Babi na 2

1.6K 132 1
                                        

        Daga nan ta san cewa kashin ta ya bushe domin tasan tabbas sunga fitar ta ne . juyawa tayi gaba da baya,gabas da yamma ,kudu da arewa, sama da k’asa duk babu wani mafita da ya wuce ta saddaqar ta zubawa sarautar Allah ido. Suna k’arasowa duk suka sauk’a k’asa daga dawakan su kusan su biyar ne guda biyun Mahir da Nasir suna daga cikin manyan sojin yak’i na masarautar ,Mahir mugu ne na gaske shi yasa tafiyar su tazo d’aya da su Ubaidah da Zulaikha. Nasir kuwa mutum ne me sauk’in kai ga tausayi shi yasa Mahir yake cin karenshi ba babbaka a kan Nasir.
  
       Sauk’a itama tayi daga saman dokin ta rungume Yaron  da ke hannun ta ,yayinda d’ayan yana baccin shi a bayanta , gadan -gadan Mahir ya nufo inda take hannun shi da zabgegiyar takobi ko da ya k’araso itama ta zaro y’ar k’aramar wuk’ar ta ,yana isowa ya sa hannu zai wafce Yaron da ke hannun ta amma kafin ya kai ga hakan ta tsaga mishi fuska da wuk’ar tuni ya ja da baya ya zube k’asa sauran guda biyun suka rik’e shi suna duba lafiyar shi ,ganin haka yasa Nasir ya jata suka hau doki a guje dokin nan ya bar gurin , Mahir da ke Kwance ya nuna su da ‘kyar yace ” Ku .ku bi su!!! ” da gudu suka haye dawakan su suka bi bayan su Shalini yayinda shi kuma suka barshi nan cikin zafin rana ga yanka a fuska.

        Mayak’an biyu sun bi bayansu amma ko kyallin su basu gani ba balle kuma har su kai ga kamasu, haka suka juya suka koma don sun san ko da sun ‘kara gaba ba samun su za’a yi ba. Suna dawowa inda yake suka tarar da Mahir tsaye jikin dokin shi ,ya dubesu da ido d’aya domin dayan shine gefen da aka ji mar ciwon , yace ” ya na ganku haka?!! Cikin rikicewa suka ce “ranka shi dade bamu same su ba ,Nasir ya riga ya tseratar da ita Mun rasa hanyar da suka bi ,shi yasa kawai muka dawo” cikin zafin nama Mahir ya zare takobin shi ya fille musu kai ,ya maida takobin yace ” aikin banza aikin wofi!! Har zaku kasa kama wannan yar ficikar abun wanda batafi na murd’e mata wuya ba!!”
( kar fa ku manta masu karatu shima kasawa yayi saboda rashin dabara amma Sam baya ganin gazawar shi sai nasu !)..

      ”  Bazai yiwu ba!! Bazan tab’a yarda cewa Matata Shalini zata aikata abin da kuka ce ba!! Ta gudu da yaran fa kuka ce!!! ” Sarki Abdallah kenan yayi wannan maganar yayinda su kuma iyayen sharrin da munafurci suna zaune murna fal ransu! Zulaikha tayi karaf tace ” dama Mun fad’a maka cewa wannan matar fa ba matar mutunci bane! In ba haka ba kanta farau? Ai ba kanta farau ba! Mu shekara nawa muka lashe bamu Haifa ba ,ko b’atan wata bamuyi ba sai ita zata zo da wani sabon salo Wai har ta haihu a gidan nan ,ni na tabbata ba y’ay’an jinin mu  bane chan dai da su gada” tsulum Mahir ya tsoma baki ” Ai ranka shi dad’e ni ina tunanin wannan Nasir d’in mai jar fuska kamar an gutsuri gauta  ba zai wuce shine uban yaran nan ba domin kuwa shi ne yayi silar tserewar da tayi har in tak’aice maka ma Allah ya baka nasara tare ya gudu da ita ” Ubaidah da ke zaune sai yanzu tace ” toh ai kuna wani abunku duk wannan maganganun da kuke fad’a sarki ba yadda zai yi ba sai Mun gabatar mishi da shaida ” sarki Abdallah ya juyo cikin rud’ani yace ” wanne irin shaida kuma ?” Ubaidah tayi wani munafukin murmushi tace ” kai Mahir ! Shigo da magatakarda !” Basu wani d’au lokaci ba suka shigo tare da magatakarda. Cikin salo irin na munafukai ya shigo ya tsaya hannun shi rik’e da wasu takardu ya bud’e ya fara karantawa , abubuwan da ya karanta kuwa sun yi kama da irin maganganun da su Ubaidah suka yi don nuna cewa y’ay’an ba na sarki bane ,rubutun kuma Sak irin na Sarauniya Shalini hakan ya sake dumar da sarki Abdallah.(Allah sarki bawan Allah bai san cewa zagaye yake da munafukai da kuma azzalumai ba ! K’ira ga y’an uwa mata ! Duk inda ka kai ga Kishi da kyashi da kuma ganin kai toh lallai a karshe zaka zama k’ask’anta ce Marar kima, babu kuma ribar da zaka ci in ka cutar da wanin ka ,Allah yasa mu dace Ameen).

GUGUWAR HAMADAOpowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz