👑 👑 👑 👑 👑 👑
💖 💖 💖 💖 💖 💖
💍 💍 💍 💍 💍 💍
...ME RABO KA DAUKA 20
Shatuuu095@wattpad
✍️AMMIN SU'AD
🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
"kin tabbatar Ama yasan kina sonshi? " latifa kewa meeyna tambaya Bayan sun fito Daga lectures.
Alhaji mu'azu Adamu shine mahaifin Ameeyna Dan asalin garin gumel cikin jihar jigawa. Yana da mata daya hajiya sakina, yana matsayin secretary to the federal government SFG, yana zaune a Abuja. Yarsa kwaya daya ce meeyna Don haka suka dauki duk son duniya suka daura mata. Kyakyawa ce ta ajin farko very classy mace me ilimin Boko Dana addini saboda sun mata tarbiyya daidai gwargwado. Tayi primary da secondary duka a Nigerian Turkish college, Tana gamawa aka fara nema mata admission a London. Tana Architecturing Sheffield university.
Ameeyna mu'azu Adamu Ama kamar yadda friends dinta ke kiranta mutum ce me kokari da tsananin kamun kai batada hayaniya. Yanxu tana shekara ta biyu duk Bayan watanni shida take zuwa Nigeria Hutu. Kokarinta da hazakarta yasa wani lecturer dinsu hada ta da ISMAIL Hussein wanda yake masters dinsa anan Sheffield din shima Yana achitecturing. Ismail Dan Nigeria ne cikin garin Kano, mutum ne Wanda yake da wata akida na bai yarda yaga mace ta wulakanta ba yana girmama mata and he is very gentle bashida hayaniya Shiyasa mutane sukafi Kwatanta shi da mai girman kai wanda a zahiri ba haka yake ba.
Ismail ya bawa meeyna Duk wata gudunmawa daya kamata, ta fannin karatu dayake shi Yafi karfin na kirashi da guru sede nace he is an exceptional child. Duk abinda ya shige mata duhu cikin karatu to Tana kiran Ismail zaiyi clarifying komai, hakan yasa suka samu shakuwa tsakaninsu wani sain yakan fita da ita shopping, ko kuma suje eatery suci abinci ko wani park haka.
Duk wani kyautatawa gurin dan Adam Ismail na bata daidai gwargwado, Ashe bai sani ba hakan da yayi mistake ne, Don kuwa zuciyar meeyna ta cika Makil da soyayyar Ismail wanda shi ko digon feelings babu a tashi, kawai dai yana kyautata mata saboda an hadasu kuma shi kadai ta sani cikin garin se kawayenta biyu daya daga madina latifa se nu'aima daga Pakistan. Duk wani sign DA gesture da mace ya kamata ta nunawa namiji to meeyna tayi Amma kwatakwata Ismail yaki fahimta, bawai bai gane ba a'a ya gane kawai bayada interest ne akan hakan shi ne yasa yake jahiltar manufarta.
***
Wata iska me sanyi ta shaka tareda jin wani feeling na am safe fulani taji lokacinda kafafuwanta suka dira Kan tafkeken parking lot din masarautar daura, no place like home haka ta fada cikin ranta. Kallon lot din tayi yau yafi cika da motoci kamar ko da Yaushe, kalilan ta gane nasu waye yawanci na yayunta ne
"muje ko?" muryar imran ta katse mata tunaninta, Kai ta kada ta nufi kofar da zata hada ta da zauren gidan. Dogarawa ne ta ko ina se kirari suke mata, wani lokacin ta daga hannu, wani sain daga Kai wani lokacin shiru, imran Dai Dan kallo ne yana daga gefenta yana ayyana dama itama tana da isa da jin kai haka? Take zuciyarsa Tace itama fa yar sarauta ce, murmushi ya saki wanda babu Abinda Ke fita sai zallar kyau da kuruciya. Kamar Ko da Yaushe tsakar gidan wanda I can't estimate girmansa a share yake kal, kunyagu Ke ta faman Kai ka wo kowa na san discharging duty dinsa, da sauri taga anyo gunta hakan ya tabbatar mata hanne ce, take ta saki fuskarta, hanne na Zuwa ta durkusa ta Fara gaesheta cikin azama ta dago ta tana fadin "Haba hanne Kinsan banaso ko? " murmushi tayi ta karbi jakar hannunta kafin ta musu jagora bangaren Mami.
Kamar kullum tana zaune cikin shiga ta alfarma, fuskarta kunshe da faraa da kamala. Tana hango fulani ta Mike hakan yasa yarima, turaki, danmaje da Abdul Aziz saurin juyawa Don ganin wa yasa mahaifiyarsu Miqewa cikin azama, da gudu ta karasa ta rungume Mami tana dariya, kawai se su kaga ta fashe da kuka Abinda ya Kada cikin imran kenan, a sanyaye ya karaso ciki inda turaki ya masa nuni Don dama yasanshi.
