👑 👑 👑 👑 👑
💖 💖 💖 💖 💖
💍 💍 💍 💍 💍
...ME RABO KA DAUKA 48
✍️AMMIN SU'AD
shatuuu095@wattpad
KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
Wata Irin shaquwa ce me tsanani tsakanin raudha da Ismail, soyayya suke hankali kwance babu wani hargowa dukda har zuwa wannan lokacin raudha Batayi confessing son da take ma Ismail ba amma tasan for sure tana sonshi Irin like she can't live idan babu shi ta yadda da wannan kuma tana ganin is high time tayi uncaging zuciyarta ta fadawa Ismail yadda take sonshi.
"dimple Munzo "
Da sauri ta dubeshi, kafin ta kalla school din confirm sunzo tana nan tana tunaninshi.
"OK" jakkarta ta dauka ta bude kofa bayan ta fita ta leko da kanta tace
"I love you honeycomb" kamar walkiya ta bace Daga gurin yayinda wani Irin farin ciki ya lullube Ismail, the long awaited day is here, finally she said it, yau kam yana jinsa complete, yana jin yakai esteem baya da wata damuwa. A hankali ya furta
"I love you too dimple" haka yaja motarshi Yana jin wani Irin nishadi da bai taba zaton zakayi katari dashi a gidan duniya ba, shikam he's blessed with such a kind soul.
Karfe hudu ya iso kofar lecture hall din Dan daukarta, kwatakwata yanxu zaman Kano baya masa dadi Shiyasa ya tattaro Zuwa Zaria Don idan Yana kusa da ita yana jin komai daidai yake cikin rayuwarsa, Allah yana sonshi da ya bashi wannan baiwar tashi, fitowa yayi daga cikin motar ya harde hannunsa yayi kan kirjinsa Yana bin school din da kallo, mutane se wucewa suke, wasu su Nata kallonshi. Wayarsa ya ciro Yana danne danne jikinsa ya bashi he's dimple is coming, kuwa dai Itace tsakiyar haseey da ruwaida se can gefen ridwan, suna hada ido ta sakar masa murmushi wanda yasa dimple din more prominent, lumshe idonsa yayi Yana jin kamar ya zuketa da idanunsa
Kafin su karaso wata matashiyar budurwa da nake da tabbacin level1 take duba da yadda taci kwalliya alamun Bata fara karbar wuta ba
"please let's click a picture kayi min kyau" yarinyar ta fada tana daga wayar daidai isowar su raudha wadda gaba daya mood dinta ya canza, kallonta Ismail yayi sannan ya kalle yarinyar dake kokarin shiga camera, dakatar da ita yayi ta hanyar fadin
"meet my wife, Seki tambayeta idan ta yarda you can click the photo"
Haseey dariya take sonyi ganin yadda yarinyar ta duburburce, within a minute ta bace, gaisawa sukayi sannan suka nufi hostel. Cikin motar Ismail yace
"ya lecture? "
Hannunta ta watsar cikin iska tace
"tiring"
Pity face yayi yace
"sorry, anything for your love? "
Se lokacin ta tuna yadda sukai da safe hakan yasa ta boye fuskarta a hijabi shima murmushi yayi ya maida kansa titi.
"Nidai daga yau ka Bari ina Zua school da kaina"
Harararta yayi yace
"inji dalili"
Kallonta ta mayar window tace
"'yan mata kallonka sukeyi" maganar ta fito so childish
Dariya ce ta kwace masa, Seda yayi me isarsa yace
"dimple ta iya kishi, see ni kuma bazan iya barinki da driver ba inde ina Zaria, me amfanina kenan?"
Shiru tayi kafin tace
"to ka dinga zama cikin mota har se na fito"
"better this, I promise "
Nawwara na Zaune gaban TV Tana kallo, Sanye da black skirt da white top se hula a kanta, fuskarta babu kwaliyya haka kuma babu alamar farin ciki, tayi kiba sosae Don iskanci take zubawa Ahmad yadda zuciyarta ta Raya mata, shikuma Kwana biu ya koyi bala'i babu hakuri duk Abinda tayi bazai dauke idonsa ba Don haka ya rame kamar ba sabon aure ba Kai ka rantse cuta yake.
Sati biyu da suka wuce ya shigo gida, Tana zaune da bum short da vest kanta babu dankwali, da sallama ya shigo amma bata ansa ba kanta na kan wayarta,
"armour Kinsan na hanaki zama da wanna kayan ko inde bana gida, Kinsan gidan jama'a ne kowa zai iya shigowa"
Kanta ta dago tace
"Daga dawowar ka ai ka Jira ka aje kayanka se kayi masifar" ta fada a harzuqe ta tsani Wannan halin nasa na masifa kamar wani damisa
"ni kike cewa masifaffe? Nawwara ni saanki ne?"
