09

2.4K 222 2
                                    

👑 👑 👑 👑 👑 👑

      💖 💖 💖 💖 💖 💖

              💍 💍 💍 💍 💍 💍

...ME RABO KA DAUKA 09

Shatuuu095@wattpad

✍️AMMIN SU'AD

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

Issa goal! We did it, we made it am proud ooo amma Nigerian...

Kamar an jefo ta haka ta fado cikin parlour inda Mami ke Zaune itada AJ da Abdullahi, da alama hira suke Don gaba daya fuskokinsu da faraa akai, kan Mami ta fada Tana fadin "I missed you mamina " riko hannunta Mami tayi ta dawo da ita gabanta yadda zata na ganinta, fuskar Mami takasa daukewa Da kyakyawan murmushi tare da mamaki Don raudha bata sanar da kowa zuwanta ba,

"fulani, daga ina da tsakar ranar nan " Mami ta tambaya, bata amsata ba se gaeshesu da tayi cikin girmamawa, suma duka amsawa sukayi Cikeda kulawa da soyayya sannan suka tambayi yanayin karatunta. Amsa ta basu kafin ta dubi Mami da ta kura mata ido Tace "Mami, nida baba Alkasim ne shi ya kawo ni " da yake Mami tasan da shi yasa ta dubi AJ tace "AJ, kasaka a bashi masauki ya huta DA duk abin bukata Zuwa lokacinda zai juya zaria" kai ya Kada sannnan ya amsa mata kafin ya fice, shima Abdullahi Miqewa yayi yana fadin "Mami Bari Naje fada, kafin na wuce gida "

"Allah ya temaka ya bada sa'a, sannan kayi tunanin maganar da mukai"

"Inshaaa Allah Mami " dubansa ya maida kan raudha yace "Anjima Za'a kawo miki kifi" sosae fulani taji dadi Don tanason kifi, godiya ta masa har ya fice, itakam tana son yanuwanta sosae.

Kallonta Mami tayi kafin tace "fulani wannan ramar da bakin na Meye? " wayanta raudha ta shafa ta bude Baki Tace "mamina karatu da xirga xirga shine ya ramar dani" girgixa Kai Mami tayi tace "ban yarda ba, Kodai baki jin dadin zaman gidan? " wani murmushi ta saki wanda Mami da ta Lura zata gane yake take tace "Haba dai Mami, basuda damuwa" kafin Mami ta furta Abinda take son fada Sega hanne da mama lami sun shigo fuskokinsu dauke da murna, Miqewa raudha tayi ta rungume mama lami tana fadin "na kewarki mamata" kafin taja hannunta suka zauna gaban Mami inda itada hannatu suka kwashi gaisuwa, hannatu gaisheta tayi cike da murna sannan ta fice Don Zuwa gyara mata daki.

"mama da gaske karatu ne ya ramar dani, GA wahalar xirga xirga " Kai mama lami ta girgixa badan ta yadda ba Sedan Bata san fulani taga kamar ta takurata, hira suka cigaba dayi. Sallamar jakadiyar me martaba suka ji, raudha ce ta Bata ixinin shigowa dayake suna xaune ne dakinta itada mama lami suna hira Bayan sallar ishai, gaisuwa ta kwasa gun fulani kafin ta sanar mata Sakon me martaba akan Yana son ganinta.

Fitowarta kenan daga gurin me martaba wanda ke tuhumarta dalilin Wannan ramar, shima karya ta masa sannnan taci abinci ta fito. A kofar ta tadda hanne tana jiranta , mamaki tayi Don tasan ita kadai tazo, karasawa tayi tana kallonta tace "me ya faru hanne? " da faraa Tace "ranki ya dade yaya Amin ce ta dawo" da kyau ta kalleta batace komai ba ta nufi hanyar dakin Ma, sallama tayi Sega Amin kwance cinyar MA, itama tana jin sallamar fulani ta taso suka rungume juna suna dariya. Zama sukayi suna ta hira har kulthum ta fito Daga study room, nan ta suka daura daga inda suka tsaya.

kallon wayarta take dake gefenta, Kwana biu kenan basui waya da Ahmad ba, se text Wanda kwatakwata Baya replying, hankalinta gaba daya a tashe yake. Sake trying number tayi tana ta ringing amma bai dauka ba, tsaki tayi sannan ta miqe ta dakko fanta Daga fridge ta Fara sha, kwankwaso kofa taji anyi, daidaita nutsuwarta tayi tace "shigo" Miqewa tayi tsaye Cikeda mamaki kawai se ta karasa ta rungume Firdausi. Firdausi yar gidan Barde ce, ajinsu daya tun primary dasu raudha, Don haka kawarta ce sosae, Bayan sunyi graduation Barde ya dauketa ya kaita Sudan karatu, dayake qaninsa acan yake Zaune Da iyalansa.

