25

2.1K 192 1
                                    

👑 👑 👑 👑 👑

💖 💖 💖 💖 💖 💖

💍 💍 💍 💍 💍 💍

...ME RABO KA DAUKA 25

Shatuuu095@wattpad

✍️AMMIN SU'AD

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

*Do you know how it feels to have someone who loves and cares at the same time? I feel happy, elated, blessed having you guys in my life. I received your message through my mail, inbox, group chat, wattpad and direct whatsapp message. I really appreciate you guys for d prayers and love you showered to this innocent shatuuu, no words can describe how u mean to me. This chapter and d Oda one issa token of appreciation from your only shatuwalle*

*A month leap*

"A gobe nake son na ganka a Nigeria idan ba haka ba Sena mugun saba maka" sarki Hashim Ke fadin haka Zaune cikin personal chamber shi, banji Abinda aka fada ba ta dayan bangaren se cewa yayi

"kaji dai na fada maka idan kuma ba haka ba kasan sauran "bai jira me zai ce ba ya kashe wayar tare da gyaran murya , a take sallaman sarki ya shigo tare da dukawa ya kwashi gaisuwa, kallonsa me martaba yayi yace

"waye yake jirana a waje"

Dukar da kanshi yayi yace

"Allah Kara wa sarki Kwana, ranka ya kara dadewa raudha ce take jiranka"

Kansa ya gyada yace

"shigo da ita"

Bayan Mintina uku raudha ta shigo cikin pink din shadda da farin hijabi, fuskarta kamar kullum tana Cikeda murmushi tayi kyau sede idanunta da suka fada wanka Ke da nasaba da exams din da take. Tsugunnawa tayi gabanshi tace

"barka da wannan lokacin baba"

"barka dae, kin fito kenan"

Sake sunkuyar da kanta tayi tace

"Eh "

"Yaushe zaku tafi zuwa Germany din? "

"jibi Inshaaa Allah "

"Allah ya kaimu ya kiyaye hanya"

"Amin baba, nagode Allah saka da alkhairi "

Murmushi yayi Irin nasu na Manya kafin ya daga newspaper din dake gabansa Yana ciro brown envelope ya mikawa raudha, a nutse tasa hannunta ta amsa tare da fadin

"nagode sosae Allah ya kara girma ya ja Kwana "

"kuje karkuyi dare"

Sallama ta sake masa sannan tayi hanyar waje, lumshe idonsa yayi haka kurum tarbiyarta Ke birgeshi inama daya daga cikin yayansa wani ya aure ta Don baya son ta bar gidan haka kurum.

Tana fita parlor hajja ta nufa inda ta sameta a Zaune, ita kadai ce babu kowa se tsirarin kuyangu. Kanta a kasa ta tsugunna ta gaesheta, kadaran kadahan haka ta amsa, Tana hararar ta kasakasa, ita kanta ta rasa dalilin tsanar yarinyar nan da tayi kawai ko ganinta tayi se gabanta ya fadi, ta rasa ganewa mussaman da Hashim yayi mata warning akanta.

Dagowa tayi ta dubi gabanta babu kowa hakan yasa tai saurin duban ikilima dake tsugunne gefe guda tace

"ina wannan kodaddiyar? "

Take ta gane wadda take nufi Don haka take kiranta, gyara tsugunno tayi tace

"Allah Kara miki lapiya, tana ta miki sallama baki amsa ba hakan yasa ta tafi"

Tsaki hajja tayi ta maida hankalinta Kan tunanin da take, kafin taji shigowar nawwara a guje Tana fadin

"hajja..... Hajja.... Hajja"

...ME RABO KA DAUKAWhere stories live. Discover now