👑 👑 👑 👑 👑
💖 💖 💖 💖 💖
💍 💍 💍 💍 💍
...ME RABO KA DAUKA 49
✍️AMMIN SU'AD
shatuuu095@wattpad
KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
*I dedicate this page to every single soul, apart or in touch with me patiently following me on this journey, I love you so much and raudha da Ismail suna gaisheku*Lol*
Nawwara na shiga daki ta janyo mayafinta ta fito ko kallonta Ahmad bai Yi ba har ta fita sannan yabi bayanta, Kamar mahaukaciya haka take tafe tana kuka, har Seda ta dangana da parlourn hajja , Tana zaune Tana zuba iko, taji kukan nawwara cikin sauri ta sallami kuyanginta se imran kawai ya rage Wanda ko kallon arziki nawwara bata samu ba, shi dama yarinyar bata burgeshi Balle kuma yanxu ranar yana nan ta dinga yiwa Ahmad rashin mutunci a ranar Wallahi da matar shi ce se ya ballata kuma se ya sake ta amma Ahmad ya Jawa kansa at least da ya riqe raudha duk haka bazai faru ba.
"Kiyi shiru kinji, fada min me ya faru " hajja ta fada duk hankalinta a tashe, Amma nawwara se kuka da take dada fashewa dashi, shigowa Ahmad yayi fuskar nan tayi kicinkicin kamar an aiko masa da mutuwa, ko gaisuwarsa hajja bata ansa ba ta fara fadin
"me kayi mata Ahmad "
"ta fada miki ita me tayi"
Cikin kuka nawwara tace
"mari na yayi"
Baki bude hajja tace
"Ahmad mari? Wata uku da aure har ka fara duka me tayi maka?"
Cikin nitsuwa ya kwashe komai ya fada mata, hajja ta girgixa mussaman fadan yau, Anya nawwara zata iya hakan?
"nawwara me yasa? Tarbiyyar da nayi miki kenan, ina nasihar da nayi miki kafin a kaiki gidanki? Kin watsar"
A hankali nawwara ta dago idonta da sukai ja tace
"Wacce tarbiya kika min, Bayan muna Zaune kike fadin bazaki taba Bari namiji ya taka ki ba, muma kuma kar mu Bari ya taka min, ki musa mana saboda na auri danki Shiyasa zaki hanani it's way too long, kuma ki ja masa kunne daga Rana Irin ta yau ya sake marina ya mari aurensa"
Nasha mamakin ganin babu Wanda ya dakatar da ita har ta gama, sannan ta nufi kofa zata tafi se kuma ta jiyo tace
"and ku sani na gaji da zaman gidannan idan Ban tare ba Wallahi me martaba zan fadawa"
Wani Irin bakin ciki ne ya turnuke hajja, Tunda take babu mahalukin da ya taba Zuwa ya cinye mata mutunci a kwayar idonta Irin na nawwara, tabbas abinda ka shuka shi zaka girba gashi ta fara gani ko cikin mafarki bata taba tunanin Za'a samu me courage din mata haka ba, se gashi yarinyar da ta koyawa Taxo tana mata, Turkashi!
"ka fadawa matarka Duk ranar da ta sake Zuwa tayi Abinda tayi yau Wallahi se nayi mata dukan mutuwa, idan kai ta rainaka ni ba saan wasanta bane."
Imran ya fada cikin fushi, kawai taci albarkacin matar yayansa ce da me ceton ta se Allah , sannan yana son hajja ta raina kanta, taga illar Abinda ta shafe shekaru ta nayi, nawwara ba tayi karya ba yasha da kunnuwansa jin nasihar ta, idan yayi magana ta koreshi gashi Abinda ya haifar. Jin sunyi shiru yasa ya cigaba da fadin
"hajja na Sha fada miki abinda kike Dora yarannan ba daidai bane, gashi nan kin gani, kaima Kai gaba dayanku alhakin raudha bazai dena bibiyarku ba, Allah rufa asiri"
Duk jikinsu yayi sanyi, hajja da take jin kamar ta mutu ta Mike Don komawa dakinta se kawai ji sukai ta fadi, da sauri suka yo kanta, idonta a bude amma bata magana, se girgixa ta suke amma ina se ido kawai take juyawa. Imran ya kira doctor dinsu nan yace zai zo Yana kan hanya, kafin wani lkci har kowa yasan hajja ta fadi amma ba Wanda ya san dalili. Hatta me martaba ya sami labari turo jakadiya yayi akan tazo taji yadda abin yake, nan doctor ya karaso, ya Dan dudduba ta ya kalli imran yace
YOU ARE READING
...ME RABO KA DAUKA
General FictionKowacce mace a duniya allura ce a cikin ruwa ME RABO KA DAUKA. Kaddara kansa mu hadu da mutane da yawa, wasu mu cutar dasu, wasu su cutar damu, wasu su bar Sautin muryoyinsu cikin kunnuwanmu, wasu Takun tafiyarsu cikin zuciyoyinmu, wasu su koya mana...