Zaro idanuwa Nawaf yayi kafin yayi magana har Mahir ya fice daga gurin gami da yin umarni a sojojin gurin da cewar kar su bari Nawaf ya fito. Nawaf na yunkurin bin shi kenan yaji an rufe k’ofar ya koma ya tsaya juye juye yana neman gurin fita Allah da ikon shi ya hango wata yar taga chan sama da kyar ya tattaka ya dira ta wajen ya kuma manta bai jefar da wannan takobin ba yabi wata y’ar hanya ta kaishi kasuwa nan suka tattare kayayyakin su shida Jabeer suka nufi hanyar komawa DUSHA kafin kace wani abu har sun b’ace………
Gudu kawai suke yi ba k’akk’autawa basu ankara ba sukaji k’arar kibiyoyi suna ta sauk’o wa ,k’ara gudun dokin nasu sukayi ba tare da sun juya ba ba kuma tareda sun san inda suka nufa ba ,sojojin SHIMLA har sun gaji sun juya su basu ma sani ba ,saida suka tabbata babu masu bin su sannan suka rage gudu. Wani daji suka hango daga chan nesa daga gani guri ne mai Ni’ima dama sun gaji ga k’ishirwa haka a daddafe suka k’arasa dajin nan suka yada zango domin gurin a wadace yake da ruwa mai gudana da kuma kayan itatuwa……….
” Wannan umarni na ne!! Ku je ku nemi duk inda wannan yaran suka fito a kawo min su da ransu, in ba haka ba duk sai kun raina kanku!! ” sarki Abdallah kenan yayi wannan maganar cikin hasala ba tare da ya juyo daga basu bayan da yayi ba ,kafin ya juyo har sun fice daga fada.
Ubaidah da ke zaune ta mik’e fuska a murtuk’e tace ” Allah ya baka nasara! Yaya za’ayi ace Wai yaro da bai wuce shekaru ashirin ba ya d’aga wannan takobin wanda yau kimanin shekaru dubu d’ari da hamsin babu wani jinin sarauta ko mai mulki na wannan masarautar da ya iya d’agawa bayan sai wani wanda ba ma a nan birnin yake da zama ba zai d’aga ?? ” sarki Abdallah ya daka mata tsawa har saida ta tsorata, ya umarce ta da ta fice ta bashi guri babu musu ta fice simi simi da rawar jiki. Ko da ta tafi d’aki kasa zama tayi se sak’e sak’e take yi tana gudun kar abunda take tunani ya zamo gaskiya ,kar Nawaf ma’keri ya zama Nawaf d’an sarki! Da wuri kuma ta kawad da kanta gefe gami da gusar da wannan tunanin amma Sam hankalin ta bai kwanta ba. Nan ta yanke shawarar kashe magatakarda domin gudun kar wataran gaskiya ta fito ya fallasa ta ………….Su Mahir kuwa kasuwa suka nufa suka samu ayarin da su Jabeer suka biyo nan suka sanar dasu daga inda su Nawaf suke ,ba tare da b’ata lokaci ba Mahir yaja ragamar tafiyar tare da mayak’an Shimla kusan arba’in zuwa k’auyen DUSHA.

YOU ARE READING
GUGUWAR HAMADA
AdventureLabari na Sarauta, yaƙi, cin amana da labari ne da ya ƙunshi soyayya, tausayi da ban dariya......