Babi na 5

1.1K 100 0
                                        

         Da gudunta matar ta k’arasa inda yake wasu ciyawi sun tokare shi hakan ya hana ruwan ci gaba da tafiya da shi, cikin fuska irin na tausayi da kuma nuna tsananin k’auna ga wannan jariri ta saka hannu ta d’auke shi ta rungume bata tsaya wata wata ba ta nufi hanyar fita daga lambun yayinda rigarta na alfarma yake share hanya daga baya. Tana isowa fada ta nufi gurin sarki shima da ya ganta ya mik’e tsaye fuskar shi da fara’a sannan kuma da alamar tambaya, ” ran ka shi dad’e mai martaba adalin sarki!” Kirarin da tayi masa kenan yayinda shima ya k’araso inda take yace ” Mu dad’e tare Sarauniya kyakkyawa ,mai adalci! Yau me kika samo mana ne haka naga kina ta murmushi mara adadi? ” mik’a masa jaririn tayi sannan tace ” a bakin ruwan lambu na sameshi , daga gani tafiyar da yayi mai nisa ce Allah ya baka nasara tunda na samu Wannan Yaron nake ji a jikina kamar adduar mu ce aka amsa mana ,Allah ya bamu d’a bayan wasu lokuta masu tsawo da muka d’auka na hak’uri da juna akan Wannan jarrabawan da Allah ya d’aura mu a kai! Ni ina matuk’ar k’aunar Wannan Yaron har cikin raina ,kana ganin zamu iya ajiyeshi a matsayin d’an mu ?” Sarkin yayi murmushi ya shafa fuskar ta da duk hannayen shi ” me zai hana ne? Nima kaina da ko mintina masu tsayi bai yi a hannu na ba na kamu da k’aunar shi ballantana kuma ke!! Kar ki damu Yaron nan zai iya zama tare da mu!” Wani murmushin jin dad’i tayi karaf d’aya idon ta ya kai ga tafin hannun jaririn taga an yi rubutu kamar tsagun aska an rubuta NAWAZ hakan ya tabbatar musu cewa wannan shine sunan Yaron , NAWAZ ! Sarauniya Ruqaiyah ta sake maimaita sunan fuskarta cike da murmushi yayinda sarki Anwar ya sumbaci Yaron a kumatu. A yini d’aya kachal sun zama kamar wasu mahaukata yadda suke nuna wa Yaron soyayya a take aka masa wanka aka bashi madara kafin kace wani abu har yayi bacci har dare sun kasa fita daga wannan d’akin…….

(K’ira a gareku mata marasa ganin darajar y’ay’a !!kar fa ku manta wani nema yake yi ko ta wanne irin hali bai samu ba , sai gashi Allah (S.W. T ) ya zab’e ku ya baku ,aikin ku ne ku kula da wannan Amanar da Allah ya baku , ko da kuwa ba naki na cikin ki bane Allah ya tsare mu daga aikata abunda bazai kaimu ga kyakkyawan k’arshe ba! Ameen.)………

            Wani k’aramin k’auye ya iso ga uban rana gashi babu wanda ya sani ,k’auyen ba wani nisa tsakanin shi da masarautar SHIMLA amma Nasir ya tabbatar a wannan k’auyen ma kad’ai zai iya rainon Nawaf kuma ya kula da shi ya kuma d’aura shi a kan tafarki madaidaiciya! Tafiya yake yana k’are ma ko ina kallo, da ‘kyar ya samu ya sayar da wannan gwala-gwalan yayi sa’a kuwa aka siya a kan farashi mai kyau wanda ya tabbatar in kana da wannan babu abunda zai hanaka siyan gida da kuma kama wata Sana’a. Hakan yayi mishi dad’i a rai ya sake rungume Nawaf wanda da ya gaji ko kukan baya iya yi ma sai baccin dole da ya kwashe shi. Wannan k’auyen da ya sauk’a a ciki ba wani bane illa k’auyen DUSHA k’auye ne wanda ba wani girma gareshi ba sai dai kuma mutanen garin akwai su da zuciyar nema ,duk wata Sana’a babu wanda basu yi , kama daga k’ira ,sassak’a ,noma dadai sauran su babu ruwan wani da wani ,su dai abunda suka sani shine su tanadi abun kai wa baka da kuma na sutura ko wanne sati kuwa sukan shiga birnin Shimla domin sayar da kayayyakin su a kasuwannin garin………

GUGUWAR HAMADADonde viven las historias. Descúbrelo ahora