Kowa yana harkokin gabanshi babu wani tashin hankali kawai su Mahir suka fara cinna ma bukkokin su wuta hakan yasa mazan da matan kowa ya fito wasu sun rasa hanyar Fitowan ma wasu y’ay’an su na ciki ga wuta yana ci ,gari ya rud’e kowa sai gudu ,su kuwa su Mahir duk wanda suka gani sai su fille masa kai ko kuma su soke shi da wuk’a ,wad’anda suka rage d’in kuma suka tarasu guri d’aya ciki harda baba Nasir wanda tun zuwan su ya gane fuskar Mahir wanda bazai tab’a mantawa ba,saidai shi Mahir bai gane shi ba sanadiyyar sumar da ta lullub’e masa fuska.
” ko ku fito da Yaron ku guda d’aya tak! Nawaf ko kuma mu hallaka ku baki daya kuma babu wanda zai rayu !! Ina yake nace??!!” Duk mutanen jiki na rawa suka amsa da” bamu sani ba ” wani mugun dariya ya bushe da shi ya ratsa cikin mutanen yana nazarin fuskokin su. Nasir bai ankara ba yaji an chafko shi anyi wurgi da shi ” abokina nasan zakayi zaton bazan gane ka ba ko?” Ya sake k’afa da Nasir yace ” ina wannan matsiyacin Yaron!!! ?” Nasir bai yi magana ba illa miyau da ya tofa wa Mahir a fuska abun ya bawa Mahir haushi ya sake mangare shi har saida bakin shi ya fashe haka suka d’aure shi kamar wani kaya suka haye dawakan su suna ta janshi cikin zafin rana ga k’ishi har suka koma SHIMLA.A birkice Nawaf da Nawaz suka shigo k’auyen nasu ,babu komai sai k’onannun bukkokin da kuma matattun mutane wad’anda suka rage basu wuce su ashirin ba Galibi ma yara ne wad’anda aka kashe iyayen su, jaririya guda d’aya ce dake ta faman zabga kuka hakan yasa Nawaf ya nufi inda take domin kula da ita ,gaba d’aya ya kasa tunanin komai yaran ma da sauran mutanen suka nufoshi gami da rungume shi domin dama chan sun d’auke shi kamar wani jigo ne a rayuwar su tabbas yau ya fahimci hakan. Nan suka kwashe labarin abunda ya faru daga farko har karshe suka sanar da shi ,Jabeer kam tuni ya sare ma ganin yadda komai ya ruguje cikin rana d’aya tak! Nawaf kuwa ya d’auki laifin a kansa “saboda ni ne haka ta faru!” Abunda ya fad’a kenan har ya kai gwiwar sa ‘kasa, Jabeer ne ya dafa kafad’ar sa yace ” kar kace haka abokina ,duk abunda ya faru kaddara ce an riga an rubuta shi dole sai ya faru saboda haka yanzu tunanin abin yi ,ma’ana mafita zamuyi tun kafin dare yay mana in ba haka ba zasu iya cutar da sauran mu domin na tabbata zasu dawo saboda haka mu tattara abunda ya rage mana mu bar wannan gurin ,wata’kila ma samu taimako daga guri Sarauniya mai adalci ina nufin Sarauniya JASEENA y’ar sarki Hameed!! ”
Nawaf ya dubeshi yace “toh in Mun tafi kuma baba na fa? Na tabbatar zai yi tsammanin zuwana domin kuwa bai haifi lalataccen namiji ba ,kudai ku tafi birnin Ramali ni zan koma SHIMLA” Jabeer yayi Jim yace ” kar fa ka manta sarkin yawa ya fi sarkin k’arfi dole ka biyo mu Ramali nasan Sarauniya Jaseena zata karb’a mana y’anci ! ” ba musu ya tashi suka fara had’a abubuwan da zasu iya suka saka yaran a keken doki me rumfa da kayayyakin abinci da zasu buk’ata sauran manyan kuma suka hau dawakai suka yi haramar Ramali…………
“Nawaz na fad’a maka kai d’an mu ne ko baka sane da cewa akwai rashin jituwa tsakanin iyayen farouq da mu ne ? Ai shi yasa zai dinga yi maka wad’annan kalaman don de kawai ranka yayi bak’i ne!” Maganar da Sarauniya Ruqaiyah ta fad’a kenan wanda hakan yayi daidai da shigowar sarki Abdoul-Rahman.” Kar ki b’ata wa kanki lokaci ya Ruqaiyah! Gaskiya ne tayi lokacin ta kar fa ki manta magana ko a rami ka yi ka binne wataran sai an ji ,yanzu babu wani batun ‘boye ‘boye domin kuwa in Mun yi mishi haka kamar bamu masa adalci bane ,a misali in duk Mun fad’i matattu a nan ina zai sa kansa ,gashi Mun ‘boye masa gaskiya ko shi wanene Ruqaiyah ina so ki fahimce ni sosai ‘boye masa gaskiya bata da wani amfani a garemu domin kuwa ko an sanar dashi ko ba’a sanar da shi ba akwai kundin tarihi na wannan masarauta wanda babu abunda aka ‘boye a ciki

YOU ARE READING
GUGUWAR HAMADA
AdventureLabari na Sarauta, yaƙi, cin amana da labari ne da ya ƙunshi soyayya, tausayi da ban dariya......