04

3K 296 3
                                    

👑 👑 👑 👑 👑 👑 👑 👑

      💖 💖 💖 💖 💖 💖 💖

           💍 💍 💍 💍 💍 💍

...ME RABO KA DAUKA 04

Shatuuu095@wattpad

✍️AMMIN SU'AD

Katon tangamemen parlour ne, Wanda yasha ado da wani lallusan carpet lemon green, bangare biyu ya kasu kana shiga wasu dankara dankaran royal seat ne yan kasar turkey kalar green da fari, se tsakiyarsu glass center table ne me kyau da land-line akai, jikin bangon wata katuwar led plasma ce da sauran kayan kallo duka bakake, Daga Kwana kuma akai wani shelve wanda ke dankare da quranai, hisnul Muslim, riyaddus salihin, DA littafin addini masu dama, ta kasa kuma glass ne Wanda iya ganinka files ne a gurin.

Dayan bangaren parlour Tim Tim ne Manya a gurin, se dan table me dauke da fruits iri iri a cikin farin glass dish. Daga gefe kuma qurani ne da wasu takaddu wanda da alama ba gurinsu bane amfani akai dasu baa dauke ba.  Sarki Suleiman Na kishingide jikin Tim Tim da farar jallabiya me gajeren hannu yana hutawa, kwarjini, kamala DA cikar zati sun tabbata akan wannan bawan Allah, dukda shekarunsa sun tasamma sittin da doriya Amma har yanxu n ba, fita tayi sannan tayi musu iso, Amin na Sanye da bakar abaya ita kuma raudha na cikin atamfa, sallama sukai masa ya amsa Yana tashi Daga kishingidin tare da sakin Fuskarshi, a tare suka gaesheshi ya amsa Yana tsokanar su, dariya sukayi sannan yasa raudha ta zuba musu fruit susha, Bayan sun gama sha su ukun jakadiya ta turo a gyara gurin sannan ta fice ta basu guri.

"Nanda sati biyu zaki tafi Abuja ko? " me martaba ya tambayi Amin "Eh abbu" Kai ya Kada Ya sake fadin "gidan abdulhakim zaki zauna" take fuskar Amin ta fitar da wani kayataccen murmushi, normally 'yayan sarki Suleiman manyan kowanne yana da wanda duk matsalolinsu akansa yake, na Amin shi ne Turaki (Abdulhakim ). Godiya tayi masa sannan ya maida kansa kan auta wadda Ke wasa da zoben gold din hannunta, "Fulani "

"naam " ta dago ta dubeshi, kafin ta sauke kanta kasa, ruwa ya kurba cikin wani transparent glass cup kafin yace "two weeks back Naje emirates council meeting a Abuja, mun hadu da sarkin zazzau nake fada mishi you will be coming to Zaria saboda karatunki.. "tsayawa yayi ya sake kurbar ruwa kafin yace "ya rokeni akan kije gidanshi ki zauna, I can't say no to na amince weekends dinnan zakije Kano ki gama duk siyayyar da shirin daya dace. " Tunda ya ambaci gidan sarkin zazzau taji gabanta na faduwa, ta tsani zama gidan wani Balle gidansu Ahmad, what if they treat her badly.... Amin ce ta zungureta hakan ya dawo da ita daga tunanin da take "nagode abbu Allah Kara girma "

Nasiha sosae yayi musu kan rayuwar university sanann ya sake emphasizing kan dokarsa ta karatu, idan suna son aure to yayi musu amma idan sukai joining makaranta to sai sun gama. hira ya cigaba da jansu dashi ganin autarsa tayi shiru yasan yau akwai daru kawai dai bazata iya fada bane, sallamarsu yayi suka nufi cikin gida. Tunda suka fito babu Wanda yayi magana cikinsu , daedae inda zaka shiga gurin Mami, raudha tayi mata sallama sannan ta sallami hanne.

