” Eheee!!! Ai dama na gaya miki duk da ta gudu zamu iya dumar da Sarki! Kin ga idanuwan shi kuwa !! Wollah ni wannan wasan ya burge ni” Zulaikha kenan ke magana. Ta ci gaba da cewa ” Yawwa! Nikam y’ar uwa yaya akayi kika iya shawo kan wannan d’an taurin kan ? Ina nufin magatakarda ” Ubaidah ta mik’e tsaye tace Hmmmm kina wasa da ni ! Ai wannan duk aikin me sauk’i ne ,kin san yanzu sai ki siye mutum da sulalla ” suka yi shewa harda tafa hannu sannan suka ci gaba da hira…..
“Nasir ga GUGUWA can yana tahowa kuma gashi mu bamu da gurin fakewa yanzu yaya zamuyi kenan? ” Nasir yayi shiru yana kallon yadda iskar ta ke zuwa ga shi da k’arfin ta take zuwa ga su kuma a tsakiyar HAMADA kafin suyi wani tunani har GUGUWAR ta iso inda suke ta ‘kank’ame Yaron da ke hannunta ta durk’usa gami da rufe idanuwan ta ,GUGUWAR tayi ta kokawa da goyon da ke bayanta har yayi nasarar fincike wa ,iskar yayi wani irin kururuwa mai tsoratarwa yayi sama da jaririn kafin kace me a take gurin ya washe kamar ba’a yi ba.
Da gudu ta bi hanyar da GUGUWAR ta nufa tana kiran d’an nata NAWAZ!! NAWAZ!!! Wayyo Allah d’ana Nasir ya nufo inda take yana bata hak’uri yayin da ta rungume NAWAF a jikinta tana ta kuka ” Nasir yanzu yaya zan yi!!? Ka duba yadda GUGUWAR HAMADA ta raba ni da d’ana ! Ina zata kai shi ne!!? Nasir wa zai kula da NAWAZ!! Ki taimaka ki dawo da shi don Allah !! Kar ki raba ni da shi! A fusace kuma ta tashi tace ” Me yasa ni bazaki d’auke ni ba !! Kika tafi min da d’ana kika rabashi da d’an uwanshi ganin tana neman sulale wa k’asa yasa Nasir yayi sauri ya rik’e ta gami da d’aura ta a kan doki sannan ya koma ya d’auki NAWAF ya hau dokin shima da hannu biyu kachal yake tuk’in basu wani ‘kara gaba sosai ba ya hango su Mahir da wata k’atuwar runduna :oops:. Shalini ta sauk’o daga kan dokin a gala baice ta rik’e hannun d’an nata tace ” Nasir ku gudu kawai ! Ku tafi kar su zo su kama ku ,kar su maida min d’ana inda zai shiga halin k’angin bauta ! Ka tafi kawai nace maka!” Nasir cikin hawaye yace ” A’a Allah ya baki nasara bazan tab’a barinki a nan ba zasu kama ki kuma na tabbatar cutar da ke za’a yi!” “A’a Nasir!! In kana yiwa Allah ka tafi ,nidai abu d’aya nake buk’ata daga gareka ,shine ka sanar da d’ana mahaifiyar shi tana k’aunar shi,kuma zata kasance mai k’aunar shi har tsawon k’arshen rayuwar ta!” Ta ciro wani sark’a a wuyan ta ta aza a hannun Nawaf tace ga wannan shine kad’ai kyautar da zan iya bashi. Ta ciro d’ayar sarkan tace ” wannan kuma duk sanda kuka yi ido hudu da Nawaz don Allah ka bashi.” Ta ciro wasu warwaraye na gwal ta mik’a wa Nasir tace ka sayar da wannan domin ka kula da kanka da kuma abincin d’ana!” Cikin kuka Nasir ya kad’a dokin a guje suka yi gabas ba tare da yasan inda suka dosa ba , su Mahir kuwa da sukaga basu iske yaran ba sai suka kamata suka koma da ita chan masarautar SHIMLA………….

YOU ARE READING
GUGUWAR HAMADA
AdventureLabari na Sarauta, yaƙi, cin amana da labari ne da ya ƙunshi soyayya, tausayi da ban dariya......