Domin da ta samu sarki da haka bata faru har ya kai ga zartar da wannan hukuncin ba ,don haka ta k’addara a ranta ta yafe mishi har Abadan ,a tare suka maida duban su ga Y’AY’AN nasu cikin nuna so da k’auna Abdallah ya bud’e musu hannayen shi ,basuyi wata wata ba suka rungume mahaifin nasu yayinda ya umarci kowa yaje ya huta shi kuwa ya keb’e da Shalini ,ranar nan shi yataimaka mata gurin gyara jikin ta ,ta fito fes da ita saidai wannan jiki nata se a hankali zai murmure tayi shiru tana kallon shi ,gaba d’aya ta manta rabonta da shak’ar iska mai Ni’ima irin ta yau…….
Da rana ,yunwa taci Afreen gashi babu abunda take tunawa sai wannan muguwar uwargijiyar tata ,a ganinta in ta koma bata san yadda zata yi ta mata bayanin abunda yake faruwa ta bar gida ba ,ta dad’e a haka bata ankara ba taji an ja karan hancin ta ,tana d’aga kai suka yi ido hud’u da Gimbiya Saleena, tace ” yaya dai kin natsu haka kinata tunani ? Ai a ganina mace kamarki me kima da aji ga kyau babu abunda zai sata tunani irin haka ,ko de baku daidaita da Yerima Nawaz bane?” Murmushi Afreen ta sakar mata tayi Ajiyar zuciya tace ” tunanin da nake ba tunani ne akan komai ba Illah lokacin da naga wannan zuria ta sake had’uwa a k’ark’ashin inuwa d’aya sai naji dama ace nima zan ga nawa a lokacin ,ak’alla yau da na cika shekaru goma sha takwas chif chif ,ban san yaya fuskar tawa mahaifiyar take ba ,sai muguwar kishiyar uwa ,haka mahaifina ma ya fad’i ya mutu ba tare da ya sanar da ni komai game da uwata ba ,ya barni cikin k’uncin rayuwa da wahala ,sai lokacin da Allah ya kawomin wani jigo cikin rayuwa da sunan Yerima Nawaz ,da nayi zaton nice nake d’auke da mugun ciwon son shi amma sai naga ba haka bane duk k’anin mu muna begen juna….” Lokacin da take maganar duk sun shigo d’akin, Sarauniya Raheena da ta d’an ji k’arfin jikinta tun da suka shigo kowa ya lura da kallon mamakin da take yiwa Afreen ,ko da ta dasa aya Raheena ta matsa kusa da ita tace wannan fuskar itace fuska da ko a cikin mafarki na ganta bazan manta ta ba balle kuma a zahirance!!” Duk suka maida duban su ga Sarauniya Raheena yayinda taci gaba da cewa ” ke y’ar gidan Lakshmi ce jikar Lakshmi rani ma! Duk wani d’a da ya fito daga gidan ku kuwa fuskar shi bata tab’a b’uya wannan yasa na gane ki sarai ,mahaifiyar ki y’ar babban gida ne gidan mutunci ,Mun taso tare tun ina y’ar shekara biyu Mun shaqu sosai ba kad’an ba ,lokacin muna y’an shekaru goma sha takwas aka aurar da mu ,wanda ya aureta babban me kud’i ne kuma auren soyayya suka yi ,ko ba mahaifin ki bane Othman Omar? ” eh shine ranki shi dad’e ” murmushi Sarauniya Raheena tayi tace ” lokacin da aka haifeki bana nan domin ni kaina ban shayar da y’ay’a na ishashen nono ba balle kuma in san halin da y’ar uwata take ciki ,tunda nake a rayuwa ban tab’a samun sab’ani da Lakshmi ba” kusa da ita Afreen ta matsa tace ” naji dad’in jin wannan labarin ,kuma ko ba komai abokiyar zamanta ta ciyar da ni kuma har na girma ,abun da tayi min na yafe mata amma bazan sake zama da ita ba ,gurin iyaye na inda zan samu gata nan ya fiye min komai” cikin kuka Raheena ta rungume ta tace ” kina gida Y’ata nan ma gidan ku ne domin kuwa babu wani abu na Lakshmi da zan kasa rikewa komi lalacin sa!!!
Nan suka d’unguma zuwa cin abinci ,ranar dai sun ci abincin ne cikin kwanciyar hankali ,k’auna kuwa tana nan k’arara a idon kowanne daga cikin su ,Nawaf bashi da aiki se tsokana tun Nawaz na murmushi har ya fara maida martani ,abunda ita kanta Raheena ta lura da shi shine ,sarauta tana jinin Nawaz fiye da Nawaf ,komai nashi daban ne ,cin abincin shi ,maganganun shi da yanayin da yake kallon mutane wanda yasha banban da Nawaf wanda babu ruwanshi bai ma san ya sarautar take ba saidai burgeshi kawai da take yi tun yana k’arami…………….
Alhamdulillah!

YOU ARE READING
GUGUWAR HAMADA
AdventureLabari na Sarauta, yaƙi, cin amana da labari ne da ya ƙunshi soyayya, tausayi da ban dariya......