Cikin murya me rawa take cewa ” Nawaz da Nawaf sunanan tafe!! K’ararrawar mutuwar ku ce take kad’awa!! Y’ay’a na na nan zuwa sai sun d’auka min fansa bi-iznillah!! Ku tsoraci dawowar GUGUWAR HAMADA!!! ” abunda take ta fad’a kenan kamar wanda aka ba wa hadda ,Jim yayi a gurin k’irjin shi na dukan goma sha, ya rasa me hakan yake nufi a ranshi yaji yana son ganin wannan tsohuwar. Wani shu’umin murmushi Mahir ya saka sannan ya fara magana cikin Muryar nuna isa ” in dai wannan tsohuwar banzar CE zaka gaji da jin kalaman nata irin na mahaukata, ai yau kimanin shekaru ashirin da wasu watanni kenan tana sarkafe cikin wannan kurkukun ,babu wanda zai ci amanar sarki Abdallah ya kwana lafiya !!” Ko da Mahir ya kai k’arshen maganganun da yake furtawa Nawaf bai dena kallon wannan k’ofar ba ,yana cikin wannan halin ne wasu ma’aikatan gurin suka shigo da tukunyaye a hannu kowanne d’auke da abinci cikin salon wulak’anci suke wurga musu gayan tuwon cikin d’akin sannan su tura musu kwanon miyar ma a wulak’ance ,da kyar na ciki suke lalumar abincin domin wani ma ya shekara arba’in babu haske balle hira da mutum d’an uwansa, haka Nawaf ya bisu da kallo har suka b’ace bai d’auke idanuwan sa da suka ciko da kwalla ba tare da sun gangaro ba! Maganar matar ne ya sake janyo hankalin shi ya maida duban shi ga k’ofar ” Shin ban fad’a muku ba ? Cewa d’ana yana nan zuwa?!! Toh gashinan lallai lokaci kad’an ya rage muku azzalumai!! ” duk kalaman ta sun dagula masa tunani, ji yayi an ja hannun shi sun nufi wata y’ar siriryar hanya wanda k’arshen ta wata k’atuwar k’ofa ce itama ,kafin su k’arasa gurin kuwa har an bud’e k’ofar tun daga gurin Nawaf ya fara hango kayan yak’i iri iri masu ban al’ajabi domin wasun ma bai tab’a ganin irin su ba, wata Kyakkyawar takobi ne a soke cikin ‘kasa a tsakiyar d’akin sai d’auke ido take yi ita kad’ai, ajiye kayan yak’in da suka shigo da shi yayi sannan ya dubi Mahir yace ” wannan fa?” Mahir yace wannan tun zamanin sarki na biyu a wannan masarautar mai suna SARKI NAWAZ DAN JAMAL aka k’era ta shi kad’ai ne ya iya d’aga wannan takobin tun bayan rasuwar sa kuma babu wanda ya iya d’aga ta yanda ya ajiye ta haka take ko girgiza bata tab’a yi ba. Zaro ido Nawaf yayi yace lallai Wannan takobin yana tattare da tarihi.
Shafa takobin yake yi a hankali Mahir kuwa ya tsaya kallon shi, ko da yayi yunkurin d’aga takobin kuwa sai karaf ya jita a hannun shi ,ga mamakin shi ko nauyi bai ji ba ,cike da mamakin hakan Mahir ya ce “yaya akayi haka! Yafi sau d’ari ina jarraba d’aga wannan takobin na kasa kamar yadda yau kusan shekaru d’ari da hamsin babu wanda ya ko girgiza wannan takobin ,babu shakka zan sanar da me martaba

YOU ARE READING
GUGUWAR HAMADA
AdventureLabari na Sarauta, yaƙi, cin amana da labari ne da ya ƙunshi soyayya, tausayi da ban dariya......