👑 👑 👑 👑 👑
💖 💖 💖 💖 💖 💖
💍 💍 💍 💍 💍 💍
...ME RABO KA DAUKA 32
Shatuuu095@wattpad
✍️AMMIN SU'AD
🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
Ummusafiyya the page is yours, my fans ku cigaba da hakuri.
A Daren jiya lahadi kenan Ahmad ya dawo Daga Columbia cikin dare Misalin karfe daya na dare, a Lagos ya Kwana kafin yau litinin da safe ya biyo jirgi zuwa kaduna daga nan ya dauki taxi Zuwa Zaria. Misalin karfe biyu na rana ya iso cikin gidan nasu. Raudha bata nan tana makaranta ba ita ta dawo ba se bayan maghrib, Tana shigowa tayi wanka taci abinci ta kwanta da yake tana off salat.
Washegari, lectures dinta karfe goma ne Don haka se karfe bakwai ta tashi wanka tayi nan zubaida ta kawo mata breakfast, toast bread ne, tea da chips. Kadan taci tace ta koshi saboda yadda take jin gabanta nata faduwa.
Karfe Tara ta fito Don tafiya makaranta, tayi kyau cikin bakin lace da orange Flowers dinkin skirt da Riga, hijabi ta saka orange da sauran accessories. Dakinta ta janyo ta fito cikin takun nan nata na manyan mata, ta kusa zuwa inda zata nufi zauren farko taji wani na fadin
"yarima Ahmad Ashe ansa rana kaida nawwara? " diiimmmm taji kunnenta, addu'a take Allah yasa yace ba haka bane, to wai da gaske Ahmad din....
"Eh Wallahi an saka 5months" taji muryar da ko a mafarki bata tunanin zata bace mata ta katse mata tunaninta
"Allah ya sanya alkhairi yasa ayi a sa'a "
Samun kanta tayi da kasa Daga ko da daya daga cikin kafarta, jitayi Ahmad yace
"nagode sosae " sannan ya juyo ya Don komawa cikin gida, ba karamin tsorata yayi ba ganin raudha a tsaye, kana kallonta kasan taji komai saboda gaba daya jikinta rawa yake ga idonta sunyi ja sun firfito waje Mashaaa Allah, samin kansa yayi da rashin jin dadin hakan, ba a haka yaso taji ba amma komai normal ai.
Raudha kam ko kifta idonta Batayi ba kallonshi kawai take me Cikeda meanings kalakala, take kuma ta juya Don komawa ciki, da karfi ta hankada kofar ta shige ciki, babban trolley dinta ta janyo ta bude wardrobe dinta tana zubo Duk Abinda hannunta yakai, Kai kanka inka kalleta kasan bata hayyyacinta. Seda ta cika shi dam sannan ta rufe shi ta janyo babbar handbag dinta ta zuba duka abinda tasan zata bukata Kwana kusa, ita kanta Bata san yanayin da take ciki ba, tana gamawa ta ciro jakar da take aje kudi ta kwashesu duka sannan ta janyo trolley dinta ta nufi kofa, duk wanda ya mata magana ko kallonshi Batayi saboda ita kadai tasan yadda zuciyarta keyi, ta baya ta fita anan wani dogari dayake ya Santa ya taya ta daukar kayan Zuwa titi, napep ta Tare tace Ya kaita Tasha, babu bata Lokaci ya kaita, dubu ta bashi ba tareda ta jira canji ba ta nufi inda wani dan union ke tsaye,
"drop nake so Zuwa daura "
Kallonta yayi yace
"yanmata da tsada fa"
A fusace tace
"nasani ai "
Baice da ita komai ba ya samo mota akai ciniki sannan aka saka mata kayanta, ta shiga ta janyo wayarta tare da kashesu duka Don kar ma wani ya neme ta. Gaba daya kwakwalwar ta ta toshe tunani take sonyi amma ta kasa, to Yaushe Ahmad ya dawo? Bai neme taba? Kenan duk zancen imran gaskiya ne? Bata san ta saki wani matsanancin kuka ba Seda driver ya juyo Yana fadin
"hajiya Kiyi hkri, haka duniya take Sede hakuri"
Ko kallonshi raudha Batayi ba donji take kamar ta shake shi, Duk basu suka sata cikin wannan halin ba, memakon ta daina kukan se ma Kara fashewa da tayi da wani sabon, haka ta dinga kuka har suka shigo cikin Kano, driver tun yana Bata hakuri har ya kyaleta.
