👑 👑 👑 👑 👑 👑
💖 💖 💖 💖 💖 💖 💖
💍 💍 💍 💍 💍 💍
...ME RABO KA DAUKA 06
Shatuuu095@wattpad
AMMIN SU'AD
Sarki Hashim shi ne sarkin zazzau mutum ne adali wanda mutanenshi suke jin dadin shugabancinsa, yana da mata uku ta farko hajiya Asiya(mama) me ya'ya goma Maza da mata, hajiya barira (hajja ) me ya'ya hudu Ahmad ne danta na farko se Amarya hajiya luba(mummy). Karfe Sha biyu na Ranar asabar raudha, kulthum, yaya AJ suka iso garin zazzau. Already ansan da zuwansu Dan haka dogarawa suna jiransu , iso akai musu har ciki saboda me martaba ya sanar da hajja a gurinta raudha zata zauna, kuyanginta suka tarbo su har cikin inda hajja ke hutawa, kana kallonta kaga Ahmad kamar an tsaga kara kamarsu har ta baci , cikin wani danyen shadda ce Tasha aiki tana kishingide tana kallon kunyangarta dake faman bata labari na nishadi. Shigowar su raudha ta sata sallamarta sannan ta Fara binsu da kallo, cikin girmamawa suka gaesheta ta amsa ba yabo ba fallasa, cikin isa tace "wacece yar makarantar? " a hankali raudha ta dago tace "ni ce" hajja batace komai ba se kallonta da take, ana haka aka shigo musu da abinci, lemuka da Fruit. Miqewa tayi tace "Kuci abinci Gashinan " Daga haka ta shige ciki. Tabbbbb ana wata ga wata. Ko baa fada ba jikinsu duka yayi sanyi musamman raudha, kulthum ce tayi karfin halin fadin "yaya AJ mu tafi ko, Ke kuma Kiyi hkri " kai AJ ya girgixa yace "mu danci ko yane karsu ji babu dadi"haka suka tsakuri abincin sunayi suna ma raudha nasiha. Suna gamawa suka sanar wa kunyangarta waya akan xasu tafi, Bayan Mintina kusan goma Sega ta ta dawo tace musu "Tace Allah ya kiyaye " sosae abin ya basu mamaki amma sai suka miqe ko mai martaba basu gani ba dondama sunsan baya gari. Tana biye dasu har suka karaso gaban mota driver har ya fiddo mata kayanta, wasu trolleys ne set hudu, carton din lemu, biscuits, wafers, sweet, chocolate da kayan tea. Hakuri suka sake bata sannan suka tafi. Wannnan shi ne Karo na farko da zatayi rayuwa ba a gidansu ba, Tunda take hutunta baya wuce sati daya ta dawo gaban Mami Shiyasa Duk cikin yayan Mami tafi sabawa da ita, Don ita a secondary school enta ma day tayi. Wasu dogarawa ne suka kwaso mata kayanta har ciki Sede batasan ina zata saka kayan ba. Haka ta koma inda ta tashi ta xauna ta zabga tagumi, babu kowa gurin se wasu tsirarin kuyangi dake shawagi. Tana nan Zaune har aka Idar da sallar axahar hajja bata fito ba kuma babu Wanda ya mata magana, sa'a daya ma tana period bata sallah da bata san yadda zatayi ba. Wayarta ta jawo ta turawa ya AJ text akan shida ya kulthum Kada Su fadawa kowa kada hankalin Mami ya tashi. Bayan wasu Mintina kulthum ta mata text akan babu damuwa tayi hakuri kawai.
