37-39

947 37 1
                                    

❄️❄️❄️❄️❄️
*Ḧ̤Ï̤B̤̈B̤̈Ä̤T̤̈Ṳ̈L̤̈L̤̈Ä̤Ḧ̤*
❄️❄️❄️❄️❄️

*°•(ĸyaυтa daga Aℓℓαн)•°*

*°ιиιqυιту,ємραтну,нυмιℓιαтισи & яσмαитι¢ ℓσνє💑°*

*MALLAKAR:HAFSAT HAFNAN💕*

*WATTPAD:HAFNANCY*

https://m.facebook.com/Hafnans-Novell-246747739535534/

*•°ѕadaυĸarwa ga Dr. υмαя fαяυq вαнαgσ,ємιя σf иιgєя ѕтαтє мιииα•°*

*ιnтellιgenт wrιтer'ѕ aѕѕo✍*
https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/
___________________________________
💥

_*°•чαu rαnαr tαkucє mч lσvlч grαnd dαughtєr'ѕ mαmαn ummí,munαt,humαírα αnd zєєч,kαkuѕ dínku tαnα чínku σvєr mч kíѕhíчσчí😀•°*_

_*°Meemarttj Ina tayaki murnar fara sabon littafinki mai suna 'MATATACE',gal kip the ball rolling cuz littafin na bada ma'ana,Allah yasa yadda kika fara lafiya ki gama lafiya,amin°*_

*NOT EDITED🔨*

*Թɑցҽ 3⃣7⃣ Եօ 3⃣9⃣*

Tunani sosai ya shiga yi akan *'AISHATU FULANI'* wanda har nema yake ya tarwatsa masa ƙwaƙwalwa don ya kasa gane abinda take nufi da zancen wai ita ta manta wacece ita sannan kuma ta manta hanyar garinsu,anya wannan abin nata babu aikin sihiri aciki?

Tambayar da yaiwa kansa kenan,can ya furta afilli"God! pls Aisha allow my brain to rest,don Allah ki k'yaleni bana cikin mood na thinking ahalin yanxu,bana son na dami ƙwaƙwalwata da tunaninki pls....."

Adaidai lokacin kuma suka karaso k'ofar gida,jiya akai rasuwar amma sai ka rantse da cewa yau ne sabida yadda mutane keta shiga da fita ana kai gaisuwar ta'aziyya wanda Hayat ne ke karba sai kuma mutanen ita Haj.Hadizar.

Mutane na ganin shigowar motocin Mai martaba Umar Faruq sai kowa ya mimmike kowanne cike da tausayinsa karara akan fuska,shi kuwa Mai martaba ganin idon Jama'a ya sanya mutuwar dawo masa danya sharab,tuni xuciyarta ta hau tafasa da sauri da sauri ayayin da hawaye ya shiga kwaranyo masa saman kunci.

Wani Secret Security wanda kuka fi sani da 'SS' shine yayi saurin xuwa ya bud'e masa k'ofa tare da d'an duƙar da kai yace"Ranka shi dade bismillah kana iya fitowa,Allah ya kara haquri da kuma juriyar rashin da akayi....."

. "Amin ngd...." shine abinda ya fada bayan ya sanya hannu yadauke hawayen dake ta malala akan kuncinsa,sam bayason ya zamo ragon banza agaban kannensa,he hav to be strong for them,kukan daya jiyo Hayat na rusawa awaje kadai ya sanya jikinsa mugun sanyi.Sannu ahankali ya diro daga cikin motar,mutane sai xubewa ake akasa ana kwasar gaisuwar rashin da yayi tare da yiwa dansa Aryaan addu'ar samun lafiya cikin gaggawa.

Hayat ya taso da sauri ya rungumeshi tare da bud'e wani sabon shafin kuka,cikin ƙaryewar murya yace"Big brother yanxu shikenan itama Haj.Babba ta tafi ta barmu kenan acikin duniyar nan?sheranjiyan nan take cemin tafa sami lfy don haka na shirya acikin kwanakin nan zamuje duba jikin Aryaan,ashe dai warkewar ta tafiya ce ban sani ba?"

Ya sake rushewa da wani kukan wanda ba karamin tausayi ya baiwa jama'ar wurin ba,ya cigaba"Yanxu shikenan mun zamo marayun karfi da yaji kenan?yanzu bamu da wanda zai kwabemu idan muka aikata ba daidai ba?yanxu bamu da wanda zamu kalla mu kira su da iyayenmu?Big brother pls speak out......."

"Hayat babu maraya sai rago,sannan kuma nasan ayanxu ne zakasan muhimmancin iyaye tunda basu araye,ayanxu ne zaka soma nadamar kura-kuran daka aikata abaya,kai I don't have much to say,bani buta nayi alwala....." dake har an soma kiraye-kirayen sallar magrib.

HIBBATULLAH Where stories live. Discover now