Da gudu Nawaf ya koma masauk’in su, zubewa yayi a gaban Baba Nasir yana Haki ,cike da mamakin yanayin da yaga d’an nasa a ciki wanda bai tab’a gani ba yasa ya yi saurin mik’e wa zaune yace” me ya faru ne d’ana?? Me ya sameka?ko kayo tsokanan naka da ka saba?” Duk a tare yayi wannan tambayoyin , Nawaf bai iya cewa komai ma sai girgiza kai da yayi alamar A’a, sai da ya samu nutsuwa sannan yace ” Baba ashe de da gaske ne mutum na da mai kama da shi a duniya ? Yau naga wani ,baba kamar mu har ta b’aci sosai ,kuma har wannan rubutun yana da shi a hannun shi ,kasan me baba? Nikam tsoro naji domin kuwa nayi zaton gamo nayi da wani shed’anin aljanni yayi siffata”. Baba Nasir na jin wannan zancen ya mik’e a firgice yace ” Nawaf a ina ka ganshi!! Tashi muje inda yake!!!!!”. Bai ma jira me Nawaf zai ce ba ya fice da wuri ,ganin haka yasa Nawaf ya bi bayanshi babu abunda yake yi Illah tambayar kansa ko meyasa baban nashi ya rikice haka?. Nasir yayi duban duniya bai ga wanda d’an nasa ya k’ira da mai kama da shi ba tuni ya nemi guri ya zube a k’asa ya ciro d’ayan b’arin sark’ar da zai bawa Nawaz yana kallonta yace ” Sarauniya Raheena (Shalini) na miki alk’awari in de naga Nawaz zan had’a shi da d’an uwanshi Nawaz ko ta wanne hali ne in Allah ya yarda !!!” Yana kai wannan ya goge hawayen fuskar shi ,a d’ayan ‘bangaren kuwa zuciyar Nawaf cike take da tambayoyi marasa adadi …………
” Umma gaskiya nake fad’a miki ,kamar mu d’aya ya kamata mu nemeshi kafin mu tafi amma kin k’i kulani ,umma na rok’eki don Allah ” wani kallo Sarauniya Ruqaiyah ta watsa mishi ,irin wannan kallon idan ya gani yasan ranta ya b’aci don haka ya fice daga d’akin ba tare da ya furta komai ba ,itama bata so hakan ba don bata son ko dai dai da rana d’aya ta b’ata mishi rai ta kasa dena mamakin yadda yazo mata da magana ta share shi domin babu abunda zai nema bata yi mishi ba indai bai fi k’arfin ta ba! Duk Wannan abun a gaban Sarki Abdoul-Rahman aka yi ,shima kasa furta kalma d’aya yayi domin a tunanin shi hakan zai iya jawo rabuwar su da d’an nasu k’waya d’aya tak!!
B’angaren Nawaf ma de haka ne domin Nasir ya ‘boye masa komai game da wannan Nawaz d’in da yake magana a kai kuma ya umarce shi da su shirya su kama hanya , b’angaren Nawaz kuwa kasancewar shi mai sauk’in kai bai nuna damuwa a fuskar shi ba ,a cewar shi in ma da akwai b’oyayyen alamari zai fito da kanshi .

ESTÁS LEYENDO
GUGUWAR HAMADA
AventuraLabari na Sarauta, yaƙi, cin amana da labari ne da ya ƙunshi soyayya, tausayi da ban dariya......