Wasawasa har aka Idar da laasar hajja bata zo ba gashi wani mahaukacin fitsari raudha keji wanda ya hanata sakat, Miqewa tayi ta dubi wata Yarinya dake Sanye cikin kayan kuyangi , fitowa tayi a kusan a gigice Tace "baiwar Allah, inane Bandaki Dan Allah " kallonta tayi ta tabbatar wata babba ce Koda ganin kayan dake jikinta, wani Bandaki ta nuna mata raudha ta nufi gurin kafin ta shiga yarinyar tace mata "bayanki ya baci da jini" dimmm raudha taji, Bata jiyo ba kawai ta kada Kai , wani Irin bakin ciki ne ya tokare mata makoshi Tunda Mami ta haifeta Bata taba shiga kuncin da take ciki ba, fitowa tayi ta dauki wasu kayan ta canzo Don tayi sa'a toilet din na da kyau. Tana fitowa yarinyar tace ta kawo kayan ta wanke mata, haka ta Bata ta koma cikin parlour ta xauna. Karfe biyar da minti arbain hajja ta fito ta sake shiri cikin atamfa, tuni raudha ta gyara zama tare da fadin "barka da fitowa" ko kallonta Batayi ba se baiwarta data kira, Tana zuwa ta gyrfana gabanta tana faman gaisuwa hannu ta Daga mata alamun ya isa kafin tace "Kai ta dakin da kuka gyara jiya, daga nan ki Turon mashida "
"an gama ranki ya dade " itama raudha godiya ta mata sannan ta bita Zuwa inda aka ce ta kaita, daki ne ba babba ba can, karamin silver bed ne da katifa akai, dressing mirror se carpet a shimfide a kasan dakin. Daga gefe kofa ce Dana tabbatar toilet ne. Babu laifi dakin yayi. Suna aje mata kayanta suka gaesheta sannan suka fice. Bin dakin tayi da kallo ko ina very neat to her liking. bedsheet ta Fara shimfidawa saman gadon sannan ta ciro wani folded wardrobe ta harhada ta kafeshi daga gefe kayanta ta Fara jerawa har kusan shida sannan ta gama. Cosmetics dinta ta jera sanann ta ciro folded rack da shelf, rack din ta ciro kayan ciyeciyenta ta jera. Shelf din ta jera books dinta da takalma kafin ta hade akwatinan da sauran kayan ta tura kasan gado. Dakin yayi kyau tana kammallawa ta fada bayi ta feso wanka sannan ta canja kaya. Tana cikin fesa turare taji ana knocking, ixinin shigowa ta bayar, wannan same Yarinya ce da ta karba kayanta ta wanke mata yarinyar bazata wuce shekaru Sha biyar ba. Tsugunnawa tayi tana fadin "ranki ya dade barka da wannan lokacin, Sunana mashida ni hajja tasa inayi miki hidima " har ranta taji dadi ce mata tayi ta tashi sannan ta mata maraba tare da gabatar mata da kanta a matsayin Bakuwa wadda tazo karatu.Karfe takwas saura ta shigo parlour saboda mahaukaciyar yunwar da take ji, cikinta har murdawa yake Tun dazu take jira taji ance Ta fita cin abinci shiru. Hajja ce kishingide se yanmata guda biyu da bazasu wuce saoin raudha ba , hira suke suna ta dariya gabansu abinci ne kalakala wani ma ko taba shi baayi ba. Sallama tayi musu babu Wanda ya amsa se kallonta da suke faman Yi , zama tayi ta gaida hajja a maimakon ta amsa se cewa tayi "me ya faru? " Kai ta girgixa tace cikin sassanyan muryarta "babu komai" yamutsa fuska tayi tace "se da safe" Kai ta kada jikinta a tsananin sanyaye ta miqe ta nufi kofar fita, Tana jin lokacinda yan matan ke fadin hajja ina kika samu wannan kuma? Bataji me hajja tace ba saboda yadda take ji kamar tunkudata ake. Tana shiga daki ta fada kan gado ta saki wani kuka, Bata taba jin bacin rai Irin na Wannan ranar ba, kuka take babu kakautawa ga babu me rarrashinta Allah sarki maminta da mama laminta, ana haka Ahmad ya fara kiranta, Tana tsananin son jin muryarshi Amma bazata iya dauka ba dan definitely se ya gane da matsala kuma batasan me zata ce masa ne damuwarta ba. Seda Ahmad ya kira sau shida amma raudha taki picking, hakan ba karamin tayar masa da hankali yayi ba Don jikinshi na bashi yau tayi tozali da mummunan halin mahaifiyarsa na kin son wani ya rabesu idan ba yayanta ba, Shiyasa itama Hidaya da Nawwara Irin wannan halin garesu.
A hankali taji an turo kofar dayake ta kashe hasken dakin se wanda ke shigowa daga waje ta cikin windows din, sallama wata murya ta mata sannan tasa hannu ta kunna bulb din, a take haske ya gauraye ko ina kofar ta rufe DA key sannan ta xauna gefen gado ta kamo hannun raudha wadda batasan wani ya shigo ba tsabar kukan da takeyi ga tsananin bacin rai ga yunwa. Dago jajayen idonta tayi jin a riqe hannunta ta sauqesu kan budurwar dake zaune wadda shekarunsu zasu zo daya, dauke kanta tayi ta sake fashewa da wani kukan, ji tayi kawai yarinyar ta janyo ta jikinta tana bubbuga bayanta alamun rarrashi, haka tayi tayi har raudha tayi shiru, toilet ta shiga ta wanke fuskarta sannan ta dawo ta xauna batace komai ba se kasa da tayi da kanta.
To fa, me kuke gani? Xa'ayi abin kirki da hajja kuwa. Let's continue going muga yadda wannan zaman zai kaya
©️ shatuuu ♥️
CZYTASZ
...ME RABO KA DAUKA
General FictionKowacce mace a duniya allura ce a cikin ruwa ME RABO KA DAUKA. Kaddara kansa mu hadu da mutane da yawa, wasu mu cutar dasu, wasu su cutar damu, wasu su bar Sautin muryoyinsu cikin kunnuwanmu, wasu Takun tafiyarsu cikin zuciyoyinmu, wasu su koya mana...