Cikin wannan k’ofa da suka shiga gida ne madaidaici babu komai a ciki sai wata shimfid’a irin ta fatar dabba da ke shimfide a gefe ,wani gefen kuma akwai wata k’ofar ita kuma a rufe take, a hankali ya tura k’ofar yana ta nazarin d’akin Afreen kuwa na faman share yanar gizo da ya kama hannun ta a garin karkad’e wa tana ja da baya ta bugi wata y’ar karfe ai kuwa sai k’asan d’akin ya bud’e Nawaz da ke tsakiyar gurin ya afka ciki a firgice ta juya taga ashe abu ta dannan a wani b’angare ta hango matakala ai kuwa da gudu ta isa gurin tana k’iran sunan shi “Nawaf !!” Cike da firgici. Tsaye ta ganshi yana karkad’e jikin shi da yasha k’ura abubuwa ne iri iri a cikin d’akin wanda ya had’a da kundin tarihin birnin SHIMLA Afreen ta karkad’e takardan da niyyar d’aga wa amma ta kasa ta juya tana kallon Nawaz da yake ta fama da wata y’ar jaka wanda wasu takardu ne a jiki jakar tayi masa kyau hakan yasa shi ya rataya jakar ,Afreen tace ” Kazo kaga wannan babban takardan “!! Da saurin shi ya k’arasa inda take tsaye suka bud’e ya sauk’e k’asa suka fara karantawa abin mamaki Nawaz ya fara ganin abubuwa irin wad’anda suka faru a baya ,tuni ya rik’e kanshi yana rufe idanuwan shi a hankali ,gani yake kamar a mafarki kafin kace me har ya zube a gurin ,Anan Afreen ta shiga matuk’ar firgici hankalin ta yakai k’ololuwa wajen tashi gashi ko ta fita za’a iya ganeta saboda haka ta kifa kai a cikin shi tana ta zubar da kwalla har bacci b’arawo yayi awon gaba da ita a haka……………
” Nifa abun nan ya fara bani tsoro! Kace zai dawo amma har yanzu shiru, nasan cewa Nawaz ba yaro bane amma kuma komai zai iya faruwa, su wad’anda suke tare da shi kuma sunce kawai suma neman shi sukayi suka rasa ,ba shi ba Afreen! Ba dole in saka a raina ba don Allah? Shi kad’ai nake da ,shekaru ashirin da y’an kai ba wasa bane mai martaba!!” Sarauniya Ruqaiyah kenan tayi wad’annan kalamai tana me ture kwanon abincin da aka aza mata a gabanta, hankalin sarki Abdoul-Rahman yakai k’ololuwa wajen tashi ,nan yasa aka baza soji aka shiga neman su shida Afreen ,duk da Afreen y’ar aikin fada ne amma Sarauniya Ruqaiyah tana jinta sosai har cikin ranta saboda yanda taga d’an ta cikin farin ciki yayinda yake tare da Afreen hakan yayi matuk’ar tada mata hankali ,har dare yayi babu labarin su ,rannan kam in ance Ruqaiyah tayi bacci toh an yi karya domin kuwa komawa tayi yadda kasan jaririya haka ma a B’angaren Abdoul-Rahman shima de haka ta kasance……….
guguwar hamada.
Hasken rana ne ya hasko inda suke Kwance a hankali Nawaz ke bud’e idanuwan shi yana kare Hasken da ya ke d’auke masa iso da hannayen shi jin motsin numfashi yayi yawa ya sa ta farka daga nannauyan baccin da ya d’ebe ta ,tana tashi shima ya tashi zaune yana ta k’ok’arin tuno irin mafarke mafarken da yayi, wannan jakar da ya rataya ya fara laluma a firgice, Afreen dai nata ido.
Cikin sassanyar murya yace ” Ramali..Ramali… Afreen wannan jakar Ramali zamu kai ta dole mu kai ta zuwa chan!!” Toh ta yaya zamu fita daga nan bayan kasan cewa neman mu ake RUWA A JALLO!! Kuma na tabbatar suna nan zagaye da mu ,sannan zai d’auke mu kwana hud’u kafin mu isa Ramali ” Nawaz yayi shiru yana kallon ta har ta idar da maganganun da zata yi sai yace ” ASAD!! Asad zai kaimu Ramali” yana fad’in haka Asad ya bayyana bayan wata y’ar k’aramar k’ura da ta baibaye d’akin wannan shine karo na farko da Afreen ta ga Asad d’in Nawaz ido da ido, a hankali kuma yake sake rikid’e wa zuwa wani kyakkyawan saurayi yace ” Yerima Nawaz nayi kewarku sosai” yana maganar ne fuskar shi mai kyalli d’auke da murmushi ,Nawaz ya nufi inda yake ya rungume shi yace ” baka tab’a barin inda nake ba don na sha wahala ,muna cikin yanayin jin dad’i muka afka wani rami ,ni kaina bazan iya k’iyasce adadin lokacin da muka d’auka kafin mu iso ‘kasa ba ,muka fad’a d’aki mai maciz …….. ” Asad yayi saurin katse shi da ” duk nasan komai Yerima yanzu kar mu b’ata lokaci ya kamata mu tafi chan Ramali koma menene zakaji…………A firgice ya farka yana ta faman dube dube duk gumi ya jik’a shi jagaf kamar Marar gaskiya sai murje ido yake yi ,a cikin wannan yanayin ne Gimbiya Saleena ta bud’e k’ofa ta shigo ,ganin yanayin da yake ciki duk ta rikice ta nemo Sarauniya Jaseena suka shigo tare ,har lokacin bai wani dawo hankalin shi ba Jaseena tayi saurin durk’usa wa a gaban shi ta gama nazarin shi sannan ta umarci wata daga cikin ma’aikatan da a kawo mishi ruwa ya sha ,haka kuwa akayi ,yana farfado wa yace” suna zuwa !! Suna zuwa !! Ban san shi ba amma ina ganin wani mai kama da ni a wasu mafarkai na ,kamar yadda na ganshi a zahiri ranar da na fara zuwa wannan birnin ” murmushi Jaseena tayi tace ” Allah ya kawo su lafiya” duk suka amsa da Ameen…………
Kafin kace wani abu sai ganin su sukayi a Ramali ba b’ata lokaci masarautar suka nufa inda sukayi mamakin irin tarbar da aka yi musu kamar an san da zuwan su.
Sarauniya jaseena ce ke sauk’owa daga matakala da mijin ta sarki Hydar bayansu kuwa Gimbiya Saleena ne da Nawaf. Tun daga nesa suka had’a ido da Nawaz a take ya mik’e tsaye har suka k’araso ,Sarauniya ta umarci Nawaz da ya zauna nan fa tasa aka k’ira magatakarda ta sa hannun ta tayi nuni zuwa inda suke zaune tace ” ga chan Nawaz da kuma Nawaf ! Kuma ga jakar da ake buk’ata nan ta iso ba tare da an nemota da wuya ba , abunda ya rage shine ka sanar da su ko su Wanene su a yanzun nan”“Da farko de ina me neman gafarar ku bisa ga abun da na aikata muku na makirci wanda ba a son raina na aikata hakan ba ,sannan kuma nabi son zuciya ta na zab’i rayuwata akan tab’arb’arewar taku rayuwar har ga Allah ban yi don raina ya soba sai don kare mutunci na da na iyali na duk dan kishiyoyin mahaifiyar ku (Raheena) ta tozarta………… Nan ya kwashe labarin abubuwan da suka faru ya labarta musu. Cikin kuka yaci gaba da cewa ,bayan wayannan shekaru masu yawa kuma se suka nemi su hallaka ni domin sun ga gaskiya ta kusa yin halinta ,yanzu haka nasan hankalin su Kwance yake cikin ruwan sanyi basu san abunda suke gudu ne zai faru ba………..
Nawaz da Nawaf a tare suka mik’e idanuwan su cike da k’walla ya juya gefen shi na hagu yace ” Asad ka kaini SHIMLA!! Ka kai ni Shimla yanzun nan !! Nawaf da ke gefe yana neman da waye ake magana sai lokacin Asad ya bayyana a gaban idon shi cike da mamaki ya dubi d’an uwan nasa yace ” ka kaimu Shimla ” Gimbiya Saleena da ke zaune a gefe ta mik’e tace ” A ina za’a bar Masoyiyar Nawaf!!!? Duk suka bushe da dariya yayinda Afreen ke zaune tana bin kowa da ido bata ce komai ba ,se Saleena tace ” k’awata yaya de? Tayi murmushi tace ” ai in banda wani ikon Allah babu abunda zai hana jameelah zuwa! Ta mik’e tana murmushi wanda ya burge su duk suka rufe idanuwan su daga nan bud’e idanun da zasu yi sai gasu a Masarautar SHIMLA babu b’ata lokaci Nawaz da Nawaf suka rufe fuskokin su da mayafi sai iya idanuwan su kake gani kai tsaye kurkukun suka nufa ganin babu masu gadin ya basu mamaki ga kuma makullan ko wanne d’aki a rataye ,basuyi wata wata ba suka bud’e wannan k’ofar da suka tab’a jin maganganun Shalini ………..
Su Saleena suna shiga fadar mai martaba sarki Abdallah yayi musu tarba mai kyau cike da mamakin abunda ya kawo su a wannan lokacin ,bayan sun huta ne Sarki Haidar ya umarci magatakarda da ya maimaita abubuwan da ya fad’a wanda ya sani ,su Ubaidah da Zulaikha kam basa nan sun fita yawon bud’e ido ,hakan ya sake bashi kwarin gwiwar zayyano wa sarki Abdallah duk abunda ya faru. Jikin sa na b’ari tun a zaunen da yake kafin kace me gumi ya karyo masa ,ya karb’i jakar ya duba ,asalin rubutun Sarauniya Shalini da ke ciki yaga abunda ta rubuta daban ne da wanda aka cika masa kunne da shi a chan baya, idanuwan sa cike da hawaye yace ” Kaicho na!! Na aikata babban kuskure a rayuwata da na yarda za zance marasa kan gado da suka d’aura ni a kai ,tsawon shekaru ashirin da wani abu Y’AY’ANA basuji d’umin jiki na ba,basu san dad’in rayuwa da iyaye ba ,basu kuma ji irin soyayya ta mahaifa ba tun bayan sun yi sati biyu kachal da zuwa duniya Nayi nadaman zama da wad’anda basa son ci gaba na a rayuwar su ,kuma nagode wa Allah da yasa Raheena na nan da ranta nasan zata yafe min amma bana tsammanin Ubaidah da Zulaikha zasu sake samun jin dad’in rayuwa har abada!!!” Yana kai wannan ya umarci wasu manya manyan masu gadin gurin da cewar “a je a taho da su Ubaidah tare da Mahir!” ………
Hannu tasa tana kare fuskar ta idanuwan ta ta kasa budewa wad’anda suka cika da hawaye domin irin rad’ad’in Hasken rana da take ji a idon ,kayan jikinta duk sun zama tsumma mayafin da Nawaz ya rufe fuskar shi ,shi yasa ya rufe mata jiki fatar ta duk ta yank’wane sai uban suma da ya sake tsayi har gadon bayan ta wanda don wahala babu irin bunu da yayi da babu a wannan kan ,babu abunda take yi sai gafi ,tunda cikin fitsari da ba bahaya take kullum nan ne kwanciyar ta ,cinta, Shanta, har ta manta a duniya me wanka yake nufi duk gab’ob’in ta rawa suke yi babu kwari gashi tayi bak’i sitik kai kace ba Shalini tsatson indiya ba, baba Nasir ne biye da ita shima Nawaf ya rik’e shi domin babu k’arfi jikin sa, suna tafe a hankali mutanen gari suna bin su da kallo har suka isa fada, a nan ne idonta ya d’an fara daidaitawa ta fara ganin Abdallah dishi dishi ,gaba d’aya hankalin shi ya tashi ganin wanda aka ajiye gaban sa a matsayin Raheenar sa jiki na b’ari ya sa hannu duk biyu ya tallafo fuskar ta da hannayen shi duka biyu sai faman rok’on ta yafiya yake yi ,kuka suke yi mai tsuma zuciya ,ita Raheena ta san bashida laifi ,shanyeshi kawai akayi amma na don haka ba da haka bata faru ba, itama wautar da ta tafka shine na yanke hukunci da tayi da kanta ta bar gidan ,haka ya sake dulmiyar da ita cikin laifi da akace ta aikata ,domin da ta samu sarki da haka bata faru har ya kai ga zartar da wannan hukuncin

YOU ARE READING
GUGUWAR HAMADA
AdventureLabari na Sarauta, yaƙi, cin amana da labari ne da ya ƙunshi soyayya, tausayi da ban dariya......