27

2.1K 210 0
                                    

👑 👑 👑 👑 👑

💖 💖 💖 💖 💖 💖

💍 💍 💍 💍 💍 💍

...ME RABO KA DAUKA 27

Shatuuu095@wattpad

✍️AMMIN SU'AD

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

*This page is dedicated to Amina Mustapha, Fatima Zarewa, yaya Nana, Annah love, Abida, Hijja, ummu naeeym, eysher m umar and A'isha major.*

*Abuja, Nigeria*

Kwana biyar kenan da dawowar meeyna daga UK, hankalin hajiya Hauwa gaba daya a tashe yake saboda yadda meeyna ta rame tayi baki kamar wadda take cikin wahala, kana ganinta kasan Tana cikin damuwa gashi Alhaji mu'azu baya kasar ya tafi official assignment Ukraine.  Tayi tayi meeyna ta fada mata Abinda yake damunta amma taki, abinci da kyar take tursasa ta take ci, shima se tayi mata wuka wuka sannan take fitowa, Sede ta kulle dakinta ta Sha kuka kamar  wadda Don haka tazo duniya.

Meeyna na kwance kan cushion a dakinta wanda ya hadu sosae kamar na wata Matar aure, half gown ce a jikinta babu dankwali tayi rub da ciki da alama tunanin wani abu take. Hajiya har ta bude kofa Amma meeyna Bata sani ba, Seda ta kalleta na kusan Mintina uku kafin ta shigo ta xauna gefenta ta dago ta, a tsorace ta kalleta Amma ganin mummy yasa ta danji dadi se kuma ta maida kanta kasa tana wasa da yatsunta,

"dago ki kalleni Amina "

A hankali ta dago ta sauke kallonta kan mahaifiyarta kafin ta maida kanta kasa

"me yake damunki? Me kike so? Waye ya tabaki "

Bude bakinta tayi a hankali tace

"mummy babu.... "

"kar kiyi min karya, na gaji da jin babu komai Daga bakinki, Bayan idonki na fada min karya kike. Kin ganki kuwa, kinga yadda kika koma me ya sameki ki fada min ko Kinada wanda ya fini kaf duniyar nan?"

Take meeyna taji zuciyarta ta karye kawai se ta fashe da kuka tare da rungume mahaifiyarta, itama mummy rungumeta tayi tana shafa bayanta a ranta tana fadin dukda meeyna ta kasance bata da hayaniya ko kadan amma suna hira Tunda ta kasance uwa kuma kawa a gurin meeynan Tunda Bata Faye shiga mutane ba balle tayi kawa, ko cousins enta idan suka zo da an gaisa zata koma daki. To amma ta kasa fahimtar wanda yake neman ruguzawa tilon diyarsu rayuwa.

Sun kusa Mintina goma a haka kafin kukan meeynan ya tsaya hakan yasa su sakin junansu, mummy ta janyo tissue ta goge mata fuskarta sannan tace

"ko saboda Ismail ya gama karantunsa Shiyasa kika damu? "

Da sauri meeyna ta girgixa kanta Don yadda taji ranta ya baci jin sunanshi tace

"Haba mummy, naga ko wancan karan da ya gama masters dinsa ba tafiya yayi ba, banyi tunanin zai sake dawowa ba kuma ya dawo, mummy babu komai Wallahi kawai grades dina ne suka danyi falling" tayi mata karya Don ta kwantar mata da hankali.

"come on, shi ne kika damu kika tayar min da hankali. To Karki damu kinji ko babu wani abu dama rayuwa is dynamic, canzawa take, yanzu canza kaya muje gidan hajiya Nana "

Murmushin nasara meeyna tayi ganin da gaske mahaifiyarta ta yarda Miqewa tayi ta dakko lace red me kwalliyan green da gold. Dinkin half gown ne da plain zani da yake babu laifi ta iya daura zani ba kamar yan matan yanzu ba.... Irinsu Zarewa and Co..... Daura dankwalin tayi ta dakko matching veil, dankunne, jaka da takalmi tayi kyau sosae ta kuma gyara fuskarta, Duk tana yi tana tunanin Ismail, kamar ta cire zuciyarta ta yasar haka take ji saboda har yanxu tana jin son Wanda ya wulakanta ta, wani barin na zuciyarta kuwa babu Abinda ya tsana Irin Ismail, tabbas da Tana da delete button da se ta goge shi cikin Rayuwarta Baki daya amma babu komai se yanzu ta gane everything is not at her disposal ,  ba komai Kake nema Kake samu ba, Ismail ya nuna mata rayuwa is all about struggles, this struggles makes you strong, ta sani zuciyarta is broken into thousand pieces amma da kanta Taga kukan datakeyi will never help hakan yasa ta hada wannan broken pieces din ta manne saboda tana son moving on, namiji bashi kadai ne damuwar ya mace ba kamar yadda suke tunani

"Ama... Ama.. Ama " muryar mummy ta daki dodon kunnenta, hakan yasa tayi saurin goge hawayen fuskarta sannan ta goga foam din powder kafin ta fice cikin nitsuwa.

