Babi na 6

1.1K 98 2
                                        

         Masarautar SHIMLA ta kasance masarauta a jerin masarautu ta farko da za’a a saka a jerin manyan masarautu masu  yawa tana da arzik’i maras adadi ga kuma kima da daraja da kuma d’aukaka! Hakan ya samo asali ne tun sarakunan baya da sukayi mulki ,mulki irin na adalci bisa tafarki na addini. A lokacin da aka nad’a sarki Abdallah sarautar wannan masarauta sarkin ya k’udiri niyyar yin abunda magabatan sa suka yi ,amma sai dai kash!! Ya had’u da mata marasa imani wad’anda duk yadda ya kai ga aikata alkhairi to sai sun yi kichin kichin sun hana ko ta wanne hali ne ,cewar su ” ai mu aka bawa sarauta ba’a ce mu zama almabazzarai ba kowa ya kawo kukan shi kace kai dole zaka nuna bajinta gaka kai adali ko?” Wani ikon Allah in suka yi makircin su ba wuya suke shanye masa zuciya. Hmm Ubaidah da Zulaikha kenan!!!

         Masarautar  SULTANPUR kuwa masarauta ce wanda tsakanin ta da masarautar SHIMLA Nisan tafiya ne na tsawon sati biyu cir a doki kenan in kuwa a rak’umi ne toh tabbas tafiyar ta wata guda ne ,sarki Abdoul-Rahman shine ke mulkin wannan masarautar matar shi guda d’aya ce mai suna Sarauniya Ruqaiyah Kyakkyawar gaske ce ga tausayi , matsalarta d’aya rashin haihuwa ,hakan ya jawo mata zagi iri iri daga gurin y’an uwan mijin wanda hakan yayi sanadiyyar rabuwar kawuna tsakanin sarki Abdoul-Rahman da d’an uwanshi wanda suke uwa d’aya uba d’aya mai suna Muhammad Ja’afar hakan ya saka Muhammad din ya tattara nashi ya bar wannan masarauta ya koma cikin gari da zama a cikin d’aya daga cikin manya manyan gidajen da suke da shi  wanda shima babu abunda ya rabashi da masarautar illa girma da fad’i, nan ya keb’e shi da matar shi  Sadiyyah da d’an su guda d’aya mai suna farouq.

      Wannan kenan……..

Bayan shekaru Ashirin

         Zaune yake a mak’erar sai faman dukan k’arfe yake da guduma rigar jikin shi wanda ruwan Zuma ne duk ya koma bak’i haka ma farar fuskar shi duk ya goga mata bak’in yana zaune ya mik’e k’afa guda dayan kima ya nad’e ta. Ji yayi ana k’iran sa daga nesa ” Nawaf! Nawaf!!! Nawaaaaf!!! Da hanzarin shi ya fito yana gyara zaman sauk’ar wuyan shi ma’ana yana cusata cikin riga sannan ya amsa , wasu maza su uku suna tsaye wad’anda basu wuce Shekarun sa ba suka k’araso inda yake suma de duk kayan nasu Sam ma kal!! “Ya naga baka shirya ba? Kana so mu makara ne? Kasan fa shiga SHIMLA cikin dare babu dad’i me zai hana mu kama hanya yanzu ?” Daya daga cikin su  (Jabeer) ne yayi Wannan maganar murmushi kawai Nawaf yayi yace “toh ku jira ni bari na yi sallama da baba tukunna ,don na riga na kammala shiri na” babu musu suka ja gefe don su jira shi.

      Yana shiga d’akin da suke k’irar ya hango baban nashi yana ta faman narka k’arfe  ya sa hannu ya d’auki wani tsinke zai soka mishi, kamar mai ido ta baya Nasir yayi wuf ya chafke hannun Nawaf suka fara wasa kamar kokawa saida sukayi mai Isarsu kowa yana haki ,sannan Nasir yace “na fad’a maka ai har yanzu baka isa ka kayar da ni ba ” shima Nawaf cikin dariya yace Hahaha!! Ka dai dena cika baki na bar ka ne don naga ka wani tsofe kawai! Amma ba don haka ba da sai na kada ka har k’asa !!” Yana yi yana duban damtsen shi. Baba Nasir yayi murmushi yace ” D’ana !! Sau nawa zan gaya maka cewa shi k’arfi ba a damtse yake ba? A zuciya yake da kuma kwakwalwa ” Nawaf ya d’an Sosa ‘keya yace ” toh baba mu Mun shirya zamu tafi Shimla sai Mun juyo ” Baba Nasir ya dubeshi yace ” d’ana nasan ka da rigima ,ka kula da kanka kada Kaje inda ba’a kaika ba!” Murmushi kawai Nawaf yayi domin in da sabo ya saba kullum sai an masa wannan kashedin. Ya fice ba tare da ya ce ‘kala ba cikin zuciyar shi kuwa cewa yayi ” Baba kana ina zan shiga gari ai babbar masarauta ce sai na zagaya !”

GUGUWAR HAMADATempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang