ganin bata taka hajja ba kamar yadda take mata amma mostly saboda Ahmad ne shine dalili, amma da tuni ta rama Tunda wannan jinin na sarauta na gudana cikin circulation dinta. Yau kam zuciyarta fal take da farin ciki zataga Mami da yan uwanta, Sede kasn zuciyarta ya dame ta da son ganin Ahmad, she's missing him iri over dinnan. Tana cikin wannan tunanin bacci ya dauketa. Bata farka ba Seda suka zo Kano, gaba daya ta gaji ga yunwa dake kwakularta, wani gidan mai sukai sallama sannan tacewa baba Alkasim suje down town suci abinci, godiya ya mata akan Ya koshi ita kadai ta shiga tayi ordering white rice da fish stew se lemu, haka tayiwa baba Alkasim shima, godiya yayi mata sosae. Cikin motar taci abinci kafin ta sake fadawa wani deep slumber din.
Karfe uku suka iso cikin daura, Tunda ta shaki iskar daura se wani farin ciki ya lullubeta kamar tayi ihu haka take ji, ga kuma wani freedom DA takeji kamar wadda akai freeing Daga prison haka takeji.
Vote
Comment
Recommend
Share
Follow me
I will always love you sosae, just show me d story is interesting by dropping your comments. Am grateful
©️ shatuuu ♥️
YOU ARE READING
...ME RABO KA DAUKA
General FictionKowacce mace a duniya allura ce a cikin ruwa ME RABO KA DAUKA. Kaddara kansa mu hadu da mutane da yawa, wasu mu cutar dasu, wasu su cutar damu, wasu su bar Sautin muryoyinsu cikin kunnuwanmu, wasu Takun tafiyarsu cikin zuciyoyinmu, wasu su koya mana...