Nawaz gaba d’aya tunanin shi ya dagule ” ashe dama zancen farouq gaskiya ne? Toh idan ni ba d’an ku bane waye ni ,daga ina nake kuma su waye asalin iyaye na??” Duk lokaci guda ya runtumo wad’annan tambayoyi. Murmushi Sarauniya Ruqaiyah tayi mai cike da takaici yau zata fad’i abunda ta dad’e tana b’oyewa domin wannan Yaron da ya riga ya zama tamkar jinin ta ya zauna tare dasu har abada, ” Tabbas babu d’aya daga cikin tambayoyin da kayi min da zan iya baka amsar su ,Nawaz ban san ko d’aya daga tambayoyin da kayi ba kuma ban yi tunanin zan san su ba ,abunda na sani guda d’aya ne tak wannan bai wuce samunka da mukayi cikin lambu ba a bakin ruwa sai rabza kuka kake yi ,tun kana jariri da bai wuce sati biyu ba da haihuwa, k’aunar ka ne da kuma tsananin Tausayin ka yasa ni d’aukan ka a matsayin d’an da muka Haifa ,kasantuwar bamu tab’a samun haihuwa ba nida mijina,haka zalika Mun yi iyakar bakin k’ok’arin mu don ganin baka tozarta ba kuma hakan ne ya faru ,sai daga b’angare d’aya tak! Aka samu matsala wanda wannan b’angare sun kasance sune manyan mak’iyan mijina da duk abunda ya mallaka. D’ana bazan hanaka yanke duk wani hukunci da kayi niyyar yankewa ba ,amma inason ka sani har in koma ga Allah babu wani mahalukin da zai ce kai ba d’ana bane in barshi lafiya ,kai d’an mu ne Nawaz kuma duk abunda ke cikin wannan masarauta taka ce! Amma ina rok’on ka abu guda d’aya tak! Ko da ka samu asalin iyayen ka don Allah ka ci gaba da kirana da mahaifiyar ka wannan kad’ai zaka min na samu nutsuwa.” Umma kar ki damu ,bazan tab’a daina k’aunar ki ba kuma in Allah ya yarda zan ci gaba da kallonku a matsayin mahaifa na na asali domin kun yi min abunda nawa iyayen suka gaza duk da ma ban san dalili ba” rungume shi sukayi dukan su kowa na hawaye cikin zuciyar su kuwa kowa da abunda yake sak’a wa…..
Kwanan su uku cir suka iso birnin Ramali ,nan suka nemi ganawa da Sarauniya Jaseena, ba tare da b’ata lokaci ba Sarauniya mai adalci ta bada daman ayi musu iso fada su kuma yaran da sauran wad’anda suka jikkata aka basu masauk’i, kayan sawa da kuma abinci.
Zaune take kan wata kujera gefen ta Sarauniya jaseena ce wanda tayi shiru wajen kimanin mintina hud’u kenan bata ce komai ba bayan ta saurari jawabin su Nawaf, Gimbiya Saleena kenan sanye da jar doguwar riga mai ratsin zinare ta yi kyau sosai ,Nawaf kawai take kallo tabbas ta gane shi sosai suna had’a ido ta kau da kai tana murmushi itadai wannan bak’in daud’a da ke fuskar shi ita ke bata dariya ba kad’an ba.” Babu wani matsala koda ban d’auki wani mataki domin musguna muku da aka yi ba zan d’auka don rayukan da aka hallaka, wannan yana d’aya daga cikin d’abiun azzaluman sarakuna ,amma zan yi mamaki ,koko ince nayi mamaki yadda sarki Abdallah zai bari haka ta faru domin mutum ne Marar matsala gashi kuma kamili mai adalci ,ban san me ya faru ba”. Nawaf ya yi wa Sarauniya Jaseena godiya da irin tarbar da tayi musu. Murmushi tayi ta dubi Saleena da ke ta faman murmushi ta k’ura wa Nawaf ido kawai ta girgiza kai ta fice tana dariya, jin motsin ta ne yasa Saleena ma ta mik’e har ta kusa tuntube duk wannan kallo fa a bak’in fuskar Nawaf take yi wa ,shi kuwa gogan naka ya zata ya burge ne sai dad’a fad’ad’a murmushin sa yake yi…………….

YOU ARE READING
GUGUWAR HAMADA
AdventureLabari na Sarauta, yaƙi, cin amana da labari ne da ya ƙunshi soyayya, tausayi da ban dariya......