GUGUWAR HAMADA da ta tafi da Nawaz bata zame ko ina ba sai bakin wani tafkeken kogi ,Nawaz na kuka kamar ranshi zai fita ga matsananciyar yunwa gashi kuma jariri ne d’anye, kamar kifta ido guguwar ta rikid’e ta dawo siffar zaki mai girman gaske ga uban gashi ,ya nannand’e Nawaz cikin zanen da yake sannan ya d’aura a saman ruwan ,abun mamaki Yaron bai lume cikin ruwan ba sai ma yabi hanyar da ruwan yake bi………..
Sarki Abdallah na zaune kan katafariyar kujerar shi na mulki shi kad’ai a fada sai tuno maganganun da suka faru yake yi duk ya birkice zuciyar shi na tafarfasa ,kofin azurfa ne a gaban shi ya yi firo da shi ya fad’i k’asa. Ubaidah da Zulaikha ne ke tahowa ,suna jin wannan ‘karar suka rugo cikin sigar munafukai suna lallashin shi “Haba ranka shi dad’e! Har yanzu kana so ka cemin ka saka ranka a tunanin wancan figaggiyar munafukar?” Ubaidah kenan wanda ta fi kowa sanin salo salo irin na munafurci!! Kafin sarki ya bata amsa ji sukayi an hankad’o k’ofa kawai ganin mutum sukayi zube a tsakiyar fada duk a galabaice jiki babu kwari Raheena wato (Shalini kenan domin a fada Raheena suke kiranta da shi Shalini sunan yare ne ) ta d’ago kai tana duban su d’aya bayan d’aya ta sani cewa yanzu kam sun riga da sun kwashe duk wani martaba da take da shi a idon sarki Abdallah ,ba tare da ya dubi inda take ba ya ce ” ku jefa matsoraciyar a kurkuku ita da ganin Hasken rana kuma sun yi bankwana!!:oops: kar in ji ance wani ya je ganin ta domin kuwa a yanzu bana mata kallon wani abu face dodanniya, Ashe ke macijiya ce ban sani ba kina ta Sara ta !! Shalini ashe kyaun d’an maciji ne da ke!! Yadda kika tozarta ni kema haka zaki gama rayuwar ki cikin tozarta Raheena!!” Cikin tsananin kuka mai rikitar wa Raheena tace “A’a ranka shi dad’e ya kamata ka saurare ni ! Ka yarda ni bazan tab’a cutar ka ba !! Ni masoyiyar ka ce ta hak’ik’a kum……….kafin ta k’arasa ya dakawa fadawan shi tsawa yace ” Wai me kuke jira ne!!! Ku fitamin da wannan k’azantacciyar abun daga gabana kuma kamar yadda na fad’a muku ! Ba ita babu kallon Hasken rana har abada!! ”
Kafin ka ce me har sun fice da ita daga fada inda aka kaita wani k’ask’antaccen kurkuku mai duhun gaske wanda ko abinci in an turo mata sai tayi lalume tukunna take samu ,ruwa kuwa sau d’aya ake samu a rana tafin hannu ma baya ganuwa a cikin wannan d’akin.
Kukan yaro da ta jiyo daga wani ‘bangaren lambun yasa ta mik’e cikin hanzari baiwar da ke b’are mata ayaba ma ta mik’e tana cewa “Allah ya baki nasara anya kuwa kunnen ki ya jiye miki Abunda nake ji yanzu haka?” Matar da ta mik’e d’in wanda da ka ganta kaga jinin sarauta ta ce ” kamar kukan jariri nake ji ” su biyun suka d’unguma suka nufi hanyar da suke jin k’arar……….
![](https://img.wattpad.com/cover/170773322-288-k47562.jpg)
ESTÁS LEYENDO
GUGUWAR HAMADA
AventuraLabari na Sarauta, yaƙi, cin amana da labari ne da ya ƙunshi soyayya, tausayi da ban dariya......