Wajen la’asar suka isa Birnin Shimla tun safe da suka taso hakan ma don suna yin gudu ne, kowa yana gudanar da ayyukan gaban shi cikin sauk’i suka zo wucewa Mahir na dukan wani bawan Allah Wai ya shiga hanyar da Sarauniya Ubaidah zata wuce Yaron yayi matuk’ar bawa Nawaf tausayi don daga gani ma bashi da wani galihu hakan yasa Nawaf ya sauk’o daga dokin shi ya nufi inda Mahir yake dukan Yaron yana zuwa ya fizge shi cikin salo na dabara yace “kai idonka yana ina ne zaka bi hanyar wanda ko zaka k’arasa rayuwar ka baza ka kai matsayi irin nata ba?!! Cikin wayo ya wurgar da Yaron gefe yace ” Haba jama’a!!! Ashe baza ku girmama wanda ya girme ku ba?” Ya nuna Mahir ya ci gaba da cewa ” ai wannan da kuke gani Isar sa ta kai ! Da har zaku zo kuna sashi gumi a tsakiyar rana ,ranka shi dad’e ina ganin Sarauniya fa zafin rana zai dameta ,me zai hana ne ta bar wajen nan saboda bai dace da ita ba!” Hakan da Nawaf yayi ya burge Sarauniya Ubaidah da shi kanshi Mahir hakan yasa Mahir ya mai da dorinar da yake dukan Yaron yace ” kai kuma waye?” Nawaf yayi wata y’ar dariya yace ” ni ba kowa bane kasuwanci ke kawo ni nan ina yin K’ira ne na ko wanne irin k’arfe, daga saman dokin da take Sarauniya Ubaidah tace ” daga yau kai da abokan ka duk wani kayan yak’i da masarautar mu ke buk’ata ku zaku dinga k’era ta!” Suka yi mata godiya ba tare da tace komai ba ta cigaba da tafiyar ta yayinda Mahir ya bi bayanta a nashi dokin,har saida suka k’ure sannan ya je ya d’aga Yaron ya bashi ruwa , yana dawo hayyacin sa ya masa godiya akan ceton shi da yayi domin yasan da yanzu wata’kila an fille masa kai ma! Kwanan su uku a cikin garin suka gama sayar da kayayyakin su sannan sukayi haramar komawa……..
” Nawaz!! Ohhhhh Haba d’ana har yanzu kana so kace baka tashi bane? Ta fad’a idonta a kan shi yayinda yake Kwance a kan tangamemen gadon shi na alfarma. Tabbas ta san idon shi biyu kawai yayi likimau ne don bai son fitowa. Bata kuma cewa komai ba ta juya ta fice a d’aki fuskar ta d’auke da murmushi ,ya tashi ya saka rigar shi cikin sauri ya bud’e tagar d’akin shi ya gama lek’a wa babu kowa a chan k’asa sanadiyyar d’akin nashi yana hawa na uku , bai ga kowa ba cikin rashin tsoro da k’warewa a gun rigima ya fita yana daddafa wa a hankali har ya iso jikin wani taga a hankali ya bud’e ya dira ciki yana dariya.
Kallon kallo suka tsaya yi ma juna daga shi har ita domin kuwa ba wanda yayi tsammanin gani cikin d’akin ya gani ba, wannan budurwa ce wanda bazata wuce shekaru goma sha takwas ba a duniya sanye da doguwar riga wanda daga wuya duk ta cinye haka ma hannayen rigar hannunta guda d’auke da tsintsiya d’ayan kuma d’auke da tasa (bowl) babba cike da kayan marmari duk ta had’a gumi ,rigar ma duk tayi daud’a ,bai daina murmushin da yake yi ba kuma bai ce mata komai ba ya wuce ta gefenta gami da zaro dami (bunch) guda na innibi ya bar d’akin kanta a k’asa kamar munafuka. Kai tsaye ya wuce d’akin cin abinci nan ya tarar da sarki Abdoul-Rahman da Sarauniya Ruqaiyah zaune suna shirin yin Karin kumallo duk ya gaida su cikin girmama wa sannan ya ja kujera ya zauna suka shiga aikin ci.
AFREEN na zaune cikin akurkin d’akinta duk tunanin Yerima Nawaz ya hanata sakat, duk da shi bai ma san me take yi ba ita kam ta zama duk inda yake tana lab’e domin kuwa babu abunda take sha’awa kamar taga yana magana ,Muryar shi ,yanayin da yake tafiyar da motsin bakin shi , tafiyar shi bugu da k’ari yadda tunanin shi ya hanata sakat duk da ma tasan cewa sama tayiwa yaro nisa saidai yasa ido yayi kallo! Dad’in da take ji yau kuwa shine don yadda taga a karo na farko sun yi ido hud’u sannan har ya d’auki abin ci daga tasan hannun ta sai wani dad’i ya lullub’e ta. Ruwan da taji an kwara mata ne yasa ta mik’e cikin sauri jiki na b’ari tana goge ruwan fuskar nata da hannayenta gashin kanta duk ya jik’e ya mammanne mata a fuska. ” Sannun uwata! Ni ne zan je miki kasuwar ai ko ? Kin zo nan kin wani zauna ,ai ke baki gaji Hutu ba ! Yadda uwarki ta gama rayuwar ta a wahale haka kema zaki gama naki munafuka kawai in an yi magana ki fara hawayen iskanci , ga kud’i can gefen fitila je ki d’auka ki tafi kasuwa ,kinsan anjima kad’an zaki wuce aiki a fada amma don tsabar bak’in ciki don ba ke kike cin kud’in ba bari ki mana bak’in ciki ko?” Afreen ta zaro ido waje tace “kiyi hak’uri !! Don Allah ba haka bane wallahy dama jira nake ki fito sai inji me zan siyo a kasuwar ,matar ta mangare ta da bayan hannu tace fita ki d’auki kud’in!! Kuma saura ki siyo min abunda raina bai so ba kiga abunda zan miki a gidan nan!!”
Tafiya take jiki duk babu kwari gashi duk a jik’e sai sauri take dokawa tana kuka ,cikin sauri ta wuce su ,shi da abokan shi Ammar da Hassan Nawaz ya gane ta sosai ya kuma ga halin da take ciki duk da bai san yarinyar ba bai kuma san sunan ta ba ,sunan da ya sa mata shine JAMEELAH (KYAKKYAWA) Ammar ya kalleshi yace ” yarima yau kuma me ya samu jameelah ?” Shima mak’e kafad’a yayi yace Allahu ya’alamu!”. Chan bayan wani dutse ta samu mai ta zauna ta had’a kai da guwiwa tana kuka kamar ranta zai fita,………….
Kamshin turaren da ta ji ne yasa ta d’ago kanta a hankali domin ta gane wa idonta wanda ya ke wannan uban kamshin wanda tayi imani babu inda ta tab’a jin irin sa face a jikin Yerima Nawaz………

ESTÁS LEYENDO
GUGUWAR HAMADA
AventuraLabari na Sarauta, yaƙi, cin amana da labari ne da ya ƙunshi soyayya, tausayi da ban dariya......