️❄️❄️❄️❄️
*Ḧ̤Ï̤B̤̈B̤̈Ä̤T̤̈Ṳ̈L̤̈L̤̈Ä̤Ḧ̤*
❄️❄️❄️❄️❄️*°•(ĸyaυтa daga Aℓℓαн)•°*
*°ιиιqυιту,ємραтну,нυмιℓιαтισи & яσмαитι¢ ℓσνє💑°*
*MALLAKAR:HAFSAT HAFNAN💕*
*WATTPAD:HAFNANCY*
https://m.facebook.com/Hafnans-Novell-246747739535534/
*•°ѕadaυĸarwa ga Dr. υмαя fαяυq вαнαgσ,ємιя σf иιgєя ѕтαтє мιииα•°*
*ιnтellιgenт wrιтer'ѕ aѕѕo✍*
https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/____________________________________
💥
*°PAGE 53•_*°Wannan page din naku ne Janaf Novella ngd kwarai da gaske da yadda kuke nuna qaunarku kan wannan littafin°*_
*NOT EDITED❌*Awanninsu Mai martaba goma sha daya da mintuna talatin asararin samaniya kan su iso garin Mumbai.ah agogonmu na Nigeria misalin biyar saura suka isa ayayin da kuma agogon India ya nuna tara na dare suka isa sabida India is 4hours,30mins ahead of Nigeria.Dama already Dr.Bature ya aika da motarsa k'irar 'Rolls-Royce Phantom'
Acikin 20mins kacal suka iso Hiranandani hospital Mumbai.Ana ida parking ah harabar asibitin,mai martaba da amininsa mai girma gwamna Alh.Aminu Abbas sukayi hanzarin fitowa babu b'ata lokaci suka soma tattaki xuwa ward din da Aryaan yake,kai kace ko matching parade suke tsabar sauri.
Sannu ahankali mai martaba ya murda k'ofar dakin ayayin da xuciyarsa ta cika da farin cikin son ido biyu da d'an nasa.Fes! idanuwansa suka sauka kan gayyar mutanen dake dakin wa'enda suka saka Aryaan ah tsakiya,iyalen Dr.Bature ne dashi karan kansa Dr.Baturen sai kuma masu yiwa Gimbiya Najmiy hidima.Kallonsa ya tsayar kan Aryaan wanda Umman tasa ke zaune agabansa tana bashi ruwan shayi da kuma Rogan gosh abaki.Aryaan duk yabi ya rame tamk'ar mai ciwon sickler,idanuwa sun rage girma ba kamar bulb eyes din da aka sanshi dasu ba,Allah sarki ciwo kenan mai sauya halittar dan'adam.
Gabaki daya hankalin mutan dakin ya koma ga wa'enda suka shigo,cike da farin ciki Dr.Bature ya mike yana fadin"A'ah mutumina barka da isowa ya hanya?"
Mai martaba bai iya bashi amsa ba don gabaki daya hankalinsa naga Aryaan ne.Aryaan din shima Abbin nasa yake kallo,can ya saki kara tare da mikewa tsaye ya ture kofin shayin dake hannun uwar yana fadin"Abbiiiiiiii......"
Cikin k'aryewar murya mai martaba shima ya furta"Aryaan my son!ashe zaka mike?wallahi ada mun cire rai akan tashiwarka,sai gashi Allah ya karbi koke-kokenmu ya sanya ka tashi,come to me my son,maza zo gareni naji dumin jikin d'ana......"
Da gudu ya isa gareshi ya rungumeshi,alokaci gud'a suka fashe da kuka mai tsuma xuciya,babu wanda baiji tausayinsu ba acikin dakin.
Can Aryaan ya cikashi ya soma dube-duben bayan ubansa kamar dai yana neman wani abin,
Mai girma Gwamna Aminu yace"Son come to me...."
Da gudu ya isa ya rungumeshi,can ya cikashi ya dubi uban yace"Abbii ina uncle yake?
Yana nufin Hayat.
Murmushi uban yayi tare da duk'awa daidai tsawonsa yace"Uncle dinka mun barosa agida sabida jama'a amma bari na kirawo maka shi awaya kuyi magana kaji?
"Abbi yi maza ka kirashi nayi kewarsa,rannan yace idan na kara girma zai siya min keke,toh kaga ai na qara girman ko?
Murmusawa akai da shirmensa don da'ace yasan yakai shekara guda da dori kwance rai ahannun Allah toh kuwa da beyi wannan maganar ba.