"na fada masifaffe, in banda masifa daga shigowanka ai ka Jira na baka izini mana, kuma Kaya da Kake zance ra'ayina ne banga wanda ya isa ya hanani ba, idan kaji haushi ka karasa gininka. Mts" tayi tsaki tana mikewa ta nufi dakinta tana karkada jiki.
Kawai Ahmad kansa ya dafe, haka auren yake ko kuwa sa'a ce shi baiyi ba, Yafi awa yana sakawa da kwancewa, kan ya Mike ya nufi daki Don tabbas ya kamata ya saka full stop, gini da take zance an riga da Angama kawai bayasan barin gidan ne Don Bata girki sede a aiko daga cikin gidan.
Seda sukai Kwana biu basa magana kowa yayi zuciya, dukda dukkansu a takure suke ko ba komai ai suna son junansu. Ganin hakan bazata kai musu ba yasa Ahmad ya sakko Se kuma dinke aka fara shiri na Kwana uku babu fada wanda rabon ayi haka Tun Satinsu na farkon aurensu. Daga nan aka daura.
Ahmad ya shigo a gajiye yayi sallama Dama ba aladarta ce amsa sallama ba Balle kasa ran idan zata shigo guri ta amsa, dago idonta tayi ta kalleshi shima ita yake kallo,
"sannu" Tace dashi kafin ta maida kanta Zuwa TV, bai amsa ba ya shige dakinsa ko ina a hargitse Don Bata gyarawa kuma tace kuyangu bazasu shiga mata dakin miji ba, wata uku da aure duk ya fita a hayyacinsa, hajja kullum complain dinta Kan ramarsa ne da nawwara bata Zuwa gaisheta, hakuri ya bata sannan yace yau zata zo.
Bayan yayi wanka ya fito, Tana zaune inda ya barta, gefenta ya zauna Yana fadin
"armour yunwa"
Kallonshi tayi tace
"Kaje kitchen akwai"
Kansa ya girgixa tare da sakin siririn tsaki yace
"kije ki zuba min mana"
Baki wangalau tace
"kana da damuwa baka ganin kallo nake, ka jira awa daya ya rage na gama se na zuba maka"
Nawwara Nada ban mamaki, kullum Se sake bude Jakarta ta rashin mutunci take
"Ke wai haka ake zaman aure, haka aka koya miki? "
"toh nan ka koma? Haka Naga anayi kaji"
Mikewa yayi ya nufi kitchen Seda yaci abincin yana me Dana sanin auren nawwara, Karo na babu adadi yaji ya rasa wani jigo wato raudha, dole bazai taba ganin daidai ba yadda ya yaudari baiwar Allah, ya saka ta kuka duk saboda shi yanzu da ita ya aura da yasan bazai ci Karo da wannan matsalolin ba. Ya cuci kanshi don ya tabbatar raudha is in a better place with a better person. Don baya mantawa sun hadu da Ismail satin da ya wuce ya dawo Daga Kai raudha school, yake tambayarsa yadda akai yasan raudha nan yace
"Man, it was arranged Amma ban taba tunanin haka abin zai zama ba, Duk duniya babu Wanda ya kaini Saar mata, she's a blessing to me, she completes me without raudha a rayuwa ta I'll be shattered "
Ahmad kamar zuciyarshi ta fito haka yaji Don haka sallama sukai da Ismail ya bar gurin Cikeda nasanin Abinda yayi. Yana kammalla cin abinci ya fito Daga kitchen, Bata tashi ba har zai wuce dakinsa se ya dawo yace
"bakida tarbiya, bakisan Meye aure ba, shashasha kawae"
Dariya tayi tace
"banyi tunanin haka ba, dakin da aka baka tarbiya nima nan aka bani, kuma haka na tashi naga babarka tana yiwa babanka so am following her step"
Kau kake ji ya dauketa da Mari Yana huci, bai taba tunanin iskancin nawwara yakai haka ba.
Shatuuu
BINABASA MO ANG
...ME RABO KA DAUKA
General FictionKowacce mace a duniya allura ce a cikin ruwa ME RABO KA DAUKA. Kaddara kansa mu hadu da mutane da yawa, wasu mu cutar dasu, wasu su cutar damu, wasu su bar Sautin muryoyinsu cikin kunnuwanmu, wasu Takun tafiyarsu cikin zuciyoyinmu, wasu su koya mana...