👑 👑 👑 👑 👑 👑 👑 👑
💖 💖 💖 💖 💖 💖 💖
💍 💍 💍 💍 💍 💍
...ME RABO KA DAUKA 05
shatuuu095@wattpad
✍️AMMIN SU'AD
Madubi ta Kara dubawa a Karo na babu adadi , cikin super Holland green da purple dinkin plain zani da riga wanda yayi mata kyau, kwalliyar fuskarta nude ce babu wani heavy Dan ko brows bata jaba, dankunnenta da sarkarta purple ne masu kyau se veil din data yafa purple, tayi kyau kamar ba gobe. Anty Laila ce ta shigo riqe DA wani flat fari da purple din Takalmi ta aje mata tana binta da kallo Irin na yanmata fa Kinyi kyau, fuskarta ta rufe najin kunya tana zura takalman da aka aje mata
"Mashaaa Allah, fulani Kinyi kyau kamar Kinsan wannan kayan zance kisa"
"Nagode Anty " kafin Anty Laila ta Bata ansa yaya Abdulhamid ya shigo Yana fadin "fulani , fito mu tafi mana karmu makara " wayarta ta dauka sannan ta fito ta wuce parlon Anty farida donyi mata sallama , babu yabo ba fallasa ta amsa hakan bai dame taba ta fito su sultan da Anty Laila suka rako ta har bakin mota. A cikin mota suna ta hira da yaya Abdulhamid, nan ya biya ta shoprite yace ta zabo turare guda biyar, raudha tasan ta kan turare kuma tasan wa Za'a kaiwa hakan yasa ta zabo masu tsadar gaske yawanci duka Arabian ne.
Cikin wani hadadden parlor wanda yasha ado da tsadadden carpet, Manya manyan Tim Tim, wata farar dattijuwa ce da shekarunta bazasu Gaza kaiwa hamsin da biyar ba a duniya, tana cikin kaya na alfarma fuskarnan a sake. bayinta da kuyanginta sun zagaye ta suna faman mata hidima, jakadiya ce a gaba raudha na bayanta se Abdulhamid Daga gefenta, ciki ta shiga jakadiya ta sanar da isowar su , kafin ta fito ta musu jagora cikin parlour. Kawata se raba ido take lol, bawai tsoro take ba kawai dai abin bakunta take, Dan Masauratar daura ma ta hadu karshen karshe.
Suna shiga, kunyanginan suka marmatsa suna ta gaeshesu hade da Yi musu Kirari, kafin suka fice baki daya, ya rage se su uku, murmushi ta sake fadadawa tana yiwa raudha alamun ta karaso gurinta , a hankali ta taka zuwa gaban ta zuciyarta na tabbatar mata da son Wannan Matar. Tsugunnawa tayi gabanta tana fadin "ranki ya dade barka da rana" dariya tayi tace mata "ina maraba da zuwan yata, amma kina kirana da ummi ina babarki ce" murmushi itama tayi tace "to Ummi" maida dubanta tayi kan Abdulhamid wanda ke ta kallonsu yana murmushi, gaisawa sukayi sannan tace "ya na ganku babu kaya? Bayan dazu munyi waya da hajiya A'isha tacemin Kwana zatayi" kasa Abdulhamid yayi Da kansa yace "kayan suna mota " kai ta kada daidai lokacin aka fara shigowa da fruits drinks kalakala, ruwa kawai Abdulhamid yasha yayi musu sallama akan gobe zai dawo daukarta. Ummi ta tura a Kira autarta wadda zasu Yi shekaru daya da raudha Don ko ruwa taki sakin jiki Tasha. Shigowa tayi cikin straight skirt fari da bakar top se farar hula akanta, gaishe da Ummi tayi sannan ta dubi raudha wadda itama kallanta take tace "Ummi, Itace fulanin dauran? " murmushi Ummi tayi mata tace "Itace, yanzu kuje daki ki tabbatar taci abinci ta huta sai ku dawo muyi hira" Miqewa tayi ta mika mata hannu, raudha ta zura Nata sannan suka fice. Wani daki suka shiga Dan karami me kyau, kana kallonsa kasan na mace ne Don komai na dakin Baki ne da fuchsia pink. Zama tayi saman cushion yayinda khausar ta tura a kwaso kayan palour Ummi. dawowa tayi ta zauna Tana fadin "khausar, ending shekarar nan zan tafi BUK zan karanci mass comm. " Kai raudha ta kada tace "raudha, Abu food science and technology "
Hira sukai tayi suna cin abinci, raudha ta sake sosae DA yake ita batada wahalar sabo, khausar ma haka suna nan a Zaune step sisters din khausar suka shigo nan fa suka dinga hira kamar Dama can sun San juna. Se da sukayi laasar sannan suka je gaida kishihoyin Ummi, Ummi (Asma'u ) Itace uwargidan sarki Hussein tana da yaya Tara gaba daya mata ne se kwaya daya ne namiji yanzu haka yana university of Sheffield UK Yana Msc. Dinsa acan, hajiya safiyya (mama )Itace ta biyu tana da yaya goma Sha daya Maza da mata se Amarya hajiya Sadiya (Anty amarya) tana da yara bakwai.
Babu laifi sun tarbe ta da kyau, basu wani jima ba suka koma gurin Ummi, haka sukai ta Hira Don raudha ta sake. Bayn sallar isha'i Ummi da kanta ta raka raudha turakar me martaba, yayi farincikin ganinta, anan ta bashi taureren da tazo dashi Dama ta bawa Ummi nata, godiya ya mata sannan yayi mata nasiha akan rayuwa da kuma university har Yana fadin "banda Kinyi registeraton a Zaria ai DA nan zaki dawo" da haka ya sallameta ta koma dakin khausar.
Washegari, karfe uku yaya Abdulhamid yazo tafiya da ita, taji dadin Kwana Dayan DA tayi Don bazata manta karamin mutanen Kano ba. alkhairi sosae sukai mata khausar ta mata alkawarin zuwa daura ko kuma Zaria. Suna komawa gida Washegari ta koma daura.
"kin tambayi Mami ko me martaba dalilinsu na turaki gaida sarkin Kano? "mama lami ke mata wannan tambayar lokacinda Mama taje dakinta Don debe mata kewa. Shiru raudha tayi kafin tace "akwai wani abun ne? Na tambayi Mami tace wai abokin abbu ne " kai ta jinjina amma zuciyarta taki amincewa da hakan do haka kirum bazaa ce fulani taje gaida Ummk Asma'u ba, time will definitely tell...."mama ko akwai wani abin ne? Ki fadamin "murmushi tayi tace "babu komai fulani, kede Kiyi kokarin ganin zuciyarki bata zurmawa Ahmad da yawa ba saboda wani Lokaci " itakam raudha Ta Kasa fahimtar inda kalamun mama suka dosa tabbas su din abin dubawa ne Amma yaya zatayi, Abu daya ta sani son Ahmad ya rigaya daya gama da duk wani lungu na zuciyarta, gangar jikinta kadai ta rage ba mallakin Ahmad ba amma zuciya, ruhi DA kwakwalwar ta Duk na gunshi, har mamakin yadda take sonshi take kamar Wanda yayi casting spells a kanta, ko mai take Ahmad na ranta, idan hira take by mistake se sunanshi ya shigo , Mami ta dade tana tambayarta waye Ahmad amma se ta waske kawai.
"Amma me yasa baka tausayin wannan marainiyar zuciyar tawa ace kwananka uku baka kirani kuma ni idan na kiraka you won't pick. Haba mana BML " shiru Ahmad yayi har ta gama korafinta kafin yace "am very sorry beauty, abubuwa sunyi min yawa amma kina raina, na fada miki dalilin? " Kai ta girgixa tace "you don't have to, amma ka daena wahalar Dani ko text ne ka barmin Kace kana lapiya" yana tsananin son raudha saboda simplicity dinta, Tana mishi uzuri babban abin shine yadda take nuna mishi so dukda har yau bata fito tace tana sonshi ba amma ya tabbatar Tana masifar sonshi. "nagode beauty na miki alkawarin sonki har karshen rayuwata, bazan taba barinki ba no matter d situation " murmushin jin dadi tayi tace "alkawari kayi ko? " Kai ya Kada kamar tana gabanshi yace "I promise, so me ya faru Kwana biyu da Bamuyi waya ba? " a hankali cikin sassanyan muryarta ta Fara fadin "na Gama Duk shirin school, jibi zan tafi amma kasan ina zan zauna? " Kai y girgixa Yana fadin "se kin fada" Dan murmushi tayi sannan tace "a gidanku "dammm ya ji saboda yadda gabanshi ya fadi basarwa yayi Yana murmushin yake yace "Amma naji dadi Bari na fadawa hajja zaki.... "da sauri ta katse shi Tana fadin "no please, Karka fadawa kowa lemme be kawai, idan time yayi kowa zai sani kuma suyi farin ciki da abin " yaji dadin maganganunta hakan yasa shi fadin "Kinyi tunani me kyau , Kina da sanyin Hali am sure bazaki samu matsala da kowa ba. Amma Kiyi hkri "haka hiransu ya kasance har wajen maghrib kafin suka hakura sukai sallama.
Vote....... Comment....... Recommend.....share......follow me
©️ shatuuu ♥️
YOU ARE READING
...ME RABO KA DAUKA
General FictionKowacce mace a duniya allura ce a cikin ruwa ME RABO KA DAUKA. Kaddara kansa mu hadu da mutane da yawa, wasu mu cutar dasu, wasu su cutar damu, wasu su bar Sautin muryoyinsu cikin kunnuwanmu, wasu Takun tafiyarsu cikin zuciyoyinmu, wasu su koya mana...