❄️❄️❄️❄️❄️❄️
*Ḧ̤Ï̤B̤̈B̤̈Ä̤T̤̈Ṳ̈L̤̈L̤̈Ä̤Ḧ̤*
❄️❄️❄️❄️❄️❄️*°•(ĸyaυтa daga Aℓℓαн)•°*
*°ιиιqυιту,ємραтну,нυмιℓιαтισи & яσмαитι¢ ℓσνє💑°**MALLAKAR:HAFSAT HAFNAN💕*
*WATPADD:HAFNANCY*
*•ѕadaυĸarwa ga Dr.υмαя fαяυq вαнαgσ,ємιя σf иιgєя ѕтαтє,мιииα•*
*°•ιnтellιgenт wrιтerѕ aѕѕo🖊•°*
___________________________________💥
*Թɑցҽ 9⃣*
Acan fada kuwa,rigima ce ko kuwa nace cin musu ce ta kaure sosai tsakanin Faruq da Hayat,shi Hayat cewa yayi sai Faruq din ya gaya masa hadisi ko kuma ya kawo masa ayar da akace nemar mace kamar Najmiy child abuse ne,shi kuwa Faruq ya kuke sai masa bayani yake akan tsarin bayahude.
Mai martaba wanda keta sauraransu tun dazu ne ya doka musu wani uban tsawa,yace"Ku min shiru mutanen banza da wofi,kunbi kun cika min kunne da shashancinku na banza.... "
Ya dubi Hayat yace"Kai kuma Hayat ko kadan banji dadin furucinka dakace wai Najmiy bata da asali ba,haqiqa kayi daƙiƙanci anan,toh ina son ka sani cewar ni awurina kallon 'yar cikina nake mata,Najmiy tana da cikakkiyar asali,kuma zan tsaya kan tsayin daka koda kuwa kowa ya gujeta ne,toh ni zanyi kokari naga na zame mata gatanta wanda zatayi alfahari dashi fid-dunya-walakhira,kuma koda wasa ka sake ka sake maimaita wannan kalmar,toh wallahi sai nayi mugun sassab'a maka,da fatar kaji abinda na fada?"
Cike da nadama Hayat yace"Eh duk naji abinda ka fada Abba mai martaba,don Allah ka gafarceni subutar baki ne... "
**
Haj.Karama kuwa tana fitowa ta aiki wani dogari da yaje ya k'irawo mata Hayat ah inda Najmiy tace yake,da sauri dogarin ya zub'e agabanta yace"Ranki shi dade,Yarima Karami yana fada.... "Bata bari ta k'arashe jin zancensa ba ta nufi hanyar fadar,har ƙuyangu sun soma take mata baya sai kuma tayi saurin dakatar dasu.Tana shiga cikin fadar kuwa ta hango Hayat durƙushe gaban mai martaba yana kara rokansa akan yayi haquri ya bashi auran Najmiy,shima Faruq din ya saka baki don bai tab'a tunanin hakan ne zai kasance ba da kuwa bai kawo kararsa ba,shi kansa bai san dalilin daya sanya mahaifin nasu yace bazai baiwa Hayat auren Najmiy ba,shifa kawai yazo ne yace masa ya kirawo Hayat ya masa fada kan ya fita hanyar Najmiy don bata kai matsayin da har zata tsaya tayi soyayya ba ayanxu,ya bari sai ta dan kara wayau da kuma girma,sai kuma gashi mahaifinsu yace kwata kwata ma wai bazai bashi auranta ba.
Babu b'ata lokaci ta isa ga Hayat fuskarta babu ko digon annuri akansa,dagoshi tayi ta mikar dashi tsaye,shi kuwa mutumin naku yana hada idanuwa da ita,ya soma sakin murmushin jindadi,don atunaninsa itama zancen ya isketa ne shine tazo ta tayashi roƙan mai martaba akan yayi haquri ya bashi Najmiy.
Babu zato babu tsammani kawai Hayat yaji saukar wani lafiyayyan mari saman kuncinsa,bai gama shanye mamakinsa ba kuma yaji saukar wani adayan gefen kuncinsa,har ta daga hannu zata k'ara masa wani,sai kawai taji an rike mata hannun,Faruq ne,Yace"Haba Haj.karama meh kuma yayi zafi haka da har yakai ga mari?"
"Cikan hannu... " shine kawai abinda ta iya furtawa da k'arfi,da sauri Faruq yayi kamar yadda ta bukata tare da jaa da baya da sauri sabida irin tsantsar bala'in daya hango shimfid'e acikin ƙwayar idanuwanta.Juyawa tayi ga Hayat wanda tsananin mamakinta ma ya hanashi furta komai,nunashi tayi da 'yar yatsa tace"Don qaniyarka ni Maymunerh ni zaka janyowa abin ƙunya da kuma abin fada agari?ka rasa wacce zakace kanaso sai wacce ba'a san asalinta ba?toh wallahi da sakel,bada yawuna ba kuma ba'a cikin wannan masarautar ba,don haka maza ka gaggauta binne wannan zancen nadai gaya maka tun wuri don kada matakin da zan dauka agareka yazo bai maka dadi ba.... "
Har ta juya zata wuce,da sauri mai martaba yace"Maymunatu maza dawo nan.... " cak! ta tsaya ah inda take,sai data kwashi kusan daƙiƙu goma kafin ta juyo ta soma dawowa da baya zuwa gareshi.Rissinawa tayi har k'asa tace"Gani ranka ya dade... "
Zuba mata idanuwa mai martaba yayi ba tare da ya furta komai ba,sai girgiza kansa yake cike da tsananin mamakin jin furucin daya fito daga bakinta,gani yake kamar ba maymunarsa bace mace mai tsananin son mutane da daukar kowa nata ne,koda yake ai ba abin mamaki bane don dama can ance mutum tara yake bai gama cika goma ba,dama duk ƙyawun halayyarka tofa dole za'a samu wani b'angare naga mai muni.Toh ayau kuwa other side dinta Gimbiya Maymunerh ta gwada masa.