"fido Yaushe kika dawo babu sanarwa? " hannunta Firdausi ta kamo tace "shekaranjiya na dawo, shi ne nazo gaida Mami tace min kinzo jiya" murmushi tayi tace "Allah sarki, Kinyi kyau Kinyi kiba kamar ba karatu kike ba " dariya fido tayi tace "kar ki wani zugani, me sameki Duk kin zabge ko Ahmad ne? " Kai ta girgixa tace "ki Bari kawai, Ahmad ma tararwa yayi" nutsuwa ta sake yi ta riko hannunta tace "tell me Meke faruwa? " tashi tayi tasa lock a kofar sannan ta debo lemu da ruwa a fridge ta aje sannan ta debo soyayyan kifi cikin plate ta aje mata. Suna sha raudha ta Fara fadin "fido, zamana gidan sarkin zazzau ban taba ganin Marar mutunci Irin hajjan Ahmad ba........" ajiyar zuciya suka aje a tare su biyun Kan fido Tace "a haka kike Zaune fulani, cikin wannan ukubar? Ki sanarwa me martaba mana ki koma hostel" Kai ta girgixa tace "bansan kowa ya sani, saboda Bana son idan aurena ya tashi da Ahmad kar mu samu matsala " ido ta zaro fido Tace "fulani ina tunanin ki ya tafi a haka kike ganin yiwuwar aurenki da Ahmad? I Nayi tunanin yadda uwarsa ke gasa ki zaki hakura dashi Baki daya Ashe hasashe nane kawai " kallonta raudha tayi cikin mamaki tace "come on fido kamar baki San soyayya ba, kina ganin Wannan dalilin kadai ya isa nabar Ahmad. Haba dai" cikin hasala fido Tace "lallai raudha, ai bansan haka Ahmad ya gama da rayuwarki ba ,wannan kuwa shine babban dalili DA zai raba aurenku...."

"me yasa kike haka fido, son da nakewa Ahmad zan iya tolerating Duk Abinda mahaifiyarsa zatayi min, burin kowacce mace ta samu me sonta, yeah he loves me what next? Dan batasona ai bada ita zan zauna ba" bude Baki fido tayi ringing wayar fulani ya katse ta , Miqewa tayi har tana tuntube ta dakko wayar, kallon mamaki Firdausi Ke binta dashi a ranta mamakin me yake sata wannan zumudin , bangaren fulani a speaker ta sashi saboda a tablet ya kirata kuma earpiece dinta na dakin Amin.

"your majesty, ina ka shiga Kwana biyu haka? " fulani ta tambayi Ahmad tana dagawa

"Haba queen, Kinsan bana son complain ko? "

"dole Nayi complain Kwana Nawa baka kirani ba, ni kuma na kira kaki picking. Da ai ba haka Kake ba" cikin hasala take fadin haka, yayinda fido Ta zubawa sarautar Allah ido

"by now ya kamata ki Fara banbance tsakanin ina nema da na samu, kin gane "ya fada Yana wani smirk na rashin mutunci

"Ahmad what are you trying to say? Am confused " ta fada muryarta a tausashe

Dariya yayi me kayatarwa kafin yace "fulani yakike? .....bai Bari Tace komae ba ya cigaba da fadin..... Test na dinga yi Shiyasa ban nemeki ba, anyimin afuwa " fulani bata ce komai ba kawai ta kashe wayar saboda yadda ranta ya baci, me Ahmad Ke nufi? Don yaga tana sonshi komai? I shine zai Nayi mata Abinda yake so?

"fulani, Bari na wuce Kada momma ta bada cigiyata" bata jira amsarta ba ta nufi gida. Wani Irin bacin rai ne ya rufe raudha, saman gado ta koma ta kwanta tana tunanin Irin rashin mutunci daxatayi wa Ahmad, Bata Gama tunani ba Sega kiranshi ya sake shigowa, abin mamaki dauka tayi suka Fara hira cikin kwanciyar hankali. So kenan sede muce fulani tayi Nisa.

©️ shatuuu ♥️

...ME RABO KA DAUKAWhere stories live. Discover now