Babi na 11

1K 89 0
                                        

    Tafe take rik’e da tulu da gani neman ruwa zata, sai faman tattare yagaggen rigar ta take yi gashi ana iska da alama ruwan sama za’a yi.” Afreen!! ” daga nesa taji an k’irata ta tsaya chak domin ganin wanda ke kwala mata wannan k’iran haka ,kan dokin shi yake yana kallon ta suna had’a ido ya fad’ad’a murmushin sa ya cigaba da k’arasawa inda take tsaye , tuni ta kau da kai gefe cikin ranta tace ” wannan Wai me yake nema da ni ne? Mutum ba’a sonshi amma kamar maye ya mak’ale min!” Kafin ya iso ta juya taci gaba da tafiya ganin haka sai ya k’ara saurin dokin nashi itama da taga haka ai kuwa ta sake tulun nata ta ruga a guje yana binta a baya duk da haka bata gaza ba!

        Nawaz da iyayen shi suna isowa birnin Sultanpur ya sauk’a daga kan dokin nashi ya mik’a wa wani bafade domin ya shiga ciki da shi , bai bi ta kan iyayen nashi ba ya fice domin yaga gari ,yana tafe sai kalle kalle yake yi shi kwata kwata bikin ma da suka je bai wani burge shi ba, a cikin wannan halin ne Yaji ya ci karo da wata,ga dukkan alamu a tsorace ma take ,yana d’aga kai kuwa suka had’a ido da Afreen wanda tun da ta gane shine ta ‘boye a bayan shi gami da ‘kank’ame rigar shi ,shi kuwa se faman dube dube yake yi wa take wa wannan uban gudun. Wani murtuk’e fuska Nawaz yayi gami da damk’e hannun shi da ya ga ashe Wannan d’an iskan ne farouq yake bin ta yasan dama bazai wuce irin su ba! Farouq ya matso inda suke yana k’are musu kallo yayi wata mahaukaciyar dariya yana zagaya su ,ko girgiza Nawaz bai yiba yayinda farouq ya juya yana fad’in ” hey d’an lambu ! Ka juri zuwa rafi da tulu domin wataran sunan tulun nan fashashshe!! Ya wuce yana dariyar k’eta.

    Duk da maganar d’an uwan nashi ya Sosa masa rai duk Kalmar d’an lambu tafi ci masa tuwo a kwarya….
” me ya had’a ki da wannan mahaukacin kuma?” Nan Afreen ta fad’a masa abunda ya faru ,sannan ta nuna masa fargabar da take ji in ta koma babu ruwa gashi an fasa mata tulun, Nawaz ya shaida mata cewa babu komai zai taimaka mata

       ” Baba Mun shirya zamu tafi Shimla ” cewar Nawaf kenan yana zaune gefen baba Nasir, ” Toh d’an nan! Ka kula da kanka  Allah ya bada sa’a! ” Ameen baba ” ya amsa gamida juyawa ya fice daga d’akin , nan suka kama hanya su da ayarin su suka nufi birnin SHIMLA!…..

          ” wad’annan makamai gaskiya sun k’eru ga su da haske fiye da na farkon,ga kuma kaifi gaskiya wad’annan sun yi ,yanzu ka biyoni muje inda za’a kai wad’annan makaman ” duk wannan maganar da Mahir ke yi idon Nawaf na kansa har ya k’arasa, ba tare da yace ‘kala ba ya d’aura jakar kayayyakin a saman keken dokin sa ya bi bayan su Mahir ,tafiya kawai yake yi amma babu wani sukuni a tare da shi ,ji yake a take jikinshi ya zama babu kwari wani tafkeken k’ofa suka shiga wanda aka yi ta da wani irin k’arfe sojojin da ke iya bud’e ko wanne b’ari na k’ofar guda ashirin ashirin ne ,idan aka had’a guri d’aya su arba’in kenan, cikin wannan k’ofar wanda wanda yake wajenta yana kallon cikinta kuwa makeken filine ba k’arami ba kuma zagayayye duk wannan filin kuwa shima zagaye yake da wasu mayak’an suna tsaye rik’e da mashi a hannayen su ,tsakiyar filin a lailaye da Gashi kai kace simintin yashi akayi a gurin. Suna tafe saida suka iso tsakiya sai Mahir ya dakawa Nawaz tsawa ,cikin jarumta ya ja dokin ya tsaya, kallon Mahir yayi cike da tuhuma me zaisa yai masa wannan tsawa haka? ” wannan gurin da ka gani kana taka shi sunan ka matacce domin kuwa babban tarko ne a gurin wannan an Gina shi tun zamanin sarki  Affan d’an Abdallah sarakuna biyar kenan kafin sarki Abdallah na yanzu kaga kuwa tarko ne mai cike da hikima mu kanmu bamusan me yake faruwa da mutum ba yayin da ya afka ciki ko aka jefa shi domin na tabbatar ko ma menene da wanda ya shiga in zai samu dama zai so ya dawo don bada labari” Mahir na kai wannan ya bushe da dariya yace ” ina matuk’ar k’aunar wannan tarkon ni da kaina na jefa masu laifuka sun fi a k’irga wasun umarnin Sarauniya Ubaidah ne wasu kuwa na y’ar uwarta Zulaikha! ” shidai Nawaf kai kawai ya jinjina yana mamakin rashin tausayi da bushewar zuciya irin ta Mahir nan ya chanja hanya ya bi gefe gefe suka shige wani sukufin lungu wanda tsabar duhun shi sai da fitilu masu gadin wurin ke tsaye ,k’ofofin wurin da ke Jere basu da tsayi kuma da k’akk’arfan ‘karfen nan aka yi shi mai ubansun nauyi ,suna isa wata kofa yaji wata irin murya wanda daga ji me shi a jigace yake ,nan k’irjin shi ya fara dukan uku uku jin abunda wannan Muryar ke  cewa!!………….


 

GUGUWAR HAMADATempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang