👑 👑 👑 👑 👑
💖 💖 💖 💖 💖
💍 💍 💍 💍 💍
...ME RABO KA DAUKA 44
✍️AMMIN SU'AD
shatuuu095@wattpad
KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
Cikin yardar ubangiji raudha suka Fara exams, kamar yadda Ismail yace mata kada tayi tunanin komai se na karatunta to haka take, sosae ta dage Don ganin tayi making papers dinta. Kullum yakan kirata sau daya yaji yadda take kuma ya exams, idan suka gama se Washegari kuma.
Tana kitchen ta gama dama quarker oats wajen Tara da Rabi na dare , haseey ta kwalla mata kira, da sauri ta shigo ciki tana mitar tasa ta kusa konewa, wayarta ta dauka dama saboda hakan haseey ke kiranta, meeyna ce zama tayi saman carpet ta dakko madara da sugar ta zuba sannan ta kira meeyna
"Amaryar Tafida"
"zaki sani Tunda na dawo kinki Zuwa ko?"
"ke zanzo wata magana nake so muyi dake"
"Tohm ina jinki Allah yasa lapiya"
"kinga, ta yaya zan fara"
"Duk ta inda kike so"
"Kinsan na hudu da imran na bikinku ko? "
Cikin zakuwa raudha tace
" bani labari Kawata"
"munyi exchanging numbers, bayan nabar Kano Saturday, Monday Yaje yaga daddy"
Wani ihun murna ta saki wanda yasa haseey kallonta
"just go to the point am eager"
Dariya meeyna tayi tace
"daddy ya bashi ixinin Zuwa guna, muna waya sosae me kika gani"
Cikin jin dadi raudha tace
"meeyna, kinga na zauna dashi, bashida matsala amma ke ya kike gani? "
Shiru meeyna tayi kan tace
"inajin kamar Allah answered my prayers"
"Yawwa 'yar gari, open your heart ki bashi chance, idan shi mijinki ne definitely zan baki wannan maganar ta Kinyi sa'a Kinyi dace. Allah ya zaba muku mafi alkhairi"
"thank you so much darling "
Random talks sukai kafin ta kashe wayar, missed calls din Ismail guda biyu, Seda gabanta ya fadi ganin har goma da yan Mintina. A hankali tayi dialing digits din nasa, katsewa yayi ya kirata, cikin sanyin jiki ta dauka
"barka da dare"
"barkanki dai, ya karatu?"
"Alhamdulillah"
"se Yaushe zaku gama exams dinne? "
"Nanda 2weeks"
"Allah ya kaimu seda safe"
Kafin tace wani abu ya kashe wayar, haushin kanta taji yau Dan tsokanar da yake mata ma baiyi ba, aje wayar tayi se taji oats din ma ya fita a kanta, rufeshi tayi ta janyo handouts dinta ta fara karatu.
Akwai wani yanayi da kakeji idan kasan kayi wani abu ba daidai ba, Irin guilty tension bazai barka ba, ko kuma feeling din burinka bai cika ba, wannan halin Ahmad yake ciki, Yana kwance kan gadonsa Tunda yaga fuskar raudha a matsayin Matar Ismail picture yaki bacewa daga idonsa, Ashe shi raino yayi masa, bai taba tunanin raudha zata Yi aure haka Kwana kusa, se gashi ta rigashi yin Auren baki daya. That beautiful and nice raudha ta zama matar Ismail, shi yasan baya sonta amma ya rasa dalilin da yasa yake son jin tun Yaushe suke tare da Ismail dama itama amanar shi take ci? Kansa ya girgixa Yana fadin emphatic NO yasan har abada bazai taba samun mai sonshi kamar raudha ba. Jin muryar imran a parlour yasa ya fito ya xauna, Seda ya jira ya gama wayar kafin yace
BINABASA MO ANG
...ME RABO KA DAUKA
General FictionKowacce mace a duniya allura ce a cikin ruwa ME RABO KA DAUKA. Kaddara kansa mu hadu da mutane da yawa, wasu mu cutar dasu, wasu su cutar damu, wasu su bar Sautin muryoyinsu cikin kunnuwanmu, wasu Takun tafiyarsu cikin zuciyoyinmu, wasu su koya mana...