Gyaran muryarsa yayi daidai da shigowar Haj.Babba cikin fadar,shiru shiru taga haj.karama bata dawo ba shiyasa ta biyo sahunta.samun wuri tayi ta zauna ganin kamar magana muhimmiyace akeyi acikin fadar.
Yace"Maymunerh yanzu na gama yiwa danki fadar wannan furucin da kikayi,sai gashi kema kin maimaitashi,maymunerh yau meya shiga cikin kwakwalarki ne da har ya sanya kikayi irin wannan furucin?Ayau Najmiy ce ta zamo mara asali?azatona kin dauketa ne tamkar 'yar data fito daga cikin cikinki,ashe tunanina akan hakan ba gaskiya bane,tunda gashi ayau kin fito kin nuna min cewar baki haifi Najmiy ba,baki dauketa kamar yadda kika dauki Hayatu ba,Najmiyya bata da gata,haka kuma bata da cikakkiyar usulin da har zaki iya bari danki ya hada jini da ita,toh ina son kisha kuruminki,ni Muhammadu bazan ma taba baiwa Hayatu auren Najmiyya ba sabida ko kadan bai cancanci abashi ita ba,don haka ki rubuta ki ajje cewa nina fadi hakan,maza kowa ya tashi ya bani wuri.... "
Haka kowa ya tashi ya fice jiki ah sabule,bayan sun fita kuwa haj.babba ta hau yi mata fada akan meyasa zatayi irin wannan furucin?meya shiga cikin kwakwalwarta ne?
Ko kala bata ce mata ba tayi b'angarenta.shi kuwa Faruq so yake ya baiwa Hayat haquri amma ko kadan bai samu damar hakan ba.
***
*°•Ah gurguje pls•°*Mai martaba M.k bahago ya saka su dogarawa sanya ido sosai akan Hayat da Najmiy,har umarni ya bada akan cewa muddin aka ga sun keb'e toh ahukunta masa Hayat,don ya riga ya gargad'eshi akan kada ya kuskura ya sake keb'ancewa da ita,karatu ma yanzu idan har zasuyi tofa sanya dogarawa ake atsakaninsu,kwata-kwata babu maganar da take shiga tsakaninsu bayan na karatu.Hayat duk yabi ya rame ya kuma lalace,sam bashi da wani sukuni da walwala,kullum cikin kuka yake,gashi mahaifiyarsa ta juya masa baya don kawai yace yana son mara asali,Faruq ma tuni ya koma makaranta,haj.babba ce kawai take dan jansa ajiki sai kuma kannensa,itama tayi tayi da mai martaba akan ya gaya mata dalilinsa daya sanya yace bazai baiwa Hayat auran Najmiy ba amma fir! yaki don yasan zasuce ba wani dalili mai karfi bane,amma shi kadai yasan abinda yake hangowa nan gaba.itama Najmiy zuwa yanzu ta soma tausayin Hayat,gashi babu damar keb'ancewa dashi,kuma ita bata masan wainar da ake tauyawa ba acikin gidan,ko kadan bata san cewa mai martaba yace bazai taba baiwa Hayatun auranta bane,itafa duk wannan mutanen da aka sanya su dunga tsaronsu ita azatonta kawai bai dace suyi soyayya bane ashekarunsu,shiyasa aka sanya masu gadin da zasu dunga lura dasu aduk sanda suka k'ebance don karatu ko wani abin can daban.
_*jan нanĸalι na ғarĸo agareĸυ ιyayen yanzυ da ĸυмa ιyayen goвe,ĸυ daιna ѕanya dogon вυrι aranĸυ don вaĸυ ѕan мaι goвe zaтa нaιғar вa,gaѕнι yanzυ мaι мarтaвa мĸ yana neмar тaғĸa вaввan ĸυѕĸυre,da'ace yaвι ѕon zυcιyar danѕa ne da ĸυwa ĸoмaι dazaι ғarυ вaι ғarυ вa,waтaĸιla мa вayan aυre yana ιya canzawa тυnda нar yana ѕon najмιy dιn da gaѕĸe,aммa dogon вυrιn da yaĸe daѕнι aĸan ғaranтawa najмιy ѕнι ya нaιғar da ĸoмaι*_ мυje zυwa🏃
_*idan har na gamsu da comments toh kuwa kuna iya ganin update anjima kadan*_
*TAKU*
*ⓗⓐⓕⓝⓐⓝ💕*