Babi na 9

974 93 0
                                        

Gari ya waye, duk da ma sanyi akeyi hakan bai hana rana b’ullo wa ba,sanyin da ake yi a garin ya saka Nawaf d’aukan wani d’an bargo maras nauyi ya rufe kansa da shi hakan yasa baka iya ganin fuskar shi me kyau suna tafe shida abokin shi Jabeer domin tsabar zumud’i ma basu jira baban nasu ba suka kama hanya…

      Tafe suke Jabeer yana ta mishi tad’i amma shi kuwa yana ta faman kallon k’auye a haka har suka k’araso kusa da masarautar ,ginin ya tsaru sosai ga uban tsayi ,yana ta kalle kallen shi ya hango ta tsaye sanye da kaya na alfarma shigarta Sak na Sarauniya Jaseena lokacin da take kogo sai shafa kan wani doki take yi fari sol da shi ,ai anan Nawaf ya ja birki turus !! Baki a bud’e ya zaro ido waje yace ” Allah mai halitta!!” Jabeer da ke neman inda abokin nashi yake kallo yace ” nifa ban ga komai ba Kazo mu tafih kar mu rasa zaman gaba ” Nawaf ya fizge hannun shi da Jabeer ya rik’e yace cikin hasala ” Kai barni mana!!” Ya ruga cikin sand’a ya wuce babu wanda ya ganshi. Tafiya take cikin nutsuwa ,takunta d’ai_d’ai tana wasa da bakin mayafin ta ,shi kuwa sai sand’a yake a bayan ta har ta shige wani d’aki ba tare da ta turo k’ofar ba ta tsaya taje gashin kanta a gaban madubi ai kuwa sai suka yi ido hud’u, a take ta saki wani irin ‘kara wanda yasa duk masu gadin kusa da gurin suka shigo ,kad’an ya rage su chafke shi kuwa da kyar ya sha ai kuwa da Jabeer ya ganshi da gudu shima ya ranci ta kare suka bar gurin ,ganin haka yasa masu gadin suka koma.

     Ita kuwa Gimbiya Saleena kujera ta ja ta zauna se dariya take yi , ita ba tsoro ya bata ba ,bak’in tukunyan da ta gani a fuskar shi duk yayi dabbare dabbare a fuskar shi ne ya bata tsoro , amma yadda taga suna guje guje da masu gadin ya mugun bata dariya…….
     Nawaf kuwa ko da ya samu ya nutsu a filin wasan babu abunda yake tunani irin kyaun da wannan yarinyar take da ,shi ihun ma dariya ya bashi, Shi kad’ai ya bushe da dariya wanda hakan yasa duk mutanen gurin suka juyo suna kallon shi ,wasu ma dariyar fuskar tashi suke yi shi bai sani ba, Nawaf kenan sarkin shirme

Filin ya cika mak’il baka ganin komai se kawunan mutane kamar tururuwa, manyan masu matsayin kuma sune a saman benen ,sarki Abdoul-Rahman da Sarauniya Ruqaiyah suma suna ciki gefen da Nawaz ke zaune ,daga shi sai sarki Abdallah tun da suka zauna sai kallon kallo suke yi musamman sarki Abdallah ya fi kallon shi hakan ya sa ya tashi domin barin gurin .Sarki Abdallah ya gane saboda me ya tashi shikam ya ji matuk’ar son Yaron a zuciyar shi, kawai murmushi yayi ya juya yaci gaba da kallon wasannin da ake gudanar wa.

         Tafiya yake cikin nutsuwa cikin garin shiru duk an tafi gurin kallon bukukkuna sai mutane d’ad’d’aya suke wuce shi a hanya , takun shi kad’ai zai nuna maka ya dama ya shanye a sanin d’abiun gidan sarauta da kuma yanayin gudanar da rayuwar su, idonshi a kan wasu dawakai da suka tunkaro hanyar da yake kawai suka gwabzu cikin girmama wa ya d’aga wannan tsohon gami da gyara masa zaman mayafin shi ,kafin baba Nasir ya d’ago shi kuma ya juya zai tafi bayan yayi masa Sannu ,Muryar da yaji irin ta Nawaf ne Amma abunda yasa bai damu ba ,yasan Nawaf shi da saka irin wad’annan kayayyakin sai lokacin da gaskiya tayi halin ta ,mahaifin su ya karbeshi a matsayin d’a! Jikin shi ya yi sanyi a Wannan lokaci ya bi Nawaf da kallo har ya b’ace daga gurin ,Yana tafe Asad na biye da shi ko shima bai sani ba!!.

          Washegari da sassafe Nawaf ya fito gari ko karyawa bai yi ba yana tafe yana y’ar wak’ar sa yaji ance ” bawan Allah ka jefar da sark’ar ka!!!” Kafin Nawaf ya juyo Nawaz ya mik’a masa sark’ar ,abunda ya bashi mamaki shine zanen da idonsa ya gane masa ,na suna a tafin hannun Nawaz  yana had’a ido da Nawaz duk suka ja da baya ba tare da sunce komai ba suka juya kowa yaci gaba da harkar shi ,amma zukatan su cike suke fal da tambaya ,ganin yadda kamar tasu ta baci………

GUGUWAR HAMADADonde viven las historias. Descúbrelo ahora