*ZAZZAU, NIGERIA*

Daren da raudha ta bar Nigeria a Wannan Daren Ahmad ya iso Nigeria, Misalin karfe daya na dare hakan yasa ya Kwana a hotel a cikin Abuja, Washegari karfe Tara ya samu taxi drop har Zaria Don Yana son surprising dinsu ne, dukda sunsan zai dawo amma bai fada musu flight time dinba, duba wayarshi yayi Se lokacin yaga message icon a saman notification bar dinshi da sauri ya bude, Dan siririn tsaki yaja ganin sunan raudha baro-baro shi se yanzu ya tuna da ita ma, ranar yaga kiranta har sau uku amma bai picking ba dukda yaso yin hakan saboda wani side na zuciyarshi na fada masa baya kyautawa, Yana wulakanta Abinda Ke sonshi donshi takamaimai ya Kasa fahimtar son raudha yake ko akasin haka? Shide yasan tana birgeshi amma bazai iya aurenta ba saboda mahaifiyarsa bata sonta, kuma bazai iya yaki da hakan ba, shi se yanzu ya gane Tun farko ma kyanta ne ya rude shi har ya ce Yana sonta tabbas da delete button he will definitely delete her and her memories in his life Don kua ta bashi memories sosae masu dadi shi kanshi yasan tana sonshi don haka yake jin tausayinta Yana ganin kamar he caused everything amma itama ai ta zake, he was creating space Shiyasa yake sati biyu Zua uku bai kira ba amma taki tafiya to yanxu yana Zua Zaria zai sanar da ita kodan zata gani da idonta ma. Duba message din yayi kamar haka

*Habibi am flying out of the country to Germany, Istanbul, Dubai and then d holy land. Inshaaa Allah I'll catch up with you kafin ka tafi zan dawo. Sannan na kiraka jiya da yau duk you didn't pick? May be baka kusa kuma ka Kira tawa bata shiga ba, don't bother yourself banyi fushi ba and always tell yourself that raudha loves you so much and will one day be yours*

Duk iskancin Ahmad Seda yaji tausayinta ya kamashi, deleting yayi Don baisan Abinda yake ji ya rinjaye shi. Haka tafiyarshi ta kasance har ya iso Zaria.

Farinciki, murna babu Wanda mutanen Masarautar nan basui ba Na dawowar Ahmad, shekara biyu ai ba wasa bace kada ma hajja da nawwara suji labari.

Yau ranar ta kasance laraba, an tashi da Ruwan sama me karfi wanda be tsaya ba se axahar, garin yayi dadi ga iska me sanyaya zuciya. Daga daki Ahmad ya fito Sanye cikin trouser cream da polo shirt off white yayi kyau sosae, wayarsa na kunnenshi da dukkan alamu waya yake, daidai nan fitowar imran daga dakinshi shima kananan kaya ne jikinshi, kallon juna sukai kafin imran ya karaso gurin yace

"yaya Ahmad ina Zuwa haka, kamar Wanda zaka ga raudha? "

Se da gaban Ahmad ya fadi Amma ya dake ya dubi imran daya tsura mishi ido yace

"Raudha kuma? Meye hadi na da ita? Don't be a silly man" ya fada yana bugar kafadarsa tare da wucewa

Da sauri imran ya sha gabansa yace

"No yaya don't do this, kasan wa nake nufi "

Dammm ya sake jin faduwar gaba me imran ke shirin Yi haka karfa ya Bata masa aiki

"wacece wai raudha? Plz ka kyaleni nawwara na jirana kuma idan ita tace ta sanni karya take"

Bai jira me imran zai ce ba ya fice da sauri kamar zai fadi, haladu me kula dashi ya take masa baya.

Nasan u gat lot of questions, karku damu just comment I'll answer and clarify everything, just don't be silent readers OK?

©️shatuuu♥️

...ME RABO KA DAUKAWhere stories live. Discover now