Babi na 17

852 67 0
                                        

Tsintar kansu sukayi cikin wani tafkeken d’aki cike da wasu murtuqa murtuqan macizai Afreen da ke Zaune a gurin kasa motsawa tayi jiki na b’ari a take ta sulale a wurin sumammiya ,yayinda macizan suka fara nannand’e ta ,cikin dabara Nawaz ya fara kwallo da macizan hakan ya bashi damar samun hanyar da zai k’arasa inda Afreen take a sume ,ya sunkuceta a kafad’a sannan ya nufi hanyar wata k’ofa da ya hango ,bai damu da farmak’i da macizan suke kawowa ba har ya k’ure daga wannan d’akin ko me ya taka a bakin k’ofar oho ! Kawai se k’ofar me macizai ta rufe da kanta ganin haka yasa ya bi hanyar da yaga itace kad’ai hanyar da ya gani a gurin..

           Wasu k’ofofi ya iso duk a rufe suke ,ga kuma masu gadin ko wanne k’ofa a tsaye kamar gumaka, a gaban shi aka shigo da wani dattijo sai faman kokawa suke yi da wad’anda suka rik’e shi ,har wannan lokacin Afreen na kafad’ar shi ,suna had’a ido da Dattijon kawai se yace ”  Nawaz!! Nawaz !! Kai ne ?? Amma dukan da mutanen ke masa ya mugun nak’asa shi suka wurga shi cikin wani d’aki wanda da kyar ma k’ofar ta bud’e don da gani an dad’e sosai wannan k’ofar ba’a waiwaye ta ba har gindin ta ya zama mafakar k’ananan kwari. Hankalin masu gadin yayi kan Nasir basu san lokacin da Nawaz ya shige ba ya fita daga gurin yana tuna irin Muryar da yaji Nasir yayi amfani da shi ,kamar ya tab’a ji a wani waje, sai da ya fice ya tuna cewa shine tsohon da ya buge a birnin Ramali kuma sark’ar dake lilo a wuyan tsohon itace irin wanda ya gani ta fad’i daga jikin wannan me kama da shi d’in nan ,gashi kuma tsohon harya san sunan shi ,abun ya matuk’ar kulle mar kai sosai ba kad’an ba amma a yanzu ta lafiyar masoyiyarshi yake yi ba wannan ba shi yasa ya bi wata y’ar k’ofa ya fice cikin kwanciyar hankali yana k’arewa garin kallo ruwa ya hango a wata rijiya wanda ta cika taf har bakinta ,cikin hanzari ya nufi gurin ya shimfide Afreen a k’asa yasa abun d’iban ruwan ya kamfato sannan ya yarfa mata, a firgice ta tashi ta zauna tana maida numfashi gamida nuna razanarta a fili ta rungume shi jikinta na rawa, murmushi kawai yayi yace ” matsoraciya babu komai yanzu tashi mu tafi ” babu musu ta mik’e suka fara zagaya gari da dai sukaga sun rasa hanya sai suka yanke shawarar tambaya ko zasu samu sunan garin da suke ,ai kuwa suna had’a ido da bafaden da zai tambaya d’in bud’ar bakin shi yace ” kai !! Gashi can !! Ku bisu!!! ” koda Nawaz yaji haka sai ya fisgi hannun Afreen da gudu su kuma sojojin suka bi bayan su a guje ,su tsallake chan su haura nan har cikin kasuwar garin ,duk Afreen ta galabaita da kyar take numfashi se haki take ganin haka ya wafce wata butar ruwa daga hannun wani yana shirin shan ruwa ya damk’a mata tana gudu tana sha rabi na zubewa, da kyar suka samu wata y’ar k’ofa suka rufta ciki se haki suke yi ,Nawaz yana lek’en su har suka wuce yayinda Afreen ta yi lakwaf a jikin Nawaz sai sauk’ar da numfashi take yi…………….

             “Waye nan?” Tambayar da aka mishi kenan bayan y’an mintina da aka wurga shi a wannan kurkuku mai duhun. Ba tare da ya sake magana ba taci gaba da maganganun ta irin na kullum kamar yadda ta saba. “NAWAZ DA NAWAF SUNA NAN TAFE!! K’ARARRAWAR MUTUWAR KU CE TAKE KAD’AWA!! Y’AY’ANA NA NAN TAFE SAI SUN D’AUKAR MIN FANSA!!!!……..KU TSORACI DAWOWAR GUGUWAR HAMADA!!!!!………..

     Maganar da ta doki kunnen Nasir kenan kuma mai ambaton wannan maganganun bata daina fad’a ba se maimaita wa take yi kamar me karatu. Cikin murya me rawa da kuma hawaye Nasir yace ” Sarauniya Shalini!! Rrrrr….. AH I…NNA!!!!!………….

GUGUWAR HAMADAOù les histoires vivent. Découvrez maintenant