❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️
*Ḧ̤Ï̤B̤̈B̤̈Ä̤T̤̈Ṳ̈L̤̈L̤̈Ä̤Ḧ̤*
❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️*°•(ĸyaυтa daga Aℓℓαн)•°*
*°ιиιqυιту,ємραтну,нυмιℓιαтισи & яσмαитι¢ ℓσνє💑°*
*MALLAKAR:HAFSAT HAFNAN💕*
*WATTPAD:HAFNANCY*
*°ѕα∂αυкαяωα gα Dr.υмαя fαяυq вαнαgσ,ємιя σf иιgєя ѕтαтє,мιииα°*
_*°•wannan page dιn naĸι ne ĸe daya мy najaтee мarυвυcιyar 'yarιмa ѕυнaιl',нaqιqa lιттaғιn na nιѕнadanтar daмυ,υвangιjι Allaн ya ĸara вaѕιra da kuma zaĸιn нand,ιna ѕo ĸι ѕanι cewar нaғnan dιnĸι тana мιĸι ѕan ѕo💕💕💕•°*_
*°•Intelligent writers Asso🖊•°*
__________________________________💥
*Թɑցҽ 1⃣0⃣*
_*вayan waтannι υĸυ*_
Zuwa yanzu Hayat ya soma fusata da gadin da ake musu,ba dama su zauna waje daya da Najmiy,sai gaka dogarawa nayiwa junansu signal alamun maza su matso kusa dasu,zancen soyayyar nan ne dai ba'a son suyita,shi yama fita harkan mahaifin nasa tunda harwa yau yaki sauraron maqigarsa(Mai martaba m.k Bahago wani irin mutum ne mai tsassauran ra'ayi,idan har yace haka yakeson abu,tofa babu wanda ya isa ya canza masa wannan tsarin,yana da kafiya akan abu sosai,Allah sarki duk fa akan baiwar Allah Najmiy yake kuntatawa dan cikinsa,don kawai ita ya faranta mata,ta samu tayi rayuwar farin ciki da kuma jindadi,(irinku sunyi karanci mai martaba m.k,Allah yaja da ran mutumin talakawa,amma ranka shi dade daka jaraba Hayat kila ya sauya halin saurin fushinsa dinnan da sauransu dai,dama ance sai kaga ta sanadin wani mutum ke canzawa daga wani halin da aka sanshi dashi.)
Haka ma mahaifiyarsa Haj.karama tace babu ruwanta dashi muddin bai fita ahanyar Najmiy ba.kannensa Abida da kuma Hidaya suma sun dan ja baya da Najmiy don aganinsu itace ke nemar tarwatsa family dinsu.zuwa yanzu Najmiy tasan wainar da ake toyawa wanda ko kadan bata ji dadin hakan ba,tausayin Hayat da take ji ya sanya har ta soma developing sonsa acikin xuciyarta,amma babu damar gaya masa,kuma ko ta gaya masan ma tasan mai martaba ba yadda zaiyi ba.
Shi kuwa Faruq koda ya koma makaranta ya kasa samun kwanciyar hankali,gashi alokacin wani da wani ne ke rik'e wayar salula balle yace zai k'ira Hayat ya sake nemar gafararsa ko zaa dace wannan karon ya sauraresa.Allah-Allah yake semester tayi ta kare ya dawo gida.Watarana Hayat da Najmiy suna bitar karatunsu as usual,gefen haqunsu da kuma damarsu masu gadinsu ne,bayan sun kare karatun,hayat ya dubesu yace"Wallahi yau fa sai dai ku min duk abinda zakumin amma agaskiya sai na gana da Najmiy.... "
Kan suyi magana ya kalli Najmiy yace _*"NAJMIYYA INA SONKI,SHIN KEMA KINA SONA?"*_
Kan tayi magana kawai yaji saukar dorina agadon bayansa,wani dogari ne wanda dama ya dade yana jin haushin Hayatu,yanzu gani yake its an opportunity ya koyawa Hayat hankali,Hayat bai damu ba,Hawaye cike fal da idanuwansa yace da d'an k'arfi"Najmiy kiyi magana karki ji tsoro,shin kema kina sona?"
Tuni Najmiy ta fashe da kuka ganin bulalar da aka sake tsula masa,wani dogari ne yayi mata alamu da ido wai ta tashi ta shige ciki,da sauri ta kwashi books dinta tayi ciki tana kuka.Hayat shima fashewa yayi da kuka mai tsuma xuciya bayan tafiyarta,ashe yanzu idan kace kana son wani ya zamo laifi?
Awannan ranar saida aka kaiwa mai martaba kararsa,ya kirashi ya tsassage masa yace ya fita aharkar Najmiy don ya riga da yayi mata miji ma amma bai fada masa cewar Faruq bane,ashe tun da dadewa suka kulla wannan zancen da sarkin kano,kan cewa Faruq zai baiwa auran Najmiy,toh shi ko kadan baya son canza magana arayuwarsa,shiyasa ya tsaya kan tsayin daka akan lallai fa Faruq zai baiwa ita.babu wanda yasan wannan kudirin nasa sai sarkin Kano.