13

2.3K 208 2
                                    

👑 👑 👑 👑 👑 👑 👑 👑

💖 💖 💖 💖 💖 💖 💖

💍 💍 💍 💍 💍 💍

...ME RABO KA DAUKA 13

Shatuuu095@wattpad

✍️AMMIN SU'AD

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

Kwana biu fulani ta kara a Kano, ta Fara shirin komawa daura, ta riga ta sanar da yaya Abdulhamid akan da wuri take son komawa daura saboda akwai Abinda take sonyi, driver kawai ya kaita. Wannan ya sanya yaya Abdulhamid arranging komai.

Ta gama sallama da kowa, ta fito parlour janye da trolley enta kawai se gani nayi taja Ta tsaya Cikeda mamaki, yaya sunusi ne yayi daidai cikin parlour kan kujera Kace na matarsa ne, Yana ganinta ya Mike tare da miqawa yaya Abdulhamid hannu yana fadin

"Bari mu wuce Tunda gata nan ta fito. "

"gwara da kazo ai, driver na ya huta " kawai raudha kallonsu take tayi kicinkicin da rai, mamakin karfin halin yaya sunusi take. Kallonta Abdulhamid yayi yace

"fulani tunanin me kike haka? Kije ku tafi Kada kuyi dare" tsabar kuluwa bata ce komai ba ta zari Handbag dinta dake Kan center table ta fice, kuyangin gidanne suka kwaso kayan Zuwa booth din motar yaya sunusi. Sallama sukai wanda da kyar fulani ta iya musu ta shige gaban motar. Magana suka danyi da yaya Abdulhamid kafin ya zagayo ya shigo tare da kallon sashen da take, ganin fuskarta yasa shi reserving maganarsa, Seda suka fito Daga cikin unguwar sannan ya kuma dubanta wannan Karon wasa take da zoben gold din hannunta.

"ko ba komai ai kya gaida ni, Balle tundaga daura na taho kawai Don na maida Ke gida"

Bata ko kalli sashen da yake ba don ya gama ruining mood dinta, cikin zuciyarta ji take kamar ta make shi, ita ta roki zuwansa? Ko kuma wani ya rokeshi? Mts... Taja tsaki har bata san ya fito ba saida taji ya gangara gefen titi, kallonshi tayi da milky idanunta masu shining wanda Seka Yi tunanin hawaye ne kwance cikinsu Amma haka hallitar idanun suke, shima sunusi kallonta yake Cikeda mamakin tsakin da tayi masa, dauke kanta tayi ta maida kan mutanen dake ta kaiwa da kawowa. Ran Maza ya baci take ya rikide ya koma sunusi wanda yara suke tsornsa, cikin daga murya yace

"young lady watch out, ko da wasa kika Kara min tsaki se na Baki mamaki. Saboda ina sonki doesn't guarantee you ki raina ni OK? " bai jira amsarta ba ya ja motarsa yayi gaba. Yaya sunusi fari ne sosae kamar ka tabashi jini ya fito, siriri ne ga rashin tsayi Se shekaru hakan yasa yake da son girma sanann ya tsani Raini.

Dukda fulani taji wani iri na rashin jin dadi, saboda ita kanta tasan da gaske yaya sunusi na tolerating shit dinta, Duk iskancin da take masa ya kasa hakura kuma se ya shanye hakan yasa itada fati da Amin Ke masa lakabi da Dan anacen fulani, ko gezau Batayi ba se ma ciro wayarta da tayi ta Fara searching wani novel a wattpad. Karatunta ta Fara ta manta Allah ya hallici wani cikin motar.

Haka suka dinga tafiya kamar kurame, gwara ma raudha ta saka earpiece tana jin kida. Karfe uku na yamma suka iso daura, straight yaya sunusi ya wuce jibril store yayi parking, jin an tsayar da motar yasa fulani dago idonta, ganin inda suke yasa ta maida hankalinta Kan wayarta. Mintina wajen ashirin ya bata sannan ya dawo hannunsa riqe da ledoji, back seat ya zubesu sannan ya ja motar ya nufi kan giwa inda fadar sarki Suleiman take.

