Chapter 14

872 58 0
                                    

       A inde yake tsaye ya yasar da flowers d'in ba tare da ya san yayi hakan ba ,kamar 'kiftawar ido ya fita daga gidan. Da fitarsa da shiga mota be wuci 'yan sakanni ba,tu'ki yake amma besan inda zashi ba,seda ya tabbata yayi nisa da area d'in ya samu yayi parking can bayan gari."No!"Ya daki steering d'in motar ya zira yatsansa cikin sumarshi se mutstsukawa yake kamar ze cire gashin kansa."It can't be,No! Rose why? why?"be ankara ba yaji idanuwansa na tsiyayar hawaye,feeling his heart broken into pieces.
Tunanin rayuwarsu da suka shafe tare ya shiga yi,ko a mafarki idan aka ce Rosie zata ci amanarsa baze yarda ba amman yau ya gani da idansa.

      Yafi 20 min yana abu d'aya wayarsa da tayi ringing yasa ya dawo daga duniyar tunanin daya tafi.

     "Mom" Ya gani a jikin screen.

     Ta kira har sau uku amma ya'ki d'agawa,lokaci guda yaji ciwon kai ya kamashi.Da 'kyar ya samu ya iya komawa gida, image d'inta ya'ki gushewa daga idansa.

      Mom ganinsa ya shigo gida tayi sauri ta 'karasa inda yake."Son, where have you been? are you ok?"

     Kai kawai ya kad'a yana 'ko'karin cire jacket d'inshi.

     "Amjad, you're looking sick" Ta fad'a tana dafa kafad'arsa fuskarta d'auke da damuwa.

    "Mom ,I just need to rest"Yayi 'ko'karin fad'a.

     "Ok ,go to your room I will prepare your a meal immediately you woke up"

     Yana shiga d'akinsa ya rufo 'kofar,yana ciro wayarsa daga aljihu sega kiran Rosie.

    "Baby boo" Ya bayyana a screen.

    Gabaki d'aya wayar yayi switching off ya cilla gefe,ya fad'a kan gadon ya rufe idansa trying to force him self to sleep.

    An hours later,2:30pm ya farka har lokacin kanshi be dena ciwon ba,tashi yayi ya shiga bathroom ya watsa ruwa yayo alwala ya tada sallah.

    Knock! Knock! Mom tayi knocking ,ganin be bud'e ba ta murd'a handle ta shiga,sallah ta tarar yana yi haka yasa ta koma.Chicken Spaghetti  ta dafa mashi tayi arranging,tana gamawa ta koma sama ta kirashi.

    Ga abincin yasa a gaba amma ya kasa ci ,Mom data san Chicken spaghetti ne favorite d'insa tayi mamaki ganin ko fork d'in be d'aga ba.

     "Amjad, don't you wanna eat?"

     "I lost my appetite"Yana fad'ar haka ya mi'ke ya bar wajen.

     " Am.."Bata 'kare ba taga har ya 'bace mata daga gani.

             ★★★

      Laila

       7:12pm suna d'aki ita dasu Maryam se hirarsu suke ta mance da wani Amjad,idan Mami ta tambayeta suna waya da Amjad setace eh,wani lokacin har alarm take sawa idan yayi ringing setai pretending kamar kiran waya ne.

      Amjad kuwa cikin dare 11:00pm sam ya kasa bacci kawai juye-juye yake akan gado daga ya rufe ido Rosie yake gani da wannan guy d'in,tashi yayi ya d'auko wani box a 'kar'kashin gado.Hotuna ne ciki na Rosie harda wanda sukai tare dashi tun suna teens daga gefe kuwa teddy ne 'karami mey heart a cikinsa wanda Rosie ce ta bashi wani lokaci da yayi birthday. D'aukansu yayi ya tarkata duka ya fita can  backyard ya cinna musu wuta yana kallo har suka 'kone ya watsa tokar a dustbin.Hatta phone d'insa babu wani abu na Rosie daya bari pictures nata na musamman daya tanada musu folder seda yayi deleting,seda ya tabbata ba abinda ya ragu nata a wayarsa ya iya samun yin bacci.Amjad sam be iya so ba haka be iya tsana ba,ya tsani yaudara mutum ne mey zafin kishi ko Zakia idan ya ganta da wani classmate bama boyfriend ba  seya ji haushi.

AMJAD(Completed)Where stories live. Discover now