Basu suka isa daura ba se bayan laasar lis, lokacin idanun raudha sunyi ja, so swollen, kanta wani Irin Ciwo yake mata, amma Har lokancin hawaye bai daena zuba ba, ita kadai tasan yadda zuciyarta Ke tafasa, wai da gaske Ahmad did this? Inba Don taji da kunnenta ba she will never believe this, Itace Rayuwarta Taxo a haka? Ita namiji yayi wa haka? Ya yaudareta me tayi masa? What..... Hell she can't believe this ita raudha upon all people, take wani kukan ya sake kwace mata lallai namiji ba abin yarda bane.
Ta baya ya sauke ta sannan ya fito mata da kayanta, yana sake Bata hakuri, batace mishi komae ba saboda yadda hawaye Ke mata zirya kan kumatunta, tabbas da hawaye Yana karewa definitely da Nata yau Ya kare, dogarai biyu suka taho gunta Don sun ganeta, suna ta gaisheta amma babu Wanda ta kula cikinsu se hijabinta DA taja ta rufe fin Rabin fuskarta, Handbag kadai ta dauka ta bar musu sauran kayan, shiga dashi sukai yayinda take jin wani jiri na dibarta, a hankali take tafiya tana ganin dishidishi har ta iso bangaren Mami inda ta samu mamin a tsaye da alama jiranta take Tunda gashi kayanta sun rugata isowa, Tana hada ido da Mami ta fashe da wani sabon kukan tare da fadawa jikin mamin, rungumeta tayi saboda ta tsorata, raudha is strong abinda zai sata yin haka babban abune. Janta tayi har inda take Zaune sannan tasa a kawo mata rua kafin ta sallami duka kuyanginta, raudha takai minti goma tana kuka ba tareda Mami tace da ita komai ba, sannan a hankali tayi shiru se ajiyar zuciya da take saki me karfin gaske kuma akai akai, ruwa Mami ta mika mata kadan Tasha sanann ta aje, sunkuyar da kanta tayi yayinda Mami wadda kana kallon fuskarta zaka ga zallar tashin hnkli ciki tace
"tashi ki shiga ciki Kiyi wanka kukan ya isa haka"
Bata musa ba Don batason kowa ya tambayeta dalilin tahowarta da kukan datakeyi saboda bata tunanin zata fadawa kowa. Tana shiga ta fada bayi tayi wanka kafin ta fito Mami tasa hanne ta kawo mata abinci, ko kallonshi Batayi ba, ta zura kaya ta hau gado hawaye na sake bin kuncinta
Kenan duk ixaya da azabar hajja da ta shanye ta jure Ashe wanda take dominshi baya gani, duk ya rasa da Abinda zai saka mata se Wannan, ita wa ta taba yaudara Balle ace Allah ya saka mishi, ko yaya sunusi bata yaudara ba cuz yasan bata sonshi, Don haka sati biyu da suka wuce ya kirata ya shaida mata ya samu mata aure zaiyi, ai kuwa tayi masa mirna suka rabu lapiya. Amma Ahmad ya cuceta bazata taba mantawa dashi ba, Kai ita ta yafe mishi Don ko a lahira batajin tana son ganinshi Balle ayi musu hisabi. Haka ta dinga tunani har sallar maghrib inda Mami ta turo hanne kan taga a wanne Hali fulanin take kuma ta tabbatar tasa ta taci abinci saboda ita baki take tayi, hanne na shigowa taga uwar dakinnata na kuka hakan yasa taji gaba daya hankalinta ya tashi, kusa da ita ta tsugunna tace
"ranki ya dade me ya faru"
Bata ce da ita komai ba ta nuna mata hanyar waje alamun ta fice, ganin taki yasa raudha ta Mike Don barwa hannen dakin, hakan yasa hanne ficewa da hanzari Don fadawa Mami, ko Mintina uku baayi ba Sega Mami da mama lami sun shigo, Mami ta zauna gefenta tana fadin
"raudha Menene? Wani abinne ya sameki a Zaria? Menene ki fadamin "
Raudha kam se kuka Wanda yasa Mami yin shiru gaba daya hnakalinta a tashe yake, Duk hasashenta ta kasa hasaso me akayiwa autar tata.
©️Shatuuu♥️
YOU ARE READING
...ME RABO KA DAUKA
General FictionKowacce mace a duniya allura ce a cikin ruwa ME RABO KA DAUKA. Kaddara kansa mu hadu da mutane da yawa, wasu mu cutar dasu, wasu su cutar damu, wasu su bar Sautin muryoyinsu cikin kunnuwanmu, wasu Takun tafiyarsu cikin zuciyoyinmu, wasu su koya mana...