Chapter 16

938 63 0
                                    

        Wani irin murd'awa cikinta ya hau yi,nan take gumi ya soma keto mata ta rasa abinda ke mata dad'i wayar ma ajje ta tayi gefe.Tashi tayi a rud'e ta nufi inda taga mey aikin ta shiga,a kitchen ta tarar da ita tana wanke-wanke.Laila tambayarta tayi toilet tana ta zufa.D'aki ta rakata wanda yake d'auke da toilet a ciki,da sauri-sauri laila ta fad'a  ciki.

     Minutes later ta dawo parlour gwiwoyinta sun fara sanyi gashi cikin har yanzu be dena hautsinawa ba,wayarta ta duba taga 3missed na Amjad. Bata ko zauna ba ta fita,a chan  farfajiyar gidan ta hangeshi yana zaune a table shi kad'ai jama'ar wajen ma sun fara raguwa.A hankali ta taka zuwa inda yake,sede ta 'karaso ya kula da ita.

    "Where have you been?"

     "Gani na fito ai"Ta fad'a.

      Mi'kewa yayi tsaye ya fara tafiya tana biye a bayansa Farouq da Aisha suka 'karaso inda suke.

     " Tafiya?"Ta tambayi Laila.

    Laila cikin ya'ke ta amsa da "Eh"

    "Toh bari na kar'bi numbernki".

     Numbernta ta fad'a mata a take tayi flashing itama Laila tayi saving, har waje suka rakosu ita de Laila kawai basarwa take cikinta ba abinda yake se hautsunawa ta 'kagu su koma gida.

      Tunda ta shiga mota bata ce 'kala ba,gani take kamar ba tu'ki yake ba har wani le'kawa take tana ganin speed d'in."Mtchww" Tayi tsaki ba tare da ta sani ba.

    "Are you alright?" Ya tambaya.

     Kai ta kad'a alamar "eh" se kad'a 'kafa take tana tapping cinyarta."Innalilahi wainna ilaihirraji'un"Ta fad'a  a ranta ganin traffic light ya tsayar dasu.

    Da 'kyar ta samu ta iya jurewa har suka koma gida,cikin sauri ta fad'a toilet ko 'kofar d'akin yau bata rufe ba.Daga dawowarsu zuwa yanzu Laila ta shiga toilet yafi sau uku,gwiwoyinta gabad'aya sunyi sanyi da'kyar take takawa.Gashi batasan inda zata sami magani ba,lokaci guda tayi zuru-zuru jinta take kamar kara dan tsabar rashin 'kwarin jiki.

       11:29pm Ring!Ring! wayar ta tayi 'kara lokacin tana toilet har 3 missed call batai picking ba.

   
     Amjad yana d'akinsa dede lokacin yake shirin kwanciya wayarsa tayi 'kara,koda ya duba yaga Farouq.

      
     Knock! Knock! Ya 'kwan'kwasa 'kofar d'akinta shiru,handle d'in ya murd'a ya shiga beganta ba.

     "Laila" Ya kira sunanta.

    Tana shirin fitowa taji ya kira sunanta ,zaro ido  tayi ido tana mamakin jinsa a d'akinta a irin wannan lokacin.

     "Laila ,come on open the door"

       Tsit kake ji ko motsi ta'ki yi gashi tsaiwar ta isheta,kan bathtub ta samu ta zauna ta dafe  cikinta.

     "Laila,can't you hear me? open the door now stop pretending I know everything"

     "Mey? Waya fad'a masa? Yasan..." Ta dafe kai shikenan tonon silili.

    "Laila don't let  me  open it myself, you know I have a spare key right?"

     "Innalillah" Jiki ba 'kwari ta mi'ke tsaya a daddafe ta 'karasa jikin 'kofar gashi jikinta kayan bacci ne riga da wando  kusan ¾,inda Allah ya taimaka ma rigar ta hauro kusan cinya,d'an'kwalin kanta ta ware yadda ze sakko 'kasa , a sanyaye ta bud'e 'kofar kanta a 'kasa.

       "Laila" Ya kira sunanta.

      A hankali ta d'ago da kanta kallo d'aya tayi masa ta maida kanta 'kasa,se jan mayafin take tana kare 'kirjinta.

AMJAD(Completed)Where stories live. Discover now