31

2K 192 0
                                    

👑 👑 👑 👑 👑

💖 💖 💖 💖 💖 💖

💍 💍 💍 💍 💍 💍

...ME RABO KA DAUKA 31

Shatuuu095@wattpad

✍️AMMIN SU'AD

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

*Your comments is gingering me Up, thank you so much and this page is for every soul following my write-up, even if it's a glance. I appreciate that and I love you all...... Irin sosai fa*

Tana shiga dakinta ta Fara neman layin Ahmad amma Kwatakwata baya shiga, jin kiran sallar maghrib yasa ta saurin shiiga toilet donyin Alwala. Tana Idar da sallah ta sake janyo wayarta amma same yaki shiga. Kafin kace me hankalinta Duk ya tashi, cire kayanta tayi ta zura skirt da top ta dauki hijab dinta ta fito, kamar ance ta daga idonta kawai ta hango nawwara Zaune saman plastic chair tana waya se murmushi take, dauke kanta tayi zata cigaba da tafiya taji nawwara na fadin

"Amma ya Ahmad kasan ina sonka ko? "

Dif taji kwakwalwar ta ta dauke, cak ta tsaya tana booting Abinda taji nawwara na fadi, inasonka as in who's yaya Ahmad? Take wani side na zuciyarta yace Ahmad dinki mana, Kai ta girgixa tace noooo it's a lie, Ahmad can't do this Sede Nata personal Ahmad din. Da Wannan ta karfafa zuciyarta ta nufi part din hajiya lubna, dukda so take tunanin nawwara bada Ahmad dinta take waya ba amma zuciyarta ta rabu biyu wani na karyata hakan, cikin nitsuwa ta shiga tare da kirkirar murmushi tasa a fuskarta, sun gaisa da mama kafin ta nufi dakin Afreen, gimbiya yar sarki tana kwance ana mata tausa, ganin raudha ta shigo a hargitse yasa ta Miqewa da sauri ta sallame kuyangin nata, kafin ta kamo hannun raudha ta zaunar gefenta Tace

"Menene raudha? "

Muryarta na rawa tace

"Afreen Meye matsayin nawwara cikin gidannan? "

Take Afreen gabanta ya fadi ta zaro ido tana addu'a cikin ranta Allah yasa raudha ba taji zancen ba

"rikonta hajja keyi me..... "

Katseta tayi tace

"Meye tsakaninta da Ahmad? "

Ya Allah not now raudha ta fada a ranta Don gaba daya a tsorace take

"ba... Babu komai Karki... Wani damu"

Wani kallo raudha ta buga mata Tace

"ki fada min gaskiya"

"nace miki babu komai, Taya zan sani ni da ba shiga harkarsu nake ba"

Mikewa tayi Afreen ta rike ta tace

"wani abu kika ji ne? "

Hannunta ta cire kawai ta fice a dakin Don tabbas tana iya bige Afreen.

*KANO*

Sallaman sarki ne ya leko ya dubi jakadiya dake zaune a gun yace

"me martaba Yana son ganin hajiya babba da kuma tafida"

Cikin hanzari ta Mike Don discharging duty dinta, bangaren ummi ta fara zuwa wadda taci ado cikin jar shadda da aikin baki, kamaninta da tafida sun sake bayyana tana zaune cikinsu hidaya suna hira, personal maid dinta ta shigo Don sanar da zuwan jakadiya, ixinin shigowa ta bata Sega ta shigo ta gurfana tayi gaisuwa sannan ta isar da saqon me martaba Daga nan ta wuce bangaren tafida, me kula dashi ta bawa sakon ya shiga ya sanar dashi kiran gaggawa da me martaba yake masa.

Tafida ne ya fara isa cikin bakar jallabiya wadda take daidai idon samunshi, Yana shiga yayi gaisuwa ya sami guri ya xauna, baa dade ba aka sanar da zuwan ummi, jakadiya ta mata iso ciki sannan suka fice, gaesheshi tayi sannan ta dubi tafida daya gaisheta itama cikin kulawa ta amsa.

...ME RABO KA DAUKAWhere stories live. Discover now