Babi na 18

951 73 0
                                        

Da rarrafe ta k’araso kusa da inda taji Muryar Nasir na tashi ta zauna duk gab’ob’in jikin ta na karkarwa a hankali tace ” kai ne? Kaine ko mafarki nake yi ? Shekaru sama da ashirin ba wasa bane ! Nasir Kaine ko murya ce ,na shiga rud’ani ,na yi hauka mara adadi ,na zauce ,naci datti iri iri haske rabona da ganin shi tun daga bakin wannan ginin k’arfen da ka gani ban sake saka d’an Adam ko dabba a idona ba, Nasir nayi kuka mara adadi da naji abunda wanda yafi soyuwa a zuciyata yace a kaina, na kwana cikin wahala na tashi a wahale ,Nasir ban yi tsammanin zan iya kallo da wad’annan idanuwan nawa ba domin na saba da duhu ,ni ba a mace ba ni ba a raye ba,Nasir na rabu da y’an uwana dad’in dad’awa y’ay’a da na tsugunna na haife su ,ina ma ni na shayar da kayana! Da sunga gata iya gata !! Ka gaya min Nasir ina Nawaf yake ne! Nasir baka had’u da Nawaz d’ina ba? Nasir ka amsamin in ji sanyi a raina ! Wannan shine karo na farko da naji motsin d’an Adam a cikin wannan akurkin…
      “Naga Nawaz !! Raheena naga Nawaz yanzun anan kuma Nawaf yana nan zuwa ,na tabbatar zasu had’u!! Ina da yak’inin komai ya kusa zuwa k’arshe! Gaskiya zatayi halinta a karo na farko!”………

            “Gimbiya Saleena dole in tafi neman babana ,shi kad’ai ya rage min ,bani da kowa in har na bari sukayi masa illa bazan tab’a iya yafewa kaina ba domin kuwa duk abunda ya faru dalili na ne ! Ni da tab’a musu abun su ni na d’auko wannan takobin mai cike da d’umbin tarihi a k’asar Shimla kinga kuwa ni ya kamata in d’auki duk wani horo da zasu zartar a kan baba ba shi ba!” Toh amma fa Nawaf akwai had’ari a abunda zaka aikata ,bai kamata ka tafi kai d’aya ba ,kayi hak’uri nasan Sarauniya tana iya k’ok’arin ta na neman hanya mafi sauk’i ” murmushi kawai Nawaf yayi jefi jefi yana jefa duwatsu cikin ruwan da ke tsakiyar masarautar a zagaye da gini sannan kuma yana da hanya wanda ruwan ke gudana. Mik’ewa yayi ya tsaya a saman ginin wanda tsakanin shi da ruwan ko da igiya aka zira zai kai mintina hud’u kafin ya isa ga ruwan amma haka ya sa kai ya afka cikin ruwan ,ganin hakan ya burgeta itama ta cire abayar ta da ta d’aura a saman kayan ta afka cikin ruwan nan suka fara watsawa junan su ruwa suna ta dariya ,lokaci guda wani farin ciki ya ziyarci Nawaf…….

       Duk abunda suke yi Sarauniya Jaseena tana tsaye saman benen d’akin ta tana k’are musu kallo ,bata tab’a ganin irin wannan nishad’i k’arara a fuskar Saleena ba ,hakan ya burgeta sosai, ba kad’an ba don tuni ita har ta kammala binciken da zatayi a kan ko waye Nawaf ! Duk wasu abubuwan da take buk’atar sani ta ji su daga bakin magatakarda na k’asar SHIMLA da su Mahir suka kusa hallaka wa , ya tsinci kanshi da nadamar abunda ya aikata yayinda wasu y’an kasuwa daga nan suka tsince shi a hanyar su ta dawowa ,ya kuma buk’aci ya ga Sarauniya wannan shine yadda akayi. Kuma duk shaidun da ya kamata ya gabatar suna chan k’asar SHIMLA wannan shine kad’ai abubuwan da take buk’ata!……..

       Juyawa tayi ta koma fadarta yayinda tana isa ta iske mijinta sarki Hydar ya dawo daga wata dad’ad’d’iyar tafiyar da yayi na kusan watanni shida, nan sabuwar babi ya bud’e suka shiga hirar yaushe gamo cikin soyayya da kewar juna……..

GUGUWAR HAMADADonde viven las historias. Descúbrelo ahora