Թɑցҽ 11

957 55 5
                                    


      ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
        *Ḧ̤Ï̤B̤̈B̤̈Ä̤T̤̈Ṳ̈L̤̈L̤̈Ä̤Ḧ̤*
           ❄️❄️❄️❄️❄️❄️

        *°•(ĸyaυтa daga Aℓℓαн)•°*
  
      *°ιиιqυιту,ємραтну,нυмιℓιαтισи & яσмαитι¢ ℓσνє💑°*

     *MALLAKAR:HAFSAT HAFNAN💕*

      *WATPADD:HAFNANCY*

_*°wannan page dιn мallaĸιnĸυ ne нιввaтυllaн ғanѕ groυp,janaғ ғanѕ groυp,yarιмa ѕυнaιl ғanѕ groυp & ιnтellιgenт wrιтer'ѕ ғanѕ groυp,нaqιqa coммenтѕ dιnĸυ yana ѕυмar danι,ιna ѕon ĸυ ѕanι cewar нaғnan тana мυĸυ тѕaғтaтaccιyar ѕoyayya,acιgaвa da gaѕнι ѕυya ѕaι ranar ѕallaн😉•°*_

  *°•ιnтellιgenт wrιтerѕ aѕѕo🖊•°*
____________________________________

                           💥

       *Թɑցҽ 1⃣1⃣*

Acan dakin horo kuwa,tuni aka isar da saƙon xuwar prince Hayat,akacewa malamin horo cewar ga Yarima Karami nan tafe ai ga laifin da mai martaba ya kamashi dumu-dumu yana aikatawa,malamin horo wato Idrisu duk yaji jikinsa ba dadi don tabbas Hayat mutuminsa ne,sosai suke dasawa da juna.Babu yadda ya iya illa mik'ewa ya dauki dorinarsa kakkaura mai baki biyu,ya shiga gyarata kafin zuwansa,don hukunci ya zama dole,don ma wai yana d'an sarki kenan shiyasa aka dan masa sassauci,wannan hukuncin da mai martaba m.k ya sanya ayiwa Hayat ba karamin dadi yayiwa mutane da yawa ba,don hakan da yayi shine daidai,ya kwatanta adalci,ya nunawa duniya cewa sam baya da son kai ko kadan,baiyi tunanin cewar ai Hayat dansa ne ba don haka bazai hukuntashi bisa laifin daya aikata ba,a'ah ya kwatanta adalci anan.

    Mamman dogari shine gaba gaba,ayayin da sauran hudun ke rik'e da Hayat,shifa Mamman sosai abin ke masa dadi,ji yake tamkar ya xuba ruwa ak'asa yasha don murnar ganin za'a hukunta Hayat (Kunsan haka abin yake,kowa zaka ga da wanda jininsa ya hadu da,haka zalika akwai wanda jininsa bai hadu dana wani ba,toh hakan take ga Prince Hayat da kuma Mamman dogari.)

  Suna shiga cikin dakin Jabir ya nufi Idrisu wanda ke tsaye yake jiran isowar Hayat.Sauran dogarawan kuwa ahankali suka zaunar da Hayat ak'asa wanda sai faman basu haquri yake tayi akan kada su bugeshi,abin dai gwanin ban tausayi.

    Jabir ne ya danyiwa sauran dogarawan clapping 👏 sau biyu,duk suka dubi inda yake ah kusa da Idrisu,yace"Duk ku matso kusa.... "

Da hanxari suka isa gareshi don shine oganninsu gabaki daya,He has the final saying kuma dolene subi duk abinda yace,idan har ya kafa wata doka toh kuwa babu dogarin dake tsallakewa koda kuwa kana jin kai din wani shegen ne irinsu Mamman tofa dole ka lafar don Jabir ko kadan baya daukar ƙaniya.

     Yace"Meh zai hana mu hade kawunanmu mu taimaki Yarima Karami?kowa anan yasan Yarima karima dai mutumin kirki ne kuma sosai yake k'yautata mu'amalarsa da mutane kamar dai mahaifinsa,shidai  abarshi da saurin fushi,mugun zuciyar tsiya wanda har hakan ke sanya ko kadan bashi da yafiya idan aka masa wani abin da ransa bai so ba,amma apart from dat,sam sam Yarima Karami bashi da matsala,kowa nasa ne,don haka abinda nakeso daku shine,kar abugeshi,mu dan bada lokaci sai awuce dashi Fada,sai yayi acting kamar an bugeshin,koya kuka ce?"

   Kowannensu ya gyad'a kai har Idrisu mai horo alamun amincewa,Cike da rashin jindadi Mamman yace"Amma dai kunsan Mai martaba yana iya gane cewar ba'a dakeshi bako?don haka nidai babu ruwana,haba ko bulala goma ne dai ayi masa gudun shiga cikin matsala..... "

HIBBATULLAH Where stories live. Discover now