Yana parking raudha ta fito, shima fitowa yayi suka jera cikin main gidan. Fuskarshi kawai zaka kalla Kaga farinciki kwance kanta, gashi ga fulani.... Lol... Kamar kullum haka gidan yake mutane, bayi, kuyangu kowa na hadahada. A tsakar gida ta hango Amin da yaya kulthum suna xaune kan kunkuru da alama hira suke, maida dubanta tayi kan hanne wadda ta taho kamar zatayi tuntube don tarbar raudha, Bayan ta karbi handbag dinta sannan ta gaisheta, Bayan ta amsa ta maida gaisuwar Zuwa gun yaya sunusi wanda ya tsaya cak shi ala dole sai ya jera da Rabin ranshi raudha, wucewa hanne tayi Don yiwa Mami albishir din dawowar fulani. Cigaba da tunkarar gurin dasu Amin suke, da gudu Amin ta taso ta rungumeta, tare da dallawa sunusi harara wanda suke gaisawa da kulthum, a zahiri Amin ta tsani tarrayar raudha da sunusi Shiyasa basa shiri don harya sani, cikin kunne ta radawa raudha "ina kika samo wancan dan anacen? " murmushi raudha tayi Don ta fahimci wa Amin Ke nufi janye jikinta tayi ta riko hannun Amin kafin tace "Se mun zauna twiny. " dariyar shakiyanci sukai wadda ta jawo hankalin kulthum da sunusi, da sauri raudha ta karasa gun kulthum tare da rungumeta tace "sister me, ya gida Inata missing enki " itama hugging dinta tai Tace "gidan babu dadi ba kwanann, se wannan fitinaniyar" dariya sukai Don kuwa tasan da Amin take, hanyar chamber MA sukai suka bar sunusi tsaye, babu yadda ya iya ya gaida Mami sannan ya nufi gida zuciyarsa na tambayar dalilin da yasa fulani bata sonshi. Kayanta ya bayar aka kawo mata, Seda ta tabbatar ya tafi sannan ta nufo part din Mami Cikeda zumudi. A kofa taci Karo da sahib zai fito hannunsa riqe dana batuul DA sauri ta karaso tare da daukar Batuul tana juyi da ita, da farko kuka Batuul ta Fara amma ganin raudha ce yasa ta Fara dariya da hakoranta da basu Gama fitowa ba, shima cikin Doki sahib yace "Lil. Mom oyoyo" Cikeda faraa Tace Tana shafa kanshi"dawa kuka zo? Yaushe? " fada mata yayi akan jiya sukaxo da mummy da daddy (yayan Abdurrauf dasuke turke). Suna zaune Mami, Anty hajara (Matar yaya Abdurrauf) se Anty Rukayya (Matar yaya Abdullahi ). Hira sukeyi sosae saboda Mami bata da duhun kan surrikan yanzu, suma basuda matsala Don yayanta Baki daya mata daidai garesu with d exception of yaya Abdulhamid shi ne me mata biyu. Idan suka zo zama suke susha hira tana sake wayar musu da Kai Kan zaman duniya.

Tana shigowa gurin Mami ta nufa tareda rungumeta ta Baya Tace "Mami na na dawo, barka da wannan lokacin " murmushi Mami tayi tana sake jin son yarta cikin ranta tace "sannu da zuwa, ya kika barosu? " tashi tayi ta dawo Kan Anty hajara wadda Ke ta murmushi tace "lapiya lau, suna gaesheku " cikin wasa suka gaisa da aunties dinta sannan ta nufi dakinta Don watsa ruwa. Amra da nini ta tarar suna ta wasa, suna ganinta suka yo kanta suma duka yayan yaya Abdurrauf, yayanshi hudu kawai nini ce babba me sunan Mami, sahib, Amra se Batuul. Wanka tayi ta fito ta shirya sannan ta kwashi yaran zuwa inda suke hutawa itada Amin.

Hira suka dingayi duk yawanci Kan karatunsu ne se matsalar da Amin Ke fuskanta itada Zahraddin BF dinta tane Dan gwamnan jigawa da suka hadu a airport.

"Kinsan Allah, twiny rabuwa zanyi dashi "

"saboda me to? Yaya Amin "

"baya kirana se yayi sati biyu bai nemeni ba, kuma farkon haduwar mu baya haka. "

Dan murmushi tayi tana ayyanawa ranta cewa matsalarsu daya, basarwa tayi tace "Haba yaya Amin, Deen bai kyauta ba amma why sudden Break up. Change it to something "

Haka suka dinga tattaunawa, yawancin damuwar ta Amin ce Don raudha she's an introvert ta gaske, Bata yadda tayi sharing matsalarta da kowa ba, Shiyasa Duk tabi ta lalace saboda yadda tasa damuwar gidan sarkin zazzau da ta Ahmad a ranta. Mami da mama lami har sun gaji da tambayarta, kulthum wadda tayi tunanin komai ya Daidaita yasa Bata kawo komae cikin ranta ba.

©️Shatuuu ♥️

...ME RABO KA DAUKAWhere stories live. Discover now