50

4.9K 250 17
                                    

👑 👑 👑 👑 👑

      💖 💖 💖 💖 💖

            💍 💍 💍 💍 💍

...ME RABO KA DAUKA 50

✍️AMMIN SU'AD

shatuuu095@wattpad

KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

*This page is dedicated to my three brides khaltum bukar Abba, ummukulthum habib Kwalam and halimatusadiya zakari, Allah bada zaman lpy yasa a daura kuma a shiga a sa'a*

*Final chap*

7 months later

Cikin wata bakwai da ya gabata Amin ta haifi kyakyawar 'yar ta me Kama da raudha, ranar suna aka sawa Yarinya Rabi'ah ana kiranta Abida sunan mamansu Abid, yaran murna kamar zasu me sunyi kanwa, basu daukarta saboda Mimi Tace sunyi kankanta Amma kuma kullum ana dawowa daga school zasu je jikin cot dinta suyi ta lekenta, suna son yarinyar kullum se sun siyo mata sweet ko chocolate wai tasha idan Mimi tace tayi kankanta se suce a aje mata har ta girma. Hakan yana saka Amin cikin farin ciki Bayan haihuwar da wata biyu ta kammalla schooling dinta a base, hankalinsu gaba daya a kwance yake masters dinta ma prof yace zata Fara da zarar abida tayi kwari.

Bangaren Imran da meeyna an kai kudi, anyi biki anyi shagali na gaske, raudha Kwananta hudu sannan ta dawo kano. Meeyna ta tare anan Abuja saboda can akai transfer dinsa da aiki. Meeyna ta riki imran kamar yadda imran ya riketa, kullum suna cikin kwanciyar hankali da soyayyar juna.

Hajja jiki ya fara sauki, me martaba Daya tabbatar ta axabtu ta gane me rayuwa Ke ciki, yasa imran da meeyna suka tafi da ita Germany, watanninsu biyu suka dawo hajja ta fara tafiya dukda baiyi kwari ba, nan ta cigaba da therapy din da ake mata. Tayi nadamar abubuwan da ta aika ta, se yanzu tasan ka ki naka se duniya ta soshi sannan kaso naka duniya ta soshi, yanxu ta gane rayuwa ba komai bace ba a bakin komai take ba. Yaran da ta nunawa so fiyeda komai take rashin mutunci kansu gashi Tun ba aje ko ina ba sun Fara gasata. Hajja yanxu ko ganin nawwara bata sonyi, sau da yawa tana fadawa Ahmad ya riqe matarsa basai tazo ba ta yafe gaisuwar da take zuwa Yi.

Bangarensu Ahmad babu wani cigaba, aure yake son karawa amma me martaba yace Tunda nawwara ya zaba to haka zai karashe rayuwarsa da ita. Bakin ciki ya zamewa Ahmad normal mood, kullum yana cikin Balai da tashin hnkli, tsoronshi da take Dan yi DA yanzu duk ta daina. Sun riga sun tare a gidansu kullum yana yawon siyo abinci, ya rame ya lalace bashida wata kwanciyar hankali, Yana shigowa gida zai kulle kansa cikin daki don kar Taxo ta daga masa hankali. Yayi da nasani Yafi million times, Istighfar babu Wacce bai yiba amma kullum gidan jiya, sau biyu tana Zuwa ayi mata criminal abortion, ranar da ya samu labari kamar zaiyi hauka, hakan yasa yaje ya samu me martaba ya fada masa halin da ake ciki. Dukda yaji Bbu dadi amma se yace yaje ya cigaba da hakuri, ranar Ahmad yayi kuka yayi Dana sani Marar amfani cuz it's too late to cry when the head is cut off. Bayan sati biyu me martaba ya kirashi ya bashi invitation card na aurensa da yar gwamnan zamfara nusaiba, dukda bai taba ganinta ba ranar murna baa magana. Haka akai aure nawwara bata sani ba se ana gobe zaa kawo ta bori ta dinga yi da threat kalakala, cikin nitsuwa yace Wallahi idan tayi masa hauka zai sake ta hakan yasa ta sarara masa, gashi su Afreen da sumayya sukai mata tas.

Raudha ta kammalla degree dinta cikin lokacin da aka diba, murna dai ranar kada Ismail yaji labari, sunyi murna sunyi farin ciki at least zasu kasance tare har zuwa lokacin da zasu deciding inda xataje. sati daya suka dada a Zaria suka kammalla parking sannan aka rufe gidan suka koma Kano Cikeda farin ciki. Daura ta Fara zuwa tayi kwanaki hudu shikuma Yaje America wani course na month daya, Abuja taje nan ma kwanaki uku tayi , sannan ta dawo gidan ummi ana rainon ciki. Cikin baya bata wahala wani sosai, Kwana biyu dazai dawo ta koma gidanta ta kintsa, soyayya me ban shaawa, suna xaune cikin aminci da salama.

...ME RABO KA DAUKAWhere stories live. Discover now