👑 👑 👑 👑 👑
💖 💖 💖 💖 💖
💍 💍 💍 💍 💍
...ME RABO KA DAUKA 37
✍️AMMIN SU'AD
shatuuu095@wattpad
KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
*Guys I love you, result was pasted today and I did it Alhamdulillah. Thanks for the prayers*
*ISMAIL*
Ismail shi ne dan ummi na hudu wanda gaba da baya mata suka gewaye shi, shi kadai ne namiji cikin mata takwas. Ummi na sonshi sosae yadda mutum baya tunani hakan yasa take mishi lakani da DINAR wato gold. A spring yayi primary school dinsa, daga nan aka maida shi FGC Kano ya gama junior secondary school dinshi sai kuma aka maida shi key science academy dake nassarawa state inda ya kammalla senior secondary school dinsa.
Jamb score dinsa was low hakan yasa me martaba ya tura shi Sheffield university dake UK inda yayi achitecturing saboda shi baya son aiki karkashin kowa kuma he's good in technical drawing back in secondary, hakan yasa ya zabi zama architect don ya zama boss din kanshi. shekaru uku ya kammalla sannan ya koma donyin masters dinshi duk a same field, anan ya hadu da meeyna wadda kowa yasan encounter dinsu. Bayan ya gama ya koma yayi wani course na shekara daya.
Ismail baya da hayaniya kuma bayada kulekule hakan yasa bashida wata wadda yake ganin zai iya aura matsayin uwar yayanshi. Tunda yake basu taba maganar aure da iyayenshi ba se kwatsam suka kawo mishi zancen auren raudha dukda yaso ya kawo zabinshi amma haka yake ganin bazai iya ketare umarnin mahainfansa ba, hakan yasa ya amince without a second thought kuma yana sake addu'ar Allah yasa hakan ya zame masa alkhairi.
Bakin wando ne jikinshi da farar top, kafarsa Sanye cikin covered baki, yayi kyau. Cikin wannan gentility din nasa ya taka zuwa bangaren ummi, tana zaune kan sofa gefenta Anty mabrukha, yaya Fatima(1st born din ummi), yaya fauza da yaya Hamida dukansu yayyan Ismail ne suna xaune hannun yaya Fatima dauke da littafi da pen, suna rubuta adadin kayan da Za'a siyo na lefe. Gefensu ya zauna suka gaisa yace da ummi
"ummi Kina nemana ko? "
Glasses din idonta ta cire ta dubeshi tace
"Yawwa so nake ending week dinnan Kaje daura ka gaida iyayenta sannan ka ganta"
Kanshi ya Sosa yace
"to ummi Allah ya kaimu, zanyiwa Ammar da Salim magana se muje"
Cikin jin dadi ummi Tace
"Allah yayi maka albarka idan ka dawo mayi zancen inda zaku zauna"
Kanshi ya kada ya dubi immediate dinsa yaya fauza yace
"ummu naeeym idan kin gama ina nemanki"
"ango ango ango, muje yanxu ma inji Menene "
Tare suka fito ya dubeta yace
" ki Bari zanzo har gida na sameki"
Kanta ta kada tace
"Tohm bros se naji ka" daga haka suka rabu.
Ranar asabar karfe biyu na rana Ismail, Ammar da Salim suka iso Masarautar daura, AJ ne yayi musu iso ciki har part din Mami. Ismail na cikin bugaggagiyar getzna ash se maiko take, hula da Takalmi bakake se agogon Rolex baki yayi kyau karshe very responsible.
Mami na Zaune itada Aziza da kulthum su Ammar suka shigo, kan carpet duka suka zauna cikin girmamawa suka gaisa da mami, itakuma ta amsa with all fara'a, gaisawa sukayi dasu Aziza, daga nan sukaje gurin ma, Bayan sun dawo AJ ya tafi dasu part dinsu Don suci abinci, shikam Ismail ya yadda da zancen ummi da tace mutane ne masu kirki da karamci ya gani kuma ya gaskata. Suna gamawa sukai sallah sannan suka tafi wajen me martaba, yayi farincikin ganinsu kuma ya tarbesu sosae. Gurin Mami suka koma Don Yi mata sallama anan tace
YOU ARE READING
...ME RABO KA DAUKA
General FictionKowacce mace a duniya allura ce a cikin ruwa ME RABO KA DAUKA. Kaddara kansa mu hadu da mutane da yawa, wasu mu cutar dasu, wasu su cutar damu, wasu su bar Sautin muryoyinsu cikin kunnuwanmu, wasu Takun tafiyarsu cikin zuciyoyinmu, wasu su koya mana...