Mami na Zaune Kan carpet din daya lullube tiles din gurin, idonta na kan plasma dake faman aiki, daga gefenta Shayi ne take kurba. Sallamar raudha taji a ciki ciki hakan ya tabbatar me martaba ya sanar da ita plan dinsa, sallamar bayin dake gurin tayi sannan ta maida dubanta Kan raudha dake kuka

"Menene abin kukan? " Bata ce komai ba sai shashaeka datake, Bata san zama gidan wani Koda yayanta ne, Amma me martaba zaice ta xauna gidan sarkin zazzau, to yanxu idan mutanen gidan basuyi treating dinta da kyau ba kuma ta tsanesu kosu tsaneta kenan hakan yana nuna matsala a relationship dinsu da Ahmad kenan? Mami ce ta katse ta da fadin

"kukan da kike fulani bashida amfani, tsoron me kike?  nasan na miki tarbiyyar da duk inda kika je ba zaki samu matsala ba. Masarauta zakije ba Irin taku ba, kada ki nuna musu ke ma yar sarauta ce na fada muku alfahari, ji da Kai, dagawa duk attributes din Allah ne, Wanda ya kwikwaya yasan me yayi" shiru tayi ta kurba tea din sannan ta cigaba da fadin"ki zauna da kowa lapiya, kada ki saki jiki da kowa, gidan sarauta Nada hatsari..... " Mami tafi awa tana mata nasiha da lallashi kafin Daga karshe tace ta shiga ciki ta kwanta. Tana kwanciya bacci ya dauketa ko Ahmad Bata saurara ba.

Washegari, raudha na Zaune gefen mama lami tana karyawa dayake kusan yawancin lokuta acan take karyawa Sede idan da Mami ko me martaba zasuci. Kwanukan ta rufe ta Kalli gefen da hanne ke Zaune, ko Batayi magana ba hanne ta gane Abinda take nufi, Kwanukan ta tattara sannan ta basu guri, mama lami ta gyara zama tace

"fulani, munyi magana da Mami tace min gidan sarkin zazzau zaki zauna amma bakya so, ranki ya dade Meye dalilinki? " shiru ne ya ratsa dakin kafin raudha ta bude Baki Tace

"mama ranar bikinsu yaya Aziza Nayi saurayi Dan sarkin zazzau. Mama ina sonshi sosae amma Bana son mu samu matsala da yan gidansu Dan zai taba alakar mu dashi. Wannan shine dalilina mama" Cikeda gamsuwa mama ta jinjina kai kafin tace "tunaninki me kyau ne Amma Bana ganin wata matsala xataxo, Sede Kinsan Ke allura ce cikin ruwa ME RABO KA DAUKA Bana son ki xurfafa son da yawa saboda nan gaba zaki cutu" me kalaman mama Ke nufi? same thing da Mami ta fada mata jiya da daddare kenan akan Duk Wanda zata so Kada Ta Bari zuciyarta tayi zurfi saboda she will be hurt later , kallon mama tayi fuskarta na nuna alamun neman Karin bayani, murmushi mama lami tayi Tace "Kada ki zargi komai fulani shawara ce na Baki, duk inda kikaje Kada ki manta tarbiyar Mami a gareki "

Bayan Kwana biyu, Amin ta tafi Registration Abuja, raudha kuma ta tafi Kano shirin makaranta ta sauka gidan yaya Abdulhamid, Kwana hudu ta gama shirinta tsaf Se daura, da daddare tana taya Anty Laila amaryar yaya Abdulhamid gyaran wardrobe, se gashi ya turo sultan ya kirata, Miqewa tayi ta daura dankwalinta sannan ta nufi parlonsa, Yana zaune kan sofa Daga gefensa uwargidanshi ce Anty farida tana faman shashan kamshi, Matar batada kirki Shiyasa DA baa zuwa gidanshi saida ya kara aure, itama raudha bata kalleta ba, ta nemi gefen kafar shi ta xauna Tana fadin

"yaya barka da dare, gani"

"barka dai fulani, me martaba ne ya kira yanason magana dake" Cikeda Doki ta Fara washe Baki wanda ya sake kular da Anty farida Miqewa tayi ta fice a parlour, binta yaya yayi Da ido kafin ya girgixa Kai sannan ya miqawa fulani wayar, har lokancin murmushi take itakam tana son babanta

"Assalamu alaikum, barka da warhaka abbu"

"barka dai fulanin abbu, Kinje Kano kin manta da babanki ko? " dariya tadan Yi Tace "Haba dai abbu na, ni wacece? "shima dariyar yayi Allah kadai yasan yadda yake son autar nan tasa

"Nacewa Abdulhamid ya kaiki gidan sarkin Kano kafin ki taho gobe ki gaida shi ai Kinsan alakar dake tsakaninmu ko? " Dan Jim tayi kafin tace "Eh abbu Allah ya kaimu, Allah ja da ranka"

Vote

Comment

Recommend

Share

Follow me

©️ shatuuu ♥️

...ME RABO KA DAUKAWhere stories live. Discover now