43

2.6K 222 1
                                    

👑 👑 👑 👑 👑

      💖 💖 💖 💖 💖

            💍 💍 💍 💍 💍

...ME RABO KA DAUKA 43

✍️AMMIN SU'AD

shatuuu095@wattpad

KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

Rufe kofar tayi sannan ta iso inda Ismail yake tsaye Yana jiranta, kallonshi tayi kamar yana tunanin wani abin

"muje na gama"

Key din motar ya bata, kin amsa tayi tace

"me zanyi dashi"

"muje Kiyi driving na gaji"

Dan dariya tayi tace

"ban iya ba"

Idonshi ya zaro yace

"Karki ce you're serious"

Dariya ya kuma bata kamar tayi committing wani crime

"serious ban taba gwadawa ba"

Wucewa yayi tabi bayanshi suna zama yace

"no way ki gama exams se muna fita training"

"tohm"

Daga haka suka Yi shiru, se can tace

"inason in siyawa su ummi abu"

Kallonta yayi yace

"OK ina zan kaiki? "

Shiru tayi tana tunani se can yace

"oops ashe ba Zaria muke ba, Bakuwa ce a kano"

Girgixa Kai tayi she never taught shima Yana da wannnan funny side din, a Kwana takwas da sukayi tare he's beyond ta fadi kirkin shi, bai taba barinta da damuwa ba, most time idan fita ba dole bace bayayi, idan ya fita kuma bai dadewa yake dawowa. Ko ba komai tana jin dadin zaman, mostly se yace ta dakko system dinta suyi karatu, Yana karantowa tana masa bayani haka suke.  Yau alhamis Tun dare yace ta shirya zasu je unguwa su gaida ummi.

A kofar jufatu enterprises na obasanjo road yayi parking, tare suka fito sunyi masifar kyau, se lokacin na lura da kayansu, Ismail na cikin voile sky blue ita kuma atamfa ce sky blue da Fuchsia pink a jiki, ciki suka shiga tana gaba yana bayanta har side din perfs zaba tayi yana gefe yana kallonta har ta kammalla. Wajen cashier suka je wani kallo ya buga mata ganin tana kokarin bude purse, kanta ta dauke kamar bata fahimci Abinda yake nufi ba, tare suka Mika ATM card dinsu, cashier ta dubesu baki daya alamun nawa zan karba, hannu yasa ya amshi na raudha sannan ya bada nashi. ledar na hannunshi bai ce komai ba har suka koma mota.

Cikin parlour ummi suka Fara shiga, come on zo kuga murna musamman da taga raudha tayi fresh ta Dan ciko alamun hankalinta a kwance yake, gaisawa sukayi sosae Tana ta tambayarsu yadda suke dukda Tafida kullum Se yazo gidan. Suna nan Zaune akai ta shigowa gaishesu, Bayan mutane sun lafa ummi tace

"raudha kuci abinci kuje ki gaida sauran matan gidan"

"Tohm ummi, khausar bata nan"

"Eh suna school itada farida"

Da kanta ta zuba mishi abincin sannan ta zuba nata , shiru sukai kowa yana cin nashi ummi na Dan yi musu hira. Suna gamawa aka kwashe kayan, dubanta ummi tayi tace

"Yaushe zaki koma Zaria?"

Dagowa tayi ta kalli tafida da shima ita yake kallo, ganin haka yasa ummi maida tambayar kanshi

...ME RABO KA DAUKAWhere stories live. Discover now