***Tap d'in sink dake zuba ya mi'ka hannu ya kashe sannan yaja baya.Laila har lokacin idanuwanta a rufe suke zuciyarta bata fasa bugawa ba,a hankali ta rage jin d'umin mutum a jikinta,da 'kyar ta soma bud'e idanuwanta gani tayi ba kowa a kitchen d'in.Tunani ta shiga yi ko dama ba gaske bane,data dubi sink d'in taga tap d'in ya dena zuba.Da sauri-sauri ta 'karasa d'auraye plates d'in ta koma d'aki,har lokacin bata dena jin tsoro ba gani take kamar zata sake ganinsa.
Shi kuwa daya koma d'aki murmushi ya shiga yi ,be zacci tsoronta yakai haka ba shikam yanzu ya samu damar hanata fad'ar abinda ranta yaso.Phone d'insa ya d'auko yayi plugging earphone tare da turning on song(Can I have this dance:high school musical).
🎵Take my hand, take a breath
Pull me close and take one step🎵
Keep your eyes locked to mine 🎵
And let the music be your guide Won't you promise me? (Now won't you promise me?)🎵
That you'll never forget (We'll keep dancing) 🎵
To keep dancing wherever we go next🎵
It's like catching lightning The chances of finding someone like you It's one in a million,🎵
the chances to feeling The way we do.....🎵
Ba'ai nisa ba ya katse wa'kar dan ta soma tuna masa da Rosie,dan itama bata da wa'ka kamarta asali ma ita tasa masa son wa'kar dan wasu lokutan tare suke jin wa'kar suna bi.
★★★
Laila har 9pm bata fito ba 'kishir ruwa take ji amma ta kasa fitowa gudun kar wani abun ya sake faruwa.Wayarta ta d'auka ta hau Instagram taga Amjad mu'az started following you,profile d'inshi ta bud'e taga post kala-kala.Wani photo data gani seda tayi tsaki ganin ko riga besa ba showing his six packs ,daga shi se ¾.
"Se kace d'an arna"Ta fad'a tana scrolling taga wani photo nashi ta gani yana yaro sosai befi 9yrs ba dariya photon ya bata yanayin yadda yayi wani kalar soko ya cakumi teddy bear.Haka tayi ta bin sauran pics d'in wasu tare da su Mom wani friends, a haka har ta soma jin bacci daga baya ta ajje wayar tayi kwanciyarta.
Washegari da wuri tayi shirin makaranta ko breakfast bata yi ba ta fice se sauri take karya fito yace ze kaita.Seda taga ta hau d'an sahu hankalinta ya kwanta,lecture biyu kad'ai sukai amma Laila ta'ki tahowa gida,2pm lokacin masjid kawai taje bayan datai sallah ta kwanta bacci ya kwasheta.
4:09pm ta farka ,mamakine ya kamata ganin har tayi bacci me tsaho haka.Tashi tayi ta d'auro alwala tayi sallah,bata ankara ba taga garin yayi duhu sakamakon hadari daya had'u.Ba shiri ta tarkata handout d'inta ta zira a jaka ta fito,sanda ta hau napep har an fara iska mey 'karfin gaske kafin ta isa gida ruwa ya sakko.Kafin ace mey nan da nan danan titi ya d'inke da abin hawa a hankali ake tu'kin ruwan se shigowa yake cikin napep d'in rabinta ta jike,ganin ta kusa 'karasawa gida kawai ta sauka ta kama tafiya sauri-sauri ,tun daga nesa ta hango wani mota a ranta ta ayyana na Amjad ne aiko tana 'karasowa ta ga shine yana ciki ya'ki fitowa gashi motar ta gagara tashi ya dad'e yana ta fama ganin ruwa ya sakko yasa ya shige ciki ya zuge glass rabi.Ta mirro d'in gaba ya hangota ,a tunaninsa ko zata tsaya amma yaga ta wuce kamar bata gane shi bane.Da kanshi ya fito daga motar dukda tsananin ruwan da ake."Laila" Ya kira sunanta.