"Menene abin kukan? Bakin samu sauki ba? " Mami ta tambaya Tana shafa bayanta, Kai ta kada batare da Tace komai ba
"ya isa to, jeki Kiyi wanka Duk yan uwanki sunzo " Miqewa tayi ta nufi dakinta da komai yake neat kamar tana ciki, Allah sarki maminta. Bayan tayi wanka wardrobe ta bude taci Karo da sababbin dinkuna da yawa, atamfa ta ciro daga ciki Fara ce se manyan circle na sky blue da yellow dinkin flowing gown. Tayi kyau haka ta fito nan taci Karo da zeeza tana faman Jan kafa, hakan yasa ta guntse dariya ganin yadda take Kai Kace gobe zata haihu."sannu yaya zeeza, Meye naga duka kunxo? "
"kin manta yau last week of june muke"se lokacin raudha ta tuna da meeting da suke na iya ya'ya after every six months, matsalolinta sunsa ta Fara manta abinda yake alada cikin gidan, gurin Mami ta koma nan take sanar da ita imran ya juya, bataji dadi ba taso Sui sallama Amma ba damuwa ta nemeshi anjima lefin babarsu ai baya shafesu ba. Bangaren MA ta nufa nan ta sami sauran sisters dinta suna ta hira, cikinsu ta xauna ana ta hira nan zeeza ta samesu. Bayan sallar ishai me martaba ya gayyacesu gaba daya cin abinci bangarensa. Bayan sun gama suka daura da hira se wajen karfe goma suka dawo dakunansu.
Mami, zeeza da fulani suna xaune kan rug din bedroom din Mami suna hira mafi yawanci akan rashin lapiyar fulani ce, anan mami ke fada mata ta taba yi sau biyu tana Yarinya an kaita Asibiti sukace asthma ce amma mild. To tundaga ranar Bata sake tashi ba Don Mami har ta manta da wannan batun.
Gaba dayansu suna xaxaune cikin garden din da yawanci me martaba ke hutawa, kowa ka gani fuskarsa cike take da annashuwa kowa cikin shiga ta alfarma yake, me martaba Yana zaune kan rug me jikin cheetah, Mami da Ma sun sashi a tsakiya. Daga gefe kuma mazan ne tundaga Kan yarima har AJ suma kan rug, Dayan side din matane suma gaba dayansu se tsakiyarsu kayan ciyeciye ne Kama Daga juices, fruit, pies, finger foods sannan manyan food warmers wanda aka dankara abinci a ciki. Haka aladar take.
Yarima ya fara bude taro da addu'a, Bayan an shafa Abbu yayi yan jawabai wanda duk sake tuni ne akan Watarana zai mutu ya Barsu Don haka suji tsoron Allah su rike zumuncinsu. Nan Mami tayi nata itama se MA. Bayan sun gama Dan maje wato yaya Abdurrauf ya gabatar da zancen Auren kulthum wadda ta tsayar da miji kuma Nanda sati biyu zata Gama final exams dinta. Kowa yayi farinciki tareda saka albarka, kowa yasan wa zata aura Dr. Mahfouz ne, bashida aure. Yana gamawa yaya turaki ya sako zancen professor Abbas yusuf akan Yana son asan da zamanshi, Abbu a take ya tambayi turaki yayi bincike nan turaki ya sanar dashi Abinda ya sani, sosae Abbu yaji dadi hakan yasa ya maida dubansa kan Amin wadda Ke ta boye kanta jikin yaya Habiba, zeeza da sulaimi dariya ta basu yayinda raudha ke zungurarta ta baya."ummul-Amin Kina son Abbas? " me martaba ya tambaya kowa ya maida dubansa kanta, sake boye kanta tayi jikin Habiba, anan ta rada mata ta amince
"Abbu tace ta amince" yaya Habiba ta fada fuskarta dauke da murmushi
Kai ya jinjina yace "Alhamdulillah, to kisani babu canji nan da ki gama makaranta se ayi auren, Kai kuma...ya maida zancen Kan turaki.... Kazo min da Abbas din Nanda sati biyu. " haka suka cigaba da tattauna batutuwa masu muhimmanci daga bisani suka ci abinci sannan taro ya watse.People are criticizing akan Ahmad da raudha, in normal life ana samun mace tafi namiji zurfafawa a soyayya, tayi ta shan wahala ta kasa fahimta. So same applied to raudha, keep calm am adding sauce to everything...... Lobbbyuuu lodilodi
Hope Kuna sani a prayers dinku? Am very much grateful for all you did, you doing and what you will do.
©️Shatuuu♥️
YOU ARE READING
...ME RABO KA DAUKA
General FictionKowacce mace a duniya allura ce a cikin ruwa ME RABO KA DAUKA. Kaddara kansa mu hadu da mutane da yawa, wasu mu cutar dasu, wasu su cutar damu, wasu su bar Sautin muryoyinsu cikin kunnuwanmu, wasu Takun tafiyarsu cikin zuciyoyinmu, wasu su koya mana...