10

2.5K 216 3
                                    

👑 👑 👑 👑 👑 👑 👑

          💖 💖 💖 💖 💖 💖

                  💍 💍 💍 💍 💍 💍

...ME RABO KA DAUKA 10

Shatuuu095@wattpad

✍️AMMIN SU'AD

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

Bonanza..... Allah ya kara daga Nigeria, up! Up! 9ja

Cikin matsanacin farin ciki ta fito Daga last paper, Kan gossip chairs dake gefen hall din ta xauna. Wayarta ta ciro ta Fara kiran baba Alkasim Don yazo daukarta so take ta wuce daura batason sake Kwana a Zaria. Bayan ta gama Sega kiran Ahmad ya shigo, Cikeda dauki ta dauka tana kashe murya, hira suka danyi duk yawanci akan exams dinta ne, dayake yau ta kammalla exams dinta na first semester. Tambayarshi tayi kan Yaushe zai dawo yace Se karshen shekara, gashi yanzu muna April, nuna masa yadda tayi missing dinsa tayi sannan suka Yi sallama.

Zaman raudha gidan sarkin zazzau haryanzu bata canza zani ba, wulakanci, tsawa da tsangwamma shi ke rabasu da hajja, nawwara da sumayya da suka Fara mata wulakanci cikin ruwan sanyi take gasa Su, Abu ne data sani zata Bari hajja tayi mata komai amma banda yayanta Don Duk Abinda suke takama dashi itama tana takama dashi. Mu'ammularta da Afreen kuwa kullum Abu gaba yake sake yi, duk yadda hajja taso ganin ta katse abin Abu yaci tura, Don ita a cewarta Bata so raudha ta samu rangwame a gun ko mutum daya cikin gidan. Most of the times, raudha idan ta kadaice takan tuna lokaci daya data kuskurowa hajja Amma ta kasa tunawa, Don from the scratch hajja ta nuna mata tsana kirikiri wadda ta rasa ta mecece, Duk Wannan abun da ake Ahmad yana samun labari Daga gurin amintacciyar baiwarsa,  wadda na rasa wacece, Duk wani move din raudha ko kuka tayi Se an sanar masa a sirrance ba tareda sanin fulanin ba. Abu daya Ke bawa raudha mamaki shi ne yadda kullum sukai waya se yace karta damu da duk Abinda zata gani gidansu na Lokaci ne Watarana zai wuce hakan ya tabbatar mata halin hajja ne haka dukda bai fito ya nuna da ita yake ba.

Bayan sallar ishai suka iso Masarautar daura, dayake hutar da baba Alkasim tayi ta biyo commercial car, a kofar baya ta sauka, dogarawan gurin suka karaso suna haska su, dagowa tayi tana binsu da kallo , suna ganinta suka xube suna kwasar gaisuwa tare da wani Irin kirari , batace dasu komai ba Don da alama yau isa da takamar ta tashi, sallamar driver tayi ta nufo gida, su kuma suka biyota da kayanta.

Bangaren Anna, mahaifiyar sarki Suleiman ta Fara zuwa, Matar na Zaune Da bayinta suna mata hidima, Daga gefe Mami ce da alama ziyara ta kawo mata, Matar ta tsufa sosae Don kaf cikin matan sarki Hassan me murabus ita kadai ce a Raye, Duk Bayan Kwana biyu sarki Suleiman Ke ziyartar ta, yayinda yau idan Mami taje gobe MA xataje haka suke. Mami Batayi mamakin ganinta ba Don ta sanar mata zuwanta, gaeshesu tayi Anna nata tambayarta karatu da kuma Zaria, daga haka suka ci abinci sannan suka koma ciki itada Mami Bayan sun tabbatar bata bukatar komai.

Washegari karfe Sha daya na safe, raudha ta gama shirinta tsaf cikin hadadden pink da ash din material skirt da riga, fitowa tayi ta nufi bangaren MA, Tana zaune kan leather seats din dake dankare cikin parlour, DA faraa ta gaisheta sannan ta mata sallama. Daga haka ta koma gun Mami dake zaune Tana duba riyaddus salihin,
"Mami na fito " dagowa Mami tayi ta bita da kallo kafin Tace "to fulanin sarki, a gaida Aziza "

"Mami zataji, Kwana hudu zanyi Se na tafi Kano Nayi sati ko? "ta tambaya Tana langwabar da Kai,

"ya kukayi da Abbunki? "ta tambaya

"yadda na fada miki haka yace"

"then sai Kiyi hakan, ku tafi Karkiyi dare Allah ya kiyaye. "

Bayan maghrib likis suka iso Abuja da driver Mami, straight gidan Aziza ya kaita dake kurudu estate, ko shiga baiyi ba ya juya kan zai Kwana kaduna , da kanta ta ja trolley dinta Bayan security din gidan ya mata tambayoyi dukda yaga kamaninta da madam din gidan.  Wannan ne Karo na farko da raudha ta Fara zuwa gidan Aziza , knocking tayi kusan sau uku kafin wata middle aged mata cikin uniform tazo ta bude mata kana ganinta kasan bata jin hausa, raudha ce ta Fara fadin
"good evening "

"evening darling, raudha right? " Kai ta kada hakan yasa Matar sakin murmushi tare da fadin "please come in"a gajiye take binta har suka shigo cikin hadadden purple parlour wanda yasha wasu haddadun leather seats, babu kowa ciki Se kamshi da sanyi da Ke tashi. Nuna mata staircase tayi tace mata suna sama. Aje trolley tayi anan ta nufi parlour sama, dariya da kamar ihu Ta Fara ji na muryar Aziza , tana Sanye da half vest da bum short suna guje guje itada yaya Mas'ood , kawai tsayawa tayi tana kallonsu, Seda suka yo gurinta sannan Mas'ood ya tsaya Yana maida numfashi itama axizan haka kafin tazo ta rungumeta, hannunta ta kama suka zauna kan carpet dukkansu fuskokinsu dauke da murmushi, raudha ce ta Fara fadin "yaya ina yini? " shima da murmushin yace "lapiya lau fulani, ya hanya dasu Mami? " "lapiya lau.... ta amsa sannan ta maida dubanta ga Aziza wadda Ke ta kallonta......ya zeeza Anyini Lpy "
"lpy lau fulanin sarki, ya kika baro kowa" Hamma raudha tayi kafin tace "suna gaesheku " tashi Aziza tayi ta bude fridge dake cikin parlour ta kawo mata abu a jug, tana budewa taga favorite mango juice dinta tane, ai kuwa ta dinga Sha kamar babu gobe, Seda ta gama sannan Aziza ta rakata dakin da zata zauna, komai neat kamar baa shiga, toilet ta nuna mata sannan ta fice. Ta kusan Mintina ashirin tana wanka kafin ta fito, anan ta samu trolley dinta, simple abaya ta zira ta saka farar hula sannan ta fito parlour, suma da alama wanka sukai Don sun canza kaya, zama tayi nesa dasu tana kallon Film din da ake A
Tashar Bollywood
"sakko muci abinci Fulani "muryar zeeza ta katse ta, Dama yunwa takeji Don haka ta sakko, shima favourite dinta ne fried rice da hadadden colslow, sunaci babu mai magana har suka gama sannan aka zo aka gyara gurin tare da fesa room freshener, nan sukai ta hira har Tara tayi raudha tayi excusing kanta akan zata kwanta.

Tana gama cire kayanta ta saka nighties enta ta hau gado ta Fara kiran abbu, basu dade ba yace ta kwanta ta huta, nan ta Kira Mami sannan Ma . Tana gamawa kiran Ahmad ya shigo, cikin wani murya me taushi raudha ta dauka tace
"your majesty ya yini lapiya? "

"lapiya lau queen dita, Kinje abujan?"

"nazo, ya can din and how u doing?"

"fine darling, just terribly missing your cute face, ki Turon Picxxx enki plz "

Sosae fulani taji dadi, "nima haka and I'll do that ranka ya dade"

Haka suka ta hira yana fada mata brother dinsa dake karatu a Nairobi zai dawo Nanda sati biyu, nanne raudha tace "dear, in tambayeka? "

"ina jinki yanmatana"

Gyara kwanciyarta tayi daidai lokacin zeeza ta leko ganin tana waya ta juya lokacin karfe Sha daya da Rabi "Ku hudu ne kawai 'yayan hajja? "

Murmushi yayi Yana girgixa Kai yace "Eh, ni, imran Se Sumayya da Nawwara auta "

"ayya Bakuda yawa kenan"

Murmushi yayi yace "Eh kun fimu yawa ai "

©️ shatuuu ♥️

...ME RABO KA DAUKAWhere stories live. Discover now