39

2.2K 207 3
                                    

👑 👑 👑 👑 👑
     
      💖  💖 💖 💖 💖

             💍 💍 💍 💍 💍

...ME RABO KA DAUKA 39

✍️AMMIN SU'AD

shatuuu095@wattpad

KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

Cikin bakar jallabiya me green stones nawwara ta fito, Tana tafe cikin tafiya me matukar daukar hankali, sumayya na Zaune kofar fita tana making call, cire wayar tayi daga kunnenta tace

"ai fa babu zama se masifaffen yawo"

Ko kallonta Batayi ba ta wuce a binta don gani take yanxu Bata da lokacin kowa se na Ahmad, Kwana biu taga sumayya na mata wani wulakanci Tunda akai fixing date, so take ta nutsu ta Daidaita ta Don ita bazata dauki iskancin kowa ba.

"nafi minti talatin ina jiranki se yanzu zaki fito? " Ahmad ya fada lokacinda nawwara ta karaso bakin motarsa, kallonsa tayi tace

"matsalata dakai fada, Haba ace kullum Se kayi complain gaskiya I don't like this" ta fada Ranta a bace tareda bude front seat ta zauna Tana cin magani, Ahmad bai ce komai ba ya tada motar, kallonta yayi yaga yadda take Harare Harare

"am sorry, Kinyi kyau "

"nasani ai Tunda ni na shirya kaina"

Daga nan Ahmad bai kuma cewa komai ba Don baiji dadin maganar nan ba amma babu yadda zaiyi.

Wani joint suka je Don cin shawarma shi ne makasudun fitowarsu, shi baiyi niyyar fita ba nawwara Tace lallai se sunje hakan yasa bashida wani option Illa ya fito. Order su aka kawo musu, Ahmad ya dube ta yace

"armour "

Batareda ta dago ba tace

"yes armour"

"ya ina miki magana kina danna waya dago mui magana please"

Batareda ta dago ba tace

"amma kasan kunne keji ba ido ba ko?"

Bai ce komai ba ya cigaba da taunar shawarma, jin shiru yasa ta dago tace

"na dago tell me "

"bikinmu na matsowa wasu shiryeshirye kuke, kamarsu event and so on"

Rolling idonta tayi tace

"events biyar nake so, sannan kuma kaga ima da friends mu bakwai zakai musu anko na duka events din"

Tunda ta Fara magana ya hangame baki yana kallonta, nawwara ta Fara hauka ne? Events bakwai? Tabdijam shi inama yaga kudin yiwa yanmata biyar set bakwai impossible shi ba aiki yake ba.

"sunyi yawa armour ai se mu xubar da albarkar auren tun a titi"

"nasan haka zakace, so Kake Kawayena sui min dariya, gaskiya sede a Daga bikin ko a fasa"

Wannan Karon he's in shock Don ko magana bazai iya ba, kallonta yayi Se fada take ita dama tasan bazai yi ba, ba sonta yake ba if not Meye a event bakwai? Ganin zasu zama abin kallo yace

"OK see xa'ayi yadda kike so muje gida yamma nayi"

Mikewa sukai suka bar gun ran Ahmad a tsananin bace amma babu halin nunawa, Karo na farko da raudha tayi crossing mind dinsa, very reasonable and responsible soul.

Bangaren Amarya raudha babu wani abu da take planning karatunta kawai take saboda aure da sati biyu zata Fara exams. Amin ce da Fido se meeyna suke ta dabdalarsu, komai aka tambayeta se tace kawai yadda twiny tace. Relationship dinsu da Ismail Zamu iya cewa LA ba'asa babu laifi, su ba son junansu suke ba amma sun amince su zauna karkashin inuwa guda. A sati ya kan kirata sau biyu Zuwa uku ko kuma idan Yana son tambayarta wani abu.

...ME RABO KA DAUKAWhere stories live. Discover now