Cikin sauri ta mik’e tsaye kamar yadda suka yi jiya bata tanka masa ba shima haka sai kallon juna da suka tsaya yi ,ya zaro abun share fuska ya mik’a mata ,babu musu ta karb’a ta share hawayen fuskan ta kafin ta bud’e ido ya juya ya tafi, wani dad’i ne ya ziyarci zuciyarta a take ta jingina a jikin wani bishiya da ke kusa da ita,ta kai mintina a haka ba tare da ta bud’e idanuwan ta da ta lumshe ba sai da ta gaji don kanta ta d’auki kwandon da zata yi siyayyar ta wuce hanyar kasuwan ,ta gama kwasan abunda zata kwasa ta wuce gida abunta ranta fal farin ciki……………
“Baba don Allah muje mana ,bikin sarakuna fa za’ayi a k’asar Ramali kasan ina so inje ko dan naga wannan gimbiyar da maza suke rubibi a kanta ina nufin Gimbiya Saleena yar gidan Sarauniya Jaseena mai mulkin Ramali” dariya kawai baba Nasir yayi ya mik’a masa takobin da ya k’era don ya kaifa shi ,shima da yaga yayi bai sake tanka masa ba akan zancen.
Bayan sati biyu…….
Nawaf na Kwance kan gadon shi na karare yayi rigingine tun safe bai kula baban Nashi ba. Baban ya shigo fuskar shi da fara’a yace ” ka shirya Muma zamu je kallon bikin da za’a yi a Birnin Ramali na sarakuna kaga kuma tafiya ce ta kwana uku cir don haka sai mu tafi tun yau” tsalle Nawaf yayi ya sauk’o daga gadon nashi ya rungume baba Nasir ” bari in sanar da su Ja’afar suma zasu je kaga Mun hadu mu da yawa kenan ko?” Baba Nasir yayi murmushi yace “toh yi maza kace su shirya” hakan kuwa akayi Ja’afar ne kad’ai zai je sauran biyun sun ce basa zuwa saboda haka suka kama hanya su uku zuwa Ramali……….
“Nawaz ya kamata ka fito kasan fa tafiyar da d’an rata zai d’auke mu kwana biyu kafin mu isa ,komai an had’a amma ka kasa shiryawa ka fito” tana k’arasawa ya fito yana murmushi duk kowa ya hau dokin shi aka fara tafiya amma shi yana chan baya ,sai hira yake da ASAD (Asad shine zakin nan wanda ya rikid’e daga guguwar hamada) babu wanda yake kallon Asad se Nawaz shi kad’ai ma in yana d’aki wataran ka jishi yana ta dariya ,ko kuma maganganu, tun abun yana damun iyayen nashi har ya zama musu jiki don sunga bazai daina ba ,wataran ma in sun ji shiru sai su tambaye shi ” yau Asad bai zo bane?”. Wannan kenan…………..
Birnin Ramali!!
Sarakuna da iyalan su ne daban daban suka iso k’asar Ramali daga cikin su kuwa sun had’a da ,Sarki Abdallah da matan sa Ubaidah da Zulaikha, sarki Abdoul-Rahman da Sarauniya Ruqaiyah ,sarkin Kalahari Rizwan d’an sarki Jalalud-deen (daga littafin JASEENA) da matarsa Sarauniya Meenah, da dai sauran sarakuna da attajirai na wannan lokacin. Dukanin su sun samu karb’uwa an basu masauk’i ,cikin attajiran kuwa sun had’a da Muhammad Ja’afar wato k’anin shi sarki Abdoul-Rahman!
Isowar su k’asar Ramali suka sauk’a a wata rumfa dake cikin kasuwar birnin nan suka yada zango domin dare yayi ,bikin kuwa za’a fara shi ne da hantsi, wanda ya had’a da wasanni irin na motsa jiki ma’ana (Olympic games a turance) wanda dama tun zamanin kaka da kakanni ya samo asali a k’asar Roma!! ” baba k’asar Ramali na da girma amma naji ance bata kai chan k’asar Kalahari girma ba domin kuwa Kalahari ance ta kai kwatankwacin masarautar Shimla ” murmushi Baba Nasir yayi yace ” wannan haka yake ,amma ai yanzu sarakunan biranen biyu wato Kalahari da Ramali sun d’auki riga da sun zamar da masarautun nasu kamar guda ko baka da tarihin GIMBIYA JASEENA y’ar sarki Hameed na Kalahari?” Ai tarihin wad’annan masarautu biyu suna k’unshe a cikin wannan littafi” murmushi kawai Nawaf yayi hannayen shi duka biyu a kuncin shi ,domin shi a rayuwar shi yana son duk wani abu da ya shafi sarauta kama daga tarihi har rayuwar su…….

VOCÊ ESTÁ LENDO
GUGUWAR HAMADA
AventuraLabari na Sarauta, yaƙi, cin amana da labari ne da ya ƙunshi soyayya, tausayi